✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Haramun ne shugabannin ’yan sanda su rika yawo da jiniya – Lauya

Ya ce mutum 16 dokar Najeriya ta ba damar amfani da jiniya

Wani fitaccen lauya a Kano, Barista Abba Hikima, ya ce yawo da jiniya da ’yan sanda ke yi a Najeriya ba don bin masu laifi su kamo su a hanya ba, ya saba wa dokar Najeriya.

Lauyan ya bayyana hakan ne a shirin In Da Ranka na gidan rediyon Freedom da ke Kano ranar Talata.

Ya ce bisa tanadin dokar amfani da hanyoyi ta Najeriya ta shekarar 2012, mutum 16 ne kacal dokar Najeriyar ta ba wa ikon yawo da jiniya da fitilarta.

“Na farko akwai Shugaban Kasa da Mataimakinsa, akwai Gwamnoni da Mataimakansu, akwai Shugaban Majalisar Dattijai da ta Wakilai da Mataimakansu.

“Sauran su ne Alkalin-Alkalai na Kasa, sai masu aikin ceto irin su asibitoci, Hukumar Kashe Gobara da sauransu, sai kuma lokutan yaki,” in ji Lauyan.

Barista Abba Hikima ya kuma ce duk wanda aka samu da karya wannan doka, hukuncinsa shi ne daurin watanni shida, ko kuma biyan tarar N10,000.