✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hare-haren kunar bakin wake da mata ke jagoranta

daya daga cikin abin takaici a rikicin da ke faruwa a yankin Arewa-maso-Gabas shi ne yadda kungiyar Boko Haram da wasu kungiyoyin ’yan ta’adda wanda…

daya daga cikin abin takaici a rikicin da ke faruwa a yankin Arewa-maso-Gabas shi ne yadda kungiyar Boko Haram da wasu kungiyoyin ’yan ta’adda wanda ke buya a bayansu  suke amfani da mata wajen kai hare-haren bama-bamai a wuraren taruwar jama’a.
Wadannan kungiyoyin suna amfani da mata musamman ’yan mata saboda yadda ake tausaya musu da kuma kallonsu a matsayin iyaye. Yanzu ana amfani da su ta hanyar da ba ta dace ba wajen kashe rayuka da lalata dukiya, inda suke jefa iyalai da dama cikin alhini. A ’yan shekarun nan, lokacin da masu tada kayar bayar suka fara amfani da salon kunar bakin wake wajen kai farmaki, ba wanda ya taba tsammanin cewa mata za su iya aikata hakan. Ta la’akari da yadda Allah Ya halicce su, ya sa ba a wa matan kallon wadanda za su iya daukar muggan makamai da ka iya cutar da wasu  ko al’umma, sabanin takwarorinsu maza. Sai dai wasu na yin amfani da wannan darajar tasu wajen salwantar da rayuka ciki har da na su kansu matan.
Kamar yadda ’yan kato da Gora (Cibilian JTF) suka bayyana cewa sun tatsi bayanan sirri wanda ke nuni da cewa akwai mata ’yan kunar bakin wake 50 wadanda  aka bai wa horo domin kai hare-hare, kuma aka watsa su cikin garin Maiduguri na Jihar Barno da umarnin kisan akalla mutum 100,000 kafin karshen wannan watan. A watan Yulin da ya wuce ne, a Jihar Katsina, aka cafke wata yarinya ’yar shekara 10 sanye da jigidar bama-bamai gabanin ta kai ga ta da su. Hakazalika, an samu wata ’yar kunar bakin wake da ta tayar da bam a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano, inda ta kashe mutane da dama da kuma raunata wasu masu yawa. Har ila yau, a watan jiya ne, wata ’yar kunar bakin wake ta kai harin bam a Kwalejin Horar da Malamai ta Gwamnatin Tarayya da ke garin Kwantagora na Jihar Nija; inda ita kadai ta rasa ranta saboda bam din ya tashi kafin ta isa wurin da aka nufi kai farmakin. Sai kuma wani mummunar harin da aka kai kasuwar Monday Market da ke garin Maiduguri wanda shi ma ’yar kunar bakin wake ce da wani mutum suka jagoranci kaiwa, inda akalla mutum 50 suka rasa rayukansu.
Wannan abin tsoro ne da ya yakamata a kawo karshensa. Ya dace a dauki mataki kafin matsalar ta zama wata babbar barazana ga kasar baki daya. Ana bukatar kara yin hobbasa wajen bai wa mata ilimi ta yadda zai rusa  akidar da aka cusa masu wadda ke sanya su zama ’yan tada zaune tsaye.
Yakamata sojoji su sauya salon yakin da suke da ’yan gwagwarmayar wadanda rahotanni suke nuna cewa jama’a sun fara dawo daga rakiyarsu. Wannan ya sa mutane suke fadawa hannun ’yan gwagwarmayar. Yana da matukar mahimmanci idan jama’a za su dauki sojojin a matsayin abokai wadanda ke kare su, ba daukarsu a matsayin makiya da ke barazana ga kowa ba.
An sha samun rahotannin jama’a na gudanar da zanga-zanga saboda zargin sojoji na musguna masu. Akwai bayanan da ke cewa sojoji suna kisan keta haddi da kuma yi wa mata fyade, laifukan da za su iya tunzura wasu zuwa daukar  fansa.
Mata ’yar kunar bakin wake suna barazanar bata wa mata kima da darajar da aka sansu da ita. Saboda bayan harin bam din da aka kai Babban Masallacin Juma’ar birnin Kano, an samu karin nuna rashin yarda ga  mata masu sanya hijabi. Akwai wasu jihohi a yankin Kudu-maso-Yamma da suka hana sanya hijabi.
Muhimmin aikin wayar wa da jama’a kai shi ne mutane su kasance masu kula a kowane lokaci.
Idan da a ce gwamnati za ta tashi tsaye da taimakon shugabannin addini da iyaye da sauran jama’a da ke rike da madafan iko, za a iya kawo karshen hare-haren ’yan gwagwarmayar baki daya da kuma farmakin da mata ’yan kunar bakin wake ke jagoranta.Ya dace shugabannin al’umma su yi amfani da duk wata dama da suka samu wajen yin Allah-wadai da yadda ake cusa wa mata akida da kuma amfani da su da ake wajen kai harin kunar bakin wake.