Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta ce kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso ba su sanar da ita ficewarsu daga cikinta a hukumance ba.
Kungiyar ta ce a shanun tashi ta ji labarin ficewar kasashen, tana yin iya kokarinta na ganin a daidaita al’amura a tsakaninsu.
Hakan dai ya biyo bayan janyewar dakarun soji daga kasashen da ECOWAS ta yi.
- Nijar, Mali da Burkina Faso sun fice daga ECOWAS
- An kama matar da ke safarar yara daga Arewa zuwa Legas
Kasashen sun sanar da ficewarsu daga ECOWAS a ranar Lahadi.
Kasashen uku, da ke yankin Sahel wadanda sojoji suka hambarar da gwamnatocin dimokuraiyya, sun dauki matakin ne a tare bayan zama da juna.
Wannan dai na dauke ne cikin wata sanarwa da kakakin mulkin sojin Nijar, Kanal Amadou Abdramane, ya fitar.
Sanarwar ta ce, “Al’ummar Burkina Faso, Mali, da Nijar na suna takaici cewa a tsawon shekaru 49 kungiyar ECOWAS ta bar turbar da aka gina ta a kai.
“Kungiyar ta gaza taimakon wadannan kasashe wajen yaki da ta’addanci da rashin tsaro.”
ECOWAS karkashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu, ta yi barazanar daukar matakin soji idan har gwamnatin Nijar ta ki mika mulki ga farar hula a kasar.
Sai dai gwamnatin sojin Nijar ta ki aminta da sharadin da aka gindaya mata, yayin da kasashen Mali da Burkina Faso suka goya wa Nijar baya.
A ranar Lahadi ne dai, shugabannin kasashen yankin Sahel uku, suka dauki matakin ficewa daga kungiyar ECOWAS.
Tun da farko shugabannin ECOWAS, sun dakatar da kasashen uku bayan juyin mulkin da sojoji suka yi musu.