Kwamitin aiki da cikawa domin dakile yaduwar coronavirus na jihar Zamfara ya koka da yadda Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta bayar da sakamakon gwajin masu cutar a ranar Litinin.
Alkaluman na ranar Litinin dai sun nuna an samu sabbin majinyata takwas a Zamfara, yayin da hukumomin jihar suka ce mutum biyu kawai aka samu.
Sakataren yada labarai na kwamitin, Alhaji Mustapha Jafaru Kaura, ya shaida wa wakilinmu cewa a iya saninsu mutane biyu kacal aka tabbatar na dauke da cutar a sakamakon gwajin da aka yi na ranar ta Litinin.
- Coronavirus: Ana neman wani ‘majinyaci’ ruwa a jallo a Zamfara
- Abubuwa bakwai da ba ku sani ba game da ayyukan NCDC
Inda aka yi kuskuren
Sai dai kuma a alkaluman da ta fitar da tsakar daren Laraba a shafinta na Twitter, hukumar ta NCDC ta yi gyara ga alklauman nata.
“An tura sunayen mutum goma, kuma kowanne mutum akwai sunan shi da kuma hoton shi a samfur din, to amma da aka tashi kawo sakamakon sai aka kawo sunayen mutum takwas wadanda ba ma ‘yan asalin jihar ta Zamfara ba ne.
“Misali, mun tura sunan Ibrahim amma sai aka kawo mana sakamako mai dauke da sunan Samuel.
“Kuma mun rubuta masu takardar koke kuma muka nemi cewa su roki gafarar mu amma [har zuwa lokacin nan da nake magana da kai] ba su yi hakan ba kuma basu canza alkaluman ba,” inji shi.
NCDC ta nemi afuwa
Kwamitin dai ya nanata cewa ya zuwa ranar Litinin din da ta gabata jihar na da adadin mutum 76 da suka kamu da cutar a yayin da kuma aka sallami mutum 45 bayan sun warke sannan kuma wasu mutum biyar suka rasa rayukan su.
Haka kuma, a halin da ake ciki, akwai mutum 28 masu karbar magani.
A sanarwar da ta wallafa dai NCDC ta amince da wannan kididdiga ta hukumomin jihar Zamfara, tana ba da hakuri bisa kuskuren da aka samu.
“Ranar 18 ga watan Mayu, an yi kuskuren sanar da sabbin majinyata a Zamfara.
Don haka zuwa 20 ga watan Mayun 2020, Zamfara na da jimillar mutum 76 ne da aka tabbatar sun kamu.
“Muna neman afuwar jihar Zamfara bisa wannan kuskurw, kuma muna jaddada kudurinmu na yin gaskiya da tabbatar da sahihanci yayin ba da samar da alkaluma”, in ji NCDC.