Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno, ya ce hana makiyaya yawon kiwo-sake a wasu jihohin ba zai yiwu ba.
Zulum ya bayyana haka ne yayin hira da gidan Talabijin na Channels, a ranar Laraba, inda ya ce haramta kiwon-saken ba zai yi aiki har sai an kawo karshen matsalar tsaro.
“Dole ne mu magance matsalar tsaro, komadar tattalin arziki da rikicin da ke tasowa a yankuna sakamakon karuwar talauci, wanda shi ne ke haifar da ta’addanci.
“Ana ci gaba da samun karancin abinci a yankin gabas wanda shi ne mafi muni.
“A kan haka ne ma gwamnatin Borno cikin shekara biyu da suka gabata, ta mayar da hankali wajen wayar da kan manoma kan muhimmancin komawa gonakinsu.
“Magance matsalar tattalin arziki da tashin hankula abu ne mai muhimmanci.
“Sannan kuma sulhunta rikicin da ke tsakanin manoma da makiyaya shi ma na da muhimmanci.
“Sai hakan ta tabbata kana a iya samar wa da makiyaya wani yanayi da zai taimake su.
“Amma maganar haramta a makiyaya kiwon-sake ba zai yiwu ba har sai mu zauna mun samo hanyoyin magance dukkan matsalolin nan,” cewar Zulum.
Wata biyu da suka gabata a garin Asaba na Jihar Delta, gwamnonin kudu suka yi taro tare da haramta wa makiyaya kiwo, wanda shi ne silar rikicin da ke faruwa tsakanin manoma da makiyaya.
Sai dai hukuncin nasu ya tada kura a tsakanin mahukunta da sauran jama’ar gari, inda gwamnatin tarayya ta mayar da martani kan cewa kundin tsarin Mulki ya bawa kowa ‘yancin yawo.