✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Har yanzu mahaifina dan APC ne —Zainab Buba Galadima

Diyar Buba Galadima da Buhari ya aurar ta ce in dai aiki a Fadar Shugaban Kasa ne ta hakura.

Diyar tsohon makusancin Shugaba Buhari, Injiniya Buba Galadima da yanzu suka raba jiha ta ce har yanzu mahaifin nata dan jam’iyyar APC ne.

Zainab Buba Galadima, tsohuwar jami’a a Fadar Shugaban Kasa ta ce akwai gyara Gwamnatin Buhari kuma da irin abin da ta gani a fadar gwamnati, sai dai a kai kasuwa.

Ta ce, “Na ji jiki sosai saboda wasu na min gani-gani, wasu su gaya maka bakar magana ko kuma kora da hali, ba wanda ban gani ba”, saboda sabanin ra’ayin mahaifinta ta Buhari.

A wata hira ta musamman, ta shaida wa Aminiya cewa ta shekara hudu tana aiki a fadar gwamnati ba a biyan ta albashi ba kuma ta yi iya kokari don a biya ta amma ya gagara.

Zainab wadda Shugaba Buhari ne madaurin aurenta ta ce, “Gaskiya ba na yi aiki a Ofishin Maitaimakin Shugaban Kasa ba ne don an biya ni”.

Ta ci gaba da cewa, “Gaskiya na yi kokari da yawa, mutane da suke kusa da shi [Buhari] kullum na gaya musu, na ba su takardu, na yi abubuwa.

“Da na ga ina ta abubuwa ba a gani sai kawai na hakura na ce to mene ne a ciki, shekara hudu ce.

“Abin da ake nuna wa mutane shi ne gwamnati ta rungume ni ana min sha-tara ta arzikai, gaskiya ban ga wannan ba.

“Da an samu an biya ni ba matsala, tunda ba a biya ni ba shi ke nan ai akwai gaba. Gaba ta fi baya yawa”.

Don karantawa ko kallon cikakkiyar hirar da a ciki ta yi wasu muhimmann bayanai masu jan hankali sai a tara ranar Asabar.