Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ba domin damina ta yi kyau a shekara biyu a jere ba, day a yi gudun hijira daga Najeriya.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a Fadar Shugaban kasa da ke Abuja lokacin da ya karbi bakuncin Majalisar Sarakuna ta kasa a karkashin jagorancin Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar a ranar Litinin da ta gabata.
Shugaba Buhari ya ce: “Mun ci sa’a bara da bana, damina ta yi kyau. Da ba ta yi kyau ba ina tabbatar muku da na fara tunanin kasar d azan gudu. Amma Allah Ya amshi addu’o’in ’yan Najeriya da dama; damina ta yi kyau a bara da bana daga rahotannin da nake samu kuma abu ne mai kyau. Muna godiya ga Allah kan samun haka. Ba domin haka ba da an shiga matsaloli da dama a kasar nan.”
Shugaban kasar ya ce, gwamnati ta san iyakokinta, don haka ne ta yanke shawarar ta inganta cibiyoyinta yayin da ’yan Najeriya kuma suka amince su zauna su yi aiki tare.
Ya dora alhakin kuncin tattalin arzikin da ake ciki a kasar nan kan almubazzaranci da dukiyar jama’a da aka shafe shekaru ana yi.
Shugaba Buhari ya yi alkawarin ci gaba da gudanar da ayyuka da tsare-tsaren da za su inganta rayuwar talakawa, inda ya ce, kasar nan ya kamata ta yi amfani da dimbin jama’arta don ci gabanta. Ya ce tsaro da tattalin arziki da yaki da almundahana za su ci gaba da kasancewa manyan abubuwan da gwamnatinsa za ta fi bai wa fiffiko.
Tun farko a jawabin Sarkin Musulmi, ya bukaci Shugaba Buhari ya kara zage damtse “don fuskantar dimbin kalubalen jagorantar kasar nan zuwa ga tudun mun tsira.”
Ya ce sarakunan gargajiya na kasar nan za su ci gaba da nasihar a zauna lafiya da yin adalci da kuma gaskiya da rikon amana.
Sarkin Musulmin ya bukaci Shugaba Buhari ya dauki bayanan da sarakuna daga shiyyoyi shida na kasar nan suka yi a matsayin abin da yake bukata don yin aiki wurjanjan ga kasar nan.
Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi, wanda ya yi magana a madadin takwarorinsa na Kudu maso Yamma ya ce: “Za mu ci gaba da nasiha ga jama’armu ta yadda za mu ci gaba da tabbatar da zaman lafiya a kasarmu, za mu ci gaba da jan kunnen matasanmu kan illar kalaman tunzurawa. Ba za mu bar gwamnati kadai da aikin bunkasa kasar nan ba, wajibi ne mu hada hannu da ita. Kuma muna ba ka tabbacin za mu tallafa wa duk shirye-shiryenka.”
Shi kuwa Lamidon Adamawa wanda ya yi magana a madadin sarakuna Arewa maso Gabas, ya ce, ’yan Najeriya suna cike da farin cikin dawowar Buhari daga hutun jinya da ya yi a birnin Landan cikin koshin lafiya, inda ya yi alkawarin cewa “Za mu ci gaba da rokon Allah Ya karfafa ka, kuma Ya ba ka karfin jiki da na hali ta yadda za ka ci gaba da yi wa kasa hidima.”
Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, ya ce sarakuna daga yankin Arewa maso Yamma suna yaba sadaukar da kan Shugaban kasa wajen tabbatar da zaman lafiya.
Shi kuma Gbom Gwom na Jos, Jacob Buba Gyan wanda ya yi magana a madadin sarakunan gargajiya daga Arewa ta Tsakiya cewa ya yi: “Batun lafiya da tsaro ba batutuwa ba ne da za a sanya siyasa a ciki, batutuwa ne da dukanmu za mu hada kai mu magance su domin kasar nan ta ci gaba. Muna yaba kokarinka a bangaren tsaro da aikin gona. Kuma a ’yan kwanaki daidai lokacin da muke murna zaman lafiya ya dawo a Filato, sai aka kawo cikas ta hanyar kai hari a kauyen Ancha da ke karamar Hukumar Bassa a Jihar Filato inda ya yi sanadin mutuwar mutum 20.”
Sarkin Nembe, Cif Edmond Daukoro wanda ya yi magana a madadin Kudu maso Kudu ya ce: “Mun san akwai dar-dar a nan da can, amma mu sarakunan gargajiya ba mu ci siyasa. Akwai bukatar a magance matsalar tattalin arziki. Kasancewar mun fito daga yankin da ke samar da mafi yawan dukiya ga kasa, duk da cewa nan gaba kadan za a fadada hanyoyin tattalin arzikin kasar, amma kafin a fadada akwia bukatar mu kare wanda muke da shi. Muna jin dadi mu yi aiki domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ta yadda za dukanmu za mu ga amfanin albarkatun da muke da su.”
Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya na shiyyar Kudu maso Gabas Cif Eberechi Dike ya ce: “Zukatanmu suna cike da farin cikin dawowarka. Ka yi musabaha da mu lokacin da ka shigo, wannan yana nuna ka yi amanna da kasancewar Najeriya kasa daya. Mun yi maka addu’o’i kuma ka dawo. Mun yi maka addu’o’i ne saboda manufarka ga Najeriya mai kyau ce. A matsayinmu na ’ya’yanka idan muka yi kuka, aikinka ne ka nemi mu daina kukan cewa za ka gyara duk abin da yake sanya mu kuka kamar munanan hanyoyi.”