Har yanzu ba gano mutum 9 da aka sace a unguwar Dawaki da ke Ƙaramar Hukumar Bwari ta Abuja ba kamar yadda iyalan waɗanda lamarin ya shafa suka shaida wa Aminiya a ranar Talata.
Sai dai tuni rundunar ‘yan sandan Abuja ta musanta wannan iƙirari da cewa mutum takwas kacal aka yi garkuwa da su, kuma an kuɓutar da su baki ɗaya.
‘Yan uwa da maƙwabtan waɗanda lamarin ya rutsa da su sun shaida wa Aminiya a ziyarar da suka kai musu cewa har yanzu ba a ga mutum 9 daga cikin waɗanda aka sace ba.
A ranar Talata ce Aminiya ta ruwaito cewa an sace mutane 20 a unguwar Fulani da ke gundumar Dawaki a yayin da suka yi wa yankin ƙawanya a ranar Lahadi.
Dawaki, wadda ke daura da gundumar Gwarinpa na nan a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kubwa, inda ta zama matsugunnin dubban ma’aikata masu matsakaicin ƙarfi.
Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce a lokacin da suke gudun hijira tare da waɗanda abin ya shafa, sun tsaya a wani yanki da makiyaya ke kiwo da ke wajen gari suka yi awon gaba da mutum biyu.
Wani mazaunin garin, Hosea Christopher, ya ce mutane biyar ne suka tsere yayin da aka fitar da su daga cikin unguwar, sannan sai wasu biyar da suka tsere a kusa da unguwar Dam Usuma da ke kan hanyar Bwari a lokacin da ‘yan bindigar suka yi artabu da jami’an tsaro na DSS.
Ya ƙara da cewa sauran waɗanda harin ya rutsa da su sun yi biyayya ga ‘yan bindigar ta hanyar bin su zuwa maɓoyarsu cikin daji.
Wani mazaunin garin, Usman Uthman ya shaida wa ɗaya daga cikin wakilanmu cewa mutane biyu da aka sace daga gidansu na daga cikin waɗanda aka ceto.
“Sojoji sun dawo da su unguwar a ranar Litinin da yamma,” in ji shi.
Sai dai ya ce wani mutum ɗaya da aka sace daga gidan, mace ce, har yanzu ba a ganta ba.
Murna Lawan, wata mazauniyar unguwar, ta ce mutum ɗaya daga gidanta, mai suna Peter, har yanzu bai dawo ba.