✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hari kan NSCDC: Kar ku raga wa ’yan bindiga —Buhari ga sojoji

Shugaban ya umarci sojojin Najeriya da su kamo ’yan bindigar su yi maganinsu.

Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da kisan jami’an Sibil Difens bakwai da wasu ’yan bindiga suka yi a Kaduna.

Cikin wata sanarwa da kakakinsa Garba Shehu ya fitar ranar Alhamis, Buharin ya bayyana takaicinsa da kisan jajirtattun jami’an da ya ce sun sadaukar da rayuwarsu ga Najeriya.

“Jami’an NSCDC din da suka sadaukar da rayuwarsu wajen tsare kasarmu ba karamin jihadi suka yi ba a bakin aikinsu.

“Ina jajanta wa iyalai da ’yan uwa da abikan arzikinsu. Ina rokon Ubangiji Ya ba su ikon jure wannan rashi”, in ji Buhari.

Daga nan ne kuma shugaban ya umarci rundunar sojojin Najeriya da su kamo ’yan bindigar su yi maganinsu.