Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta ce ba a sanar da ita hukuncin da kotu ta yanke cewa ta biya Sunday Igboho Naira biliyan 20 saboda shiga gidansa ba bisa ka’ida ba.
Aminiya ta kawo rahoto cewa Mai Shari’a Ladiran Akintola na Babbar Kotun Jihar Oyo, shi ne ya bayar da umurnin biyan kudaden bayan karar da lauyan Igboho, Yomi Aliu ya shigar yana kalubalantar DSS.
- Dokar hana sayar da fetur a jarkoki za ta fara aiki a Jigawa
- Halin da ’yan bindiga ke ciki bayan katse hanyoyin sadarwa
Igboho ya roki kotu da ta tilasta wa hukumar ta biya shi Naira miliyan 500 a matsayin diyya ta musamman kan barnar da aka yi masa a gidansa da kuma motarsa.
Alkalin kotun ya kuma umarci Gwamnatin Tarayya da DSS da su nemi afuwar Igboho tare da mayar masa da kayayyakin da aka lalata masa a gidansa wadanda darajarsu ta kai Naira miliyan biyu.
Da Aminiya ta tuntubi kakakin hukumar DSS, Peter Afunanya, ya shaida mata cewa kotun ba ta aike musu da umarnin ba.
Ya ce, “Kotu ba ta sanar da mu hukuncin da ta yanke ba, don haka ba mu da masaniya.”
An saki wasu mataimakan Igboho da aka kama yayin wasu samamen biyu kan zargin ta’addanci.
A halin da ake ciki Igboho na tsare a gidan yari da ke Jamhuriyar Benin, bayan kama shi da jami’an tsaron kasar suka yi.