Hukumar tsaro ta Sibil Defens a jihar Gombe ta gabatar da wasu mutum takwas da ta kamo da ake zargin suna sayarwa mutane mushen nama.
Da yake gabatar da waɗanda ake zargin ga manema labarai a hedkwatar hukumar, Kwamandanta na Jihar Gombe, Muhammad Bello Mu’azu, ya ce rundunar ta fara kama jagorar wadanda ake zargin ce mai suna Mary Paul tare wasu mutum hudu, kafin daga bisani ta sake kama wasu karin mutum uku.
Kwamandan wanda jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SC Buhari Sa’ad, ya yi magana a madadinsa ya ce sun kama mutanen ne bisa bayanan sirri da suka samu kan haramtacciyar sana’ar da ake zargin mutanen na yi.
Ya ce an kama waɗanda ake zargin ne a wata kasuwar da ke a kwaryar Gombe, kasancewar sun saba sayar da mushen ga jama’a a jihar da ma wasu jihohin Kudancin kasar nan, musamman Jihar Delta.
A cewar Kwamandan, Mary da tawagarta yawanci suna sarrafa naman ne tare da gyara shi don sayarwa jama’a ba tare da sun san naman mushe ba ne.
Ya kuma ce jami’ansa sun kama wasu ma a babur mai kafa uku ɗauke da wata matacciyar saniya da suka sayo daga Kanawa a yankin Ƙaramar hukumar Yamaltu Deba inda suka sa aka binne ta a wajen gari.
Muhammad Bello Mu’azu, yace da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu.
Sannan sai ya kirayi jama’a da su yi hattara da irin naman da suke saya, da inda suke saya da kuma wurin wadanda suke saya.
Jagorar wadanda ake zargin, Mary Paul, ta ce a baya tana sayar da naman daji ne da aka farauto, amma dai daga baya ta koma sayar da mushen.
Mary ta ce ta shafe tsawon shekaru tana wannan sana’ar inda take amfani da sinadarai wajen sarrafa naman da kuma adana shi.