Akalla mutum hudu ne suka halaka bayan wani bam ya tashi a birnin Basra na Kudancin kasar Iraki, kamar yadda sojojin kasar suka tabbatar.
A cikin wata sanarwa da suka fitar ranar Talata, sojojin sun ce wani babur makare da bama-bamai ne ya tayar da su, lamarin da ya yi sanadiyyar tirnikewar bakin hayaki a sararin samaniya.
- ’Yan bindiga sun tare hanya a Zamfara, sun kone matafiya 6 a cikin mota
- Kotu ta daure tsohon jami’in Kwastam kan fasakwaurin bindigogi
Ya zuwa yanzu dai kwararru na wajen inda suka ci gaba da aikin ceto tare da binciken musabbabin tsahin bam din.
Kazalika, karin wasu mutum 20 kuma samu munanan raunuka kuma suna can suna samun kulawa, kamar yadda ’yan sandan kasar suka tabbatar wa da Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters.
Wata majiya daga jami’an tsaron kasar ta shaida wa kafar yada labarai ta Rudaw a cikin wata sanarwa cewa bama-baman sun tashi ne a kusa da wani asibiti mai suna Al-Jumhouri da ke tsakiyar birnin na Basra.
“Yanzu haka jami’an tsaro sun yi wa wajen kawanya domin gano yanayi da kuma girman harin,” inji majiyar.
A cikin ’yan shekarun nan dai ba kasafai ake samun kai hare-hare ba a birnin na Basra, musamman tun bayan murkushe kungiyar ISIL a shekarar 2017.
Har zuwa yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai harin.