Maruru wani nau’in ciwon fata ne da kwayoyin cuta kan kawo kuma shi ma za a iya kare kai daga kamuwa da shi. Wannan ciwo kan zo da kuraje masu durar ruwa kuma masu ciwo ko zogi. kwayoyin cuta na bacteria da ake kira Staphylococcus aureus, wadanda ke rayuwa a saman fatar jikin dan Adam, su ne suke samun damar shiga cikin fatar ta kofofin gashi, su kawo wannan ciwo. Wato dai su kwayoyin wadanda ke saman fatar ba sa kawo wani ciwo har sai sun samu damar shiga cikin fata ta kofar gashi.
Har ila yau, ba kamar yadda mukan ce ba a al’adance, cewa sai mutum ya tsallaka fitsarin da gwauro ya yi ne wadannan kuraje ke fitowa, babu wata alaka tsakanin fitarin gwauro da wannan kurji, wanda idan ya fito a gwiwa ake cewa fitsarin gwauro.
Kusan kowa a rayuwarsa ya taba samun maruru wanda ya fashe ya tafi da kansa ba tare da an yi masa magani ba. Amma idan yana yawan fitowa to an fi ganin wannan a mutanen da ba su faya kula da tsabtar jiki ba, yara ne ko manya, duk da dai an fi samu a yara din saboda raunin garkuwar jiki. Akan samu ma sosai a mutane masu yawan gumi ko zufa ko masu kiba ko masu ciwon suga, wadanda ba su shan magani sosai, domin kwayar bacteria tana son sugan da yakan taru a fatar mai ciwon suga, kuma shi kansa ciwon suga kan raunata garkuwar jiki ko wadanda garkuwar jikinsu ta karye ko wadanda abinci mai gina jiki bai wadace su ba ko mashaya barasa, domin giya takan hana cin abinci, wanda shi kuma abinci shi kan ba da karfin garkuwar jiki.
Yaya Alamun Wannan Ciwo Yake?
Maruru kan zama abin damuwa ainun ga mutane wadanda musamman yakan fito masu a kai-a kai, wato yakan zo ba sau daya ba ba sau biyu ba. Duk da ya fi fitowa lokacin zafi, a kan iya samunsa a kowane yanayi. Za a iya ganinsa a wuraren da gumi ya fi fitowa kamar hammata, matse-matsin cinyoyi, karkashin mama, ko a gwiwar hannu ko ta kafa da fatar gadon baya ko a wurin kasumba ga masu yawan aski da rezar da ba ta da tsabta. Wato yakan iya fitowa a fatar fuska kusa da hanci ko gashin ido ko fatar kunne duka. Yakan fito ma a karkashin fatar kugu, inda ake allura, idan aka yi allurar ba tare da an goge saman fatar da magani ba, wato kamar tsinin allurar ne ke shigar da kwayoyin ciki.
Akwai zogi sosai idan ya fito saboda fatar wuraren damewa take sosai, musamman idan ya fara durar ruwa kafin ya fashe saboda kuma cinye karkashin fata da kwayoyin suke. Wani lokaci yakan fito dan karami, wani lokaci kuma ya fito babba ko kananan su hade su zama babba a wuri guda. Yakan duri ruwa ya fashe da kansa bayan kamar kwanaki 5 zuwa 10.
Akwai sunayen maruru daban-daban a likitance dangane da wurin da ya fito. Na gashin ido sunansa daban da na fatar jiki. Sauran alamun sun hada da jin dan zazzabi da kasalar jiki idan ya fito. Sa’annan za a ji kaluluwar saman wurin ta kumbura. Idan a gwiwar kafa ko cinya ya fito, za a ji kaluluwar matse-matsin cinyoyi sun kumbura. Idan a hannu ne za a ji kaluluwar hammata sun kumbura suna zogi. Idan a fuska ne a ji na wuya sun kumbura. Duk ba wani abin damuwa ba ne domin su wadannan kaluluwa (lymph nodes) abokanai ne da kwayoyin garkuwar jiki, suna tattaro kwayoyin cutar ne daga karkashin fata su rike su wuri guda don kada su samu su shiga jini a samu matsalar da ta fi ta maruru.
Hanyoyin Kariya Daga Wannan Ciwo:
A wadanda wannan ke fitowa a kai-a kai, dole su bi wadannan hanyoyin kariya:
1-Kiyaye tsabtar jiki da ta kayan sa wa ta hanyar yin wanka akalla sau daya a rana da yawan wanke suturar sa wa a kalla bayan sa wa biyu.
2-Yawan aske gashin hammata da na matse-matsin cinyoyi zai rage fitowar maruru.
3-Dole kuma askin sai da abu mai tsabta ko wanda aka tafasa idan an taba amfani da shi a baya.
4-Idan hakan bai yi maganin maruru ba, za a iya soma wanka da sabulu mai kashe kwayoyin cuta na fata wato antiseptic, musamman idan mutum yana yawan fama da matsalar. Za a iya shafa sabulun ma a wuraren da aka yi aski ko gyaran fuska, don kare aukuwar hakan. Wasu za su ga ana shafa musu man kashe kwayoyin cuta na spirit bayan an yi gyaran fuska, to duk domin a kiyaye aukuwar irin wannan matsalar ne.
5-Idan har wa yau ba su daina damun mutum ba to dole a je a yi gwajin suga, a tabbatar ba ciwon suga ne ke damun mutum ba.
6-Idan maruru ya fashe da kansa (kada a fasa shi ta karfi), sai a wanke wurin da ruwa da sabulu na musamman, wato antiseptic, a tsane wurin da sauri domin in ruwan marurun ya taba fata mai lafiya ba a wanke da wuri ba, zai iya sake dawowa.
7-Cin abinci da ’ya’yan itatuwa na marmari kan gina kwayoyin halitta na garkuwar jiki wadanda su ne idan kwayar cutar ta shigo cikin fata kan yi maganinta.
8-Idan ya dade yana zogi kuma bai fashe da kansa ba, kamar wanda ke fitowa bayan an yi allura, dole a je asibiti a tsaga, a fitar da ruwan da wuri, a karbi kuma magunguna.
9-A je a ga likitan fata idan mutum na yawan fama da wannan matsala, domin a duba a tabbatar maruru ne, kuma a ba da maganin da ya dace, domin a wasu lokuta idan abin ya yi yawa sai an ba da magungunan kashe kwayoyin cuta don magance su da ma kiyaye yawan fitowar tasu.