✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Har yanzu Manchester City ba tsarar Liverpool ba ce —Bernardo Silva

Tazarar maki hudu ke tsakanin City da Liverpool wadda ke da kwantan wasa daya a hannu.

Dan wasan tsakiya na Manchester City Bernardo Silva ya yi ikirarin cewa har yanzu kungiyarsa ba tsarar Liverpool ba ce duk da yadda suka tashi wasansu da Crystal Palace babu ci a karawarsu ta ranar Litinin karkashin gasar firimiyar Ingila.

A zantawar Silva da Sky Sports, ya ce ya kamata a ce su ke da nasara a wasan amma kuma aka samu kura-kurai, sai dai duk da hakan ba ya fargabar Liverpool za ta iya gogayya da su a firimiya.

Silva ya ce yana da yakinin tazarar da ke tsakaninsu da Liverpool zai koma maki 6 gabanin karkare wasanni 9 da suka rage na gasar, domin a cewarsa ba za su yi wasa da damar bakuntar Reds da za su karba cikin watan Afrilu ba.

Tazarar maki hudu ke tsakanin jagorar ta Firimiya da Liverpool wadda ke da kwantan wasa daya a hannu.

A yanzu kenan idan har tawagar ta Jurgen Klopp ta iya nasara kan Arsenal a ranar Laraba, tazarar da ke tsakanin kungiyoyin biyu manyan abokanan dabi zai koma maki 1 tal.

Makwanni 8 da suka gabata dai City na jagoranci ne da tazarar maki 13 tsakaninta da Liverpool wadda a wancan lokaci ke matsayin ta 3 da kwantan wasanni 2 a hannu, amma yanzu ya koma maki 4, yayin da tawagar ta Pep Guardiola ke shirin haduwa da kungiyoyin Tottenham da Manchester United da kuma Everton baya ga Crystal Palace a wasanninsu na gaba, wanda ke nuna akwai babban kalubale a gabanta.