Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce har yanzu bata san adadin daliban da aka yi garkuwa da su a Jami’ar Greenfield dake jihar ba.
Sai dai ta ce ta tabbatar da kisan ma’aikacin jami’ar guda daya yayin da ’yan bindiga suka kai hari Jami’ar da daren ranar Talata.
- Jami’in soja ya yi batan dabo bayan harin ’yan bindiga kan sansanin sojoji a Neja
- Majalisar Dattawa ta amincewa gwamnati ciyo bashin $1.5bn da €995
- Masari na so a binciki musabbabin tashin gobara a Majalisar Dokokin Katsina
Kwamishinan Tsaron da Al’amuran Cikin Gida na jihar, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan ranar Laraba a Kaduna, inda ya ce tuni aka jibge jami’an tsaro a yankin.
’Yan bindigar dai sun kai hari makarantar ne ranar Talata da daddare.
Aruwan ya ce, “Bayan gudanar da bincike da kuma kokarin kubutar da dalibai da ma’aikatan jami’ar, an tabbatar da ’yan bindigar sun kashe wani ma’aikacinta guda daya, sannnan suka yi garkuwa da daliban da dama.
“A yammacin ranar Laraba 21, ga watan Afrilun 2021, jami’an tsaro suka mika sauran daliban da suka ajiye a wurinsu ga hukumar gudanarwar jami’ar,” inji Kwamishinan.
Aruwan ya kuma ce tuni hukumar makarantar ta dukufa wajen kokarin gano adadin daliban da aka yi awon gaba da su ta hanyar bibiyar kundin rijistarsu.