Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Najeriya (IPMAN) ta ce duk da tsadar da mutane ke kuka da ita a halin yanzu, Najeriya ce ta fi kowacce kasa arhar man a kaf nahiyar Afirka.
Jami’in Hulda da Jama’a na kungiyar na kasa, Yakubu Sulaiman, ne ya bayyana haka a wata hirarsa da gidan talabijin na Arise a ranar Alhamis, a kan tashin farashin man.
- Gobara ta kone shaguna 10 a Kasuwar Rimi da ke Kano
- Zaɓin Ganduje lalata tsarin APC ne – Salihu Lukman
Ya kuma dora alhakin tashin farashin na kwanan nan a kan faduwar darajar Naira da tashin Dalar Amurka, wacce da ita ake shigo da man.
Ya ce, “Kamar yadda aka saba, wannan tashin farashin yanayin kasuwa ne ya haddasa shi. Yanzu kasuwa ce take yanke wa kanta farashi. Na biyu kuma akwai batun Dala, wacce a hakin yanzu ta tashi. Duk lokacin da ta sauka, shi ma farashinsa zai sauka.
“Maganar gaskiya kawai jita-jita cewa wai mutane na farin ciki da wannan tsadar. Duk Dillalin man da ya ce yana farin cikin da hakan to gaskiya yaudararka kawai yake yi.
“Idan ka shigo da mai, zai karaso Najeriy ne a kan N565. Amma muna fatan ba zai sake tashi sama da haka ba a nan gaba. Ya kamata mu hadu tare mu yi addu’a don ya sauka.
“Bugu da kari, idan ka kwatanta da wasu kasashen na Afirka, har yanzu man fetur dinmu ya fi na kowacce kasa sauki,” in ji Yakubu.
A ranar Talata ce dai Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) ya kara farashin man aga N537 zuwa tsakanin N617 da N630.