Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta ce har yanzu haramcin da ta sanya kan amfani da mutum-mutumi a shagunan sayar da kayan sa wa da na teloli a fadin Jihar na nan daram.
A watan Yunin bara ne dai hukumar ta sanar da haramta amfani da mutum-mutumin a Jihar, tare da barazanar kama duk wanda ya karya dokar.
- Kotu ta yi wa mahaifi daurin rai-da-rai kan yi wa ’yarsa fyade
- Yadda alaka mai karfi ta kullu tsakanina da Abacha —Janar Abdulsalami
A cewar Babban Kwamandan hukumar, Harun Ibn Sina, sun dauki matakin ne saboda amfani da mutum-mutumin ya saba da koyarwar addinin Musulunci.
Sai dai a wani taro da ta yi da Kungiyar Teloli ta Kasa reshen Jihar ranar Alhamis, hukumar ta Hisbah ta sake jaddada cewa haramcin na nan daram.
Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sashen yada labarai na hukumar ya fitar a ranar Juma’a.
A cewar Ibn Sina yayin taron nasa da telolin “Hukumar Hisba ta Jihar Kano bisa dogaro da sashen dokar Hisba ta shekarar 2001, wacce aka yi wa kwaskwarima a 2003, ta hana kowanne mai dinki saka mutum-mutumi, wanda yake dauke da siffar mutum cikakkiya, ko ta mace ko ta namiji.
“Amma za a iya anfani da wanda babu kai ajikinsa ko a jikanta, ita ’yar tsanar da ake saka wa kaya.
“Wannan shine kadan daka cikin muhimman abin da aka tattauna a kai yau,” inji Ibn Sina.
Daga nan sai Kwamandan na Hisbah ya yi kira ga telolin da su bi dokar ta hukumar tare da neman su tsaftace sana’ar tasu.