Sanatan Borno ta Kudu, Muhammad Ali Ndume, ya ce har yanzu akwai sauran mutanen da suka maƙale da ba ceto ba, bayan ambaliyar da ta auku a Maiduguri.
Ali Ndume ya jaddada muhimmancin kai musu ɗaukin fito da su daga gidajensu domin ceto su daga rayuwarsu bayan sun shafe kwanaki shida a maƙale a yankunan, bayan aukuwar ambaliyar.
Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakin yasa da kuma buɗe hanyoyin ruwa a yankunan domin mutanen su samu sauƙin fitowa.
Ya ce, “yawancin gidajen da ambaliyar ta shanye ba su da ƙwari sosai, kuma idan suka ci gaba da zama a cikin ruwa, za su iya rushewa.
- Tinubu ya kai ziyarar jaje Maiduguri
- Seaman Abbas: Hedikwatar Tsaro ta ƙaddamar da bincike kan tsare shi
“Yawancin mutanen sun maƙale ne a yankunansu kuma har yanzu ba a iya ceto su ba, saboda da kwalekwale sojoji da gwamnatin jihar da sauran hukumomin tsaro suke amfani wajen aikin ceton,” in ji Sanata Ndume.
Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakin yasa da kuma buɗe hanyoyin ruwa a yankunan domin mutanen su samu sauƙin fitowa.