✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Harin bam ya kashe Yahudawa biyu a Birnin Kudus

’Yan sandan Isra’ila sun bayyana harin a matsayin na ta’addanci.

Mutane biyu sun rasa rayukansu ciki har da yaro mai shekara shida, a wani harin bam da aka kai da wata mota a tashar bas a unguwar Yahudawa da ke gabashin Birnin Kudus.

Wannan harin da ‘yan sandan Isra’ila suka bayyana a matsayin na ta’addanci, ya faru ne a Ramot inda yawancin masu tsattsauran ra’ayi ke zaune a wuraren da Isra’ila ta mamaye.

Dama dai ana fargabar barkewar tashin hankalin da ba za a iya shawo kansa ba sakamkon yadda rikicin Isra’ila da Falasdinu ke ci gaba da ruruwa tun farkon wannan shekara.

Ko makonni biyun da suka gabata ma, sai da wani Bafalasdine ya harbe wasu ‘yan Isra’ila shida da wata ‘yar kasar Ukraine har lahira a kusa da majami’ar unguwar Yahudawa da ke gabashin Birnin Kudus.

Kasashen duniya da dama sun yi kiraye-kiraye ga Isra’ila da ‘yan yankin Falesdinu da su kwantar da hankulansu sakamakon karuwar tashe-tashen hankula.