✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Harin Boko Haram kan turakun lantarki ya jefa Maiduguri cikin duhu

Wannan dai shine karo na biyu a cikin watanni uku da ake kai hari kan turakun wutar lantarki a hanyar Maiduguri.

Mazauna birnin Maiduguri na jihar Borno sun fada cikin matsalar wutar lantarkin sakamakon harin da aka kaiwa daya daga cikin manyan turakun wutar da ya sada jihar da sauran sassa na kasa.

Rahotanni sun nuna cewa matsalar wutar lantarkin wacce ta shafe kusan mako daya ta yi mummunar illa ga sana’o’i da dama, musamman wadanda suka ta’allaka da ita.

Wadanda kuma suka koma amfani da janareto sun rika gudanar da harkokinsu sama-sama.

A tattaunawarsu da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), wasu daga cikin mazauna birnin ba wai kawai sun yi Allah-wadai da lamarin ba ne, sun kuma koka kan abinda suka kira halin ko-in-kula daga hukumomi kan shawo kan matsalar.

A cewar Ibrahim Abubakar, wani mazaunin birnin, “Yanzu mako daya kenan cif amma mutane ba su san me ya hana mu samun wuta a Maiduguri ba.

“Muna so mu san abinda ya haddasa matsalar da kuma irin kokarin da kamfanonin wuta ke yi wurin magance ta.

“Ba zai yuwu ka bar mutane a cikin duhu ba tare da cikakken bayani ba,” inji shi.

Shima wani mai sana’ar walda, Moses Bala ya ce lamarin ya tasamma durkusar da sana’arsa saboda da wutar ya dogara wajen gudanar da ita.

“Saboda a ’yan watannin baya an yi ta samun wutar yadda ya kamata, na dogara kacokam kan wutar gwamnati, amma yanzu kusan mako daya kenan a zaune kawai nake saboda babu wutar.

“Ga shi ni kuma ba ni da karfin sayen janareta saboda har yanzu sana’ar tawa jaririya ce,” inji Moses.

Daga nan sai yayi kira ga hukumomin da abin ya shafa kan su daure su lalubo bakin zaren matsalar.

Sai dai da wakilinmu ya tuntubi Shugaban Sashen Hulda da Jama’a na Kamfanin Rarraba Hasken Wutar Lantarki na Shiyyar Yola (YEDC) wanda shine ke kula da jihohin Borno da Yobe da Adamawa da Taraba, Mista Kingsley Nkemneme ya ce ba abinda zai iya cewa a kai saboda matsala ce da ta shafi Kamfanin Samar da Wutar na Najeriya (TCN).

Wannan dai shine karo na biyu a cikin watanni uku da ’yan ta’addan kungiyar Boko Haram ke kai hari kan turakun wutar lantarki a hanyar Maiduguri.