✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Haramtattun makamai miliyan shida na shawagi a Najeriya — Abdussalami

Tabbas hakan ya kara tabarbarewar matsalar tsaro wanda ya yi sanadiyar mutuwar sama da mutum 80,000.

Tsohon Shugaban Najeriya, Abdulsalami Abubakar, ya yi korafi tare da shelanta cewa akwai haramtattun makamai akalla miliyan shida da ke shawagi a hannun mutanen da bai dace sun mallake su ba.

Abdulsalami wanda shi ne Shugaban Majalisar Wanzar da Zaman Lafiya a Najeriya, ya bayyana hakan ne yayin taron da ta gudanar tare da masu ruwa da tsaki a Otel din Transcorp Hilton da ke birnin Abuja a ranar Laraba.

A cewar tsohon Shugaban, karuwa makamai sun janyo ta’azzarar matsalolin tsari da suka addabi kasar wanda sun yi sanadiyar salwantar rayukan fiye da mutum 80,000 a Najeriya.

Ya ce kalubalen da kasar ke fuskanta sun zarta matsalar kadai, inda a mahanga da sojoji ta shafi dukkan bangarori.

Daga cikin matsalolin da Najeriya ke fuskanta kamar yadda tsohon shugaban ya wassafa sun hada da rikicin Boko Haram, ta’addancin ’yan bindiga da barayin shanu da masu garkuwa da mutane, da masu fafutikar raba kasa gami da talauci da kuma yunwa.

“Yadda ake samun yawaitar nau’ika daban-daban na haramtattun makamai da ke shawagi a Najeriya abin damuwa ne saboda an yi kiyasi cewa akwai akalla haramtattun makamai miliyan shida a kasar nan.”

“Tabbas hakan ya kara tabarbarewar matsalar tsaro wanda ya yi sanadiyar mutuwar sama da mutum 80,000 da kuma kusan mutum miliyan uku da ke gudun hijira,” in ji Abubakar.

Tsohon Shugaban yayin ci gaba da tsokaci a kan matsalar tsaro, ya ce ba a tanadar wa hukumomin tsaro kudade da kayan aikin da suka dace ba, wanda a cewarsa ba za su iya aiki a wannan zamani ba madamar ba su wadata da makamai masu inganci ba.

Yayin da yake bayar da tabbaci a kan masaniya da kuma goyon bayan Shugaba Muhammadu Buhari game da taron, Abdulsalami ya ce suna fatan Najeriya za ta shawo kan wadannan matsaloli ta hanyar tuntubar mashawarta domin inganta al’amura a kasar.

A nasa jawaban, tsohon Shugaban Kasa Janar Yakubu Gowon, ya bukaci al’ummar kasar da su jingine banbacin akida ta siyasa da addini da kabilanci ba domin taimakawa wajen magance matsalolin da kasar ke fuskanta a yanzu.

Daga cikin mahalarta akwai Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar na III, Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti, Gwamna Simon Bako Lalong na Jihar Filato da sauran shugabannin addinai da manyan ma’aikata na Hukumomin tsaro.