✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin bam ya raunata Kakakin gwamnatin Somaliya

Rahotanni sun ce wannan ba shi ne karo na farko da ake kai kakakin hari ba, ana yunkurin hallaka shi.

Wani harin bam da wani dan kunar bakin wake ya kai Mogadishu, babban birnin kasar Somaliya ya raunata Kakakin gwamnatin kasar, Mohamed Ibrahim Moalimuu.

Kafafen yada labaran gwamnatin kasar sun tabbatar da harin da aka kai ranar Lahadi a kofar gidan jami’in gwamnatin.

 

Wani mai daukar hoto a inda lamarin ya faru ya ce an ga wasu sassan jikin mutane da harin ya daidaita, yayin da shi kuma kakakin aka garzaya da shi asibiti.

A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Gwamnatin Kasar, an kai harin ne a kusa da wata mahadar babbar hanya da ke birnin.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan kasar, Abdifatah Aden, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, “Maharin ya yi kokarin hallaka kakarin gwamnatin ne, kuma yanzu an garzaya da shi asibiti sakamakon raunukan da ya samu.”

Nasra Bashir Ali, wani dan jaridar da ke aiki a ofishin Firaiministan kasar, a inda nan ne ofishin Kakakin ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa Mohammed din bai ji wani mummunan hari ba sakamakon harin da aka kai wa motar da yake ciki.

Rahotanni sun ce wannan ba shi ne karo na farko da ake kai wa kakakin, wanda tsohon dan jarida ne, hari ba ana yunkurin hallaka shi.

Dan kunar bakin wajen dai ya tayar da bam din ne lokacin da kakakin ke kokarin fitowa daga gidansa a ranar Lahadi.

Babu dai wanda ya dauki alhakin kai harin kai tsaye ya zuwa yanzu.

Kungiyar Al-Shabab, wacce ke da alaka da Alka’ida a kasar dai wacce ke kokarin hambarar da gwamnatin kasar da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya a lokuta da dama ta sha daukar alhakin kai makamantan wadannan hare-haren.

Kazalika, kasashe kawayen Somaliya na ci gaba da nuna damuwa kan yadda ake ci gaba da fuskantar takun saka tsakanin ofishin Shugaban Kasa da na Firaiministan kasar.