A makalata ta makon jiya mai taken ALLAH (SWT) YA SA SHEKARAR 2018 TA FI TA 2017 ALHERI, na yi tsokaci a kan manyan batutuwan nan uku da jam’iyyar APC ta Shugaba Muhammadu Buhari ta yi kamfen din yakin neman zabe da su a shekarar zabe ta 2015. Wadannan batutuwa su ne farfado da tattalin arzikin kasa da ya durkushe a sanadiyar faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya da kuma farfado da matakan tsaro da samun yaki da ‘yan kungiyar Boko Haram a shiyyar Arewa maso Gabas da na ta’addanci irin na sace mutane da neman kudin fansa da rikicin Fulani mikiyaya da manoma da a ’yan shekarun nan ya dauki sabon salon na rikici mai kama da addini da kabilanci.
A waccan makalar, na bi sahun wadancan batutuwa guda uku daya bayan daya da inda suka kwana ya zuwa karshen shekarar 2017, da ta gabata. Na kuma yi alkawarin a wannan makon zan duba wasu daga cikin batutuwan da suka jibanci ayyukan raya kasa da ma na siyasa in fili ya samu, kasancewar wannan shekara ka iya cewa ita ce shekarar yakin neman zaben 2019, kasancewar zuwa yanzu Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, wato INEC, a cikin jaddawalin zaben da ta fitar ta tabbatar da cewa za a yi zaben farko a ranar Asabar 16 ga watan Fabrairun 2019.
Ko shakka babu Gwamnatin APC ta tarayya karkashin jagorancin Shugaba Muhammdu Buhari, duk da ta yi sa’ar samun rinjaye a Majalisun Dokoki na kasa da ma na jihohi da rinjayen gwamnonin jihohi, amma tana ta fama da rigingimu na ciki da wajenta, tamfar ba ta da wancan rinjaye da na ambata. Haka kuwa bai rasa nasaba daga irin yadda madugun tafiyar Shugaban kasa Muhammdu Buhari ya dage a kan jawabinsa na ranar 29 ga watan Mayun 2015, a lokacin da aka kaddamar da shi, inda a takaice ya ce, “Ni na kowane, amma ba ni da kowa. A lokacin da ya yi wancan jawabi, ba dukkan ‘yan kasa suka fahimci inda ya dosa ba, sai ya zuwa yanzu da aka fara ganin kamun ludayin gwamnatin, musamman a kan batun yaki da cin hanci da rasahawa, wanda yake daya daga cikin batutuwan nan uku da jam`iyyar APC ta yi wa `yan kasa alkawarin aiwatarwa a lokacin yakin neman zaben shekarar 2015.
Wannan yaki duk da ya zuwa wannan lokaci ya ci Sakataren farko na gwamnatin Injiniya Babachir Dabid Lawal, bisa ga kwangilar Hukumar tallafa wa `yan gudun hijira da yanki shiyyar Arewa maso Gabas da rikicin Boko Haram ya daidaita da aka samu tsohon Sakataren gwmnatin ya bai wa Kamfanoninsa kwangilar wasu ayyukan Hukumar. Haka Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki yana ta fama da kokarin kwatar kansa daga Kotun da`ar ma`aikata, inda gwamnatin ta gurfanar da shi bisa ga zargin yin aringizo cikin bayyana kaddarorinsa lokacin da yake gwamnan jiharsa ta Kwara.
Duk da irin wadannan misalai da ake da su, amma dai `yan adawa sun ci gaba da cewa yaki da cin hanci da rashawar da Gwamnatin Buharin ta daura ba ya taba shafaffu da mai na mukarraban gwamnatin. Ko a cikin makon jiya sai da tsohon shugaban kungiyar Lauyoyi na kasa babban Lauya Joseph Daudu ya zargi gwamnatin tarayyar da kasa gurfanar da wasu mukarrabanta da ake yi wa hararar sun aikata ba daidai ba a lokacin da suke kan karagar mulki. A kullum dai gwamnatin tarayya na kare kanta a kan a bi ta a hankali sannu ba ta hana zuwa, in an yi hakuri.
Wani batu da gwamnatin ya kamata ta yi wa duban tsaf, kuma ta san yadda za ta bullo masa don gyara, shi ne, irin yadda ake samun sa-in-sa tsakanin wasu manyan jami`anta, alal misali sabanin fahimtar da aka dade ana fama da shi tsakanin Darakta Janar na Hukumar tsaro ta DSS da shugaban riko na Hukumar EFCC, wadda ita ta yi sanadin har ya zuwa wannan lokaci duk da shugaba Buhari ya tura sunan Ibrahim Magun gaban Majalisar Dattawa har kusan karo na uku, amma Majalisar ta ki amincewa da shi, bisa ga zargin rahoton da Hukumar ta DSS ta mika mata, wanda ya yi nuni da cewa Magun bai dace ya shugabanci Hukumar ta EFCC ba. Wannan dambarwa da makamantansu da zan kawo nan gaba suna bukatar lallai Gwamnatin Buharin ta yi kokarin shawo kansu a cikin wannan shekarar.
Akwai kuma batutuwa irin na yin garkuwa da mutane don neman kudaden fansa da yanzu suka game kasa, duk kuwa da irin yadda a kullum rundumomin `yan sanda na jihohi suke baje kolin irin wadancan miyagun mutane da suke cewa sun kama. Wannan ta`addancin garkuwa da mutane ta kai annobar da duk inda ka shiga mota a kasar nan walau ta kanka ce ko ta haya, to, kuwa kana cikin zullumin za a iya yin garkuwa da ku. Akwai kuma batun kawo karshen rikicin Fulani makiya da manoma da sauran matsaloli irin na yau da kullum na gudanar da mulki.
Bari in tsaya nan saboda sauran batutuwan da nike son waiwaya da ya kamata Gwamnatin Buhari ta mayar da hankali a kan aiwatar da su a wannan shekarar, wadda ita ce cikakkiyar shekara daya da ta rage mata na ta gudanar da wasu muhimman ayyukan da `yan kasa za su kara gani da idanuwansu ko su taba da hannayensu ko su taka da kafafuwansu, bayan ci gaba da gudanar da wadancan muhimman ayyuka uku da nike ta maimaitawa a wannan makala.
A cikin jawabinsa na sabuwar shekarar nan Shugaba Buhari ya bijiro da gaggarumin burin da yake da shi na gudanar da wasu manya-manyan ayyukan raya kasa da suka jibanci gina da inganta hanyoyin jirgin kasa irin na zamani da na mota da na inganta wutar lantarki, ayyukan da gwamnatin ta sha alwashin za su shafi dukkan shiyoyin shidda na kasar nan. Ayyukan gina layin dogon ma, bayan sun karade sassan kasar nan, har birnin Maradi na Jamhuriyar Nijar za su dangana. Haka labarin yake akan inganta tashoshin wutar lantarki, ta yadda masana`antu za su farfado ayyukan yi ga `yan kasa su kara samuwa.
Ko shakka babu lokaci na kurace wa wannan gwamnatin, don haka kamar yadda na fadi tun farko yanzu ya kamata ta tashi tsaye haikan, ko ta kara samun karbuwa ga `yan kasa, musamman yanzu alamu na nuna cewa Shugaba Buhari zai sake neman takarar shugabancin kasar nan a badi in Allah Ya kai rai. Tabbas Buhari ya kwan da sanin akwai gagarumin bambanci tsakanin zaben 2015, da kuma mai zuwa na 2019, duk kuwa da talakawan kasa masu zunzurutun kuri`u suna tare da shi.
Ta`aziyya ga iyalen marigayi Alhaji Lawai Kaita
Wannan fili yana mika ta`aziyyarsa ga daukacin iyalan marigayi Kankiyan Katsina Alhaji Sada Nadada, da yanzu suke karkashin jagorancin Kankiyan Katsina Alhaji Musa Hassan Sada, bisa ga babban rashin uba, kaka, da ma dan uwa Alhaji Muhammadu Lawai Kaita tshohon gwamnan tsohuwar Jihar Kaduna da Allah Ya yi ma rasuwa a ranar Talatar makon jiya a wani assibiti mai zaman kansa a Abuja, bayan ya sha fama da jiyya. Allah Ya gafarta masa Ya sa ya huta Ya yaye masa duhu da azabar kabari Ya kuma duba bayansa, tare da ba da hakurin rashin, amin summa amin.