✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Har yanzu akwai mutanen da suka maƙale bayan ambaliyar Maiduguri —Ndume

Ya roki Gwamnati ta buɗe hanyoyin ruwa a yankunan domin mutanen su samu sauƙin fitowa

Sanatan Borno ta Kudu, Muhammad Ali Ndume, ya ce har yanzu akwai sauran mutanen da suka maƙale da ba ceto ba, bayan ambaliyar da ta auku a Maiduguri.

Ali Ndume ya jaddada muhimmancin kai musu ɗaukin fito da su daga gidajensu domin ceto su daga  rayuwarsu bayan sun shafe kwanaki shida a maƙale a yankunan, bayan aukuwar ambaliyar.

Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakin yasa da kuma buɗe hanyoyin ruwa a yankunan domin mutanen su samu sauƙin fitowa.

Ya ce, “yawancin gidajen da ambaliyar ta shanye ba su da ƙwari sosai, kuma idan suka ci gaba da zama a cikin ruwa, za su iya rushewa.

“Yawancin mutanen sun maƙale ne a yankunansu kuma har yanzu ba a iya ceto su ba, saboda da kwalekwale sojoji da gwamnatin jihar da sauran hukumomin tsaro suke amfani wajen aikin ceton,” in ji Sanata Ndume.

Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakin yasa da kuma buɗe hanyoyin ruwa a yankunan domin mutanen su samu sauƙin fitowa.