Ministan Shari’a na Najeriya, Abubakar Malami ya bayyana cewa har yanzu bai ayyana tsayawa takarar wata kujerar siyasa ba a zaben 2023 da ke tafe.
Mai magana da yawun ministan, Dokta Umar Jibrilu Gwandu ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai ranar Talata a Abuja.
Ya ce wannan sanarwa ta zama tilas duba da yadda wasu kafofin sadarwa suka yada labarai na karya kan cewa Ministan ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Gwamnan Jihar Kebbi a 2023.
Gwandu ya ce shelanta tsayawa takara a siyasance bai taba zama wani boyayyen abu ba da har wasu kafofin yada labarai suke gaggawar riga malam shiga masallaci.
Ya ce rahoton da aka yada ya samo asali ne daga wadanda suka kagara kuma suke sha’awar Ministan ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara.
Da wannan Gwancu yake mika sakon godiya ga magoyan bayan Ministan da kuma sauran al’umma da suka nuna sha’awarsu ta ganin ya tsaya takarar a 2023.
Dokta Gwandu ya ce idan lokacin da ya dace a sanar da al’umma ya yi, za a ji domin kuwa waka a bakin mai ita ta fi dadi, inda za a sanar da dukkan kafofin watsa labarai, masu ruwa da tsaki, magoya baya da kuma ’ya’yan jam’iyya.