Azumin wata Ramadan wani tsagi ne na shika-shikan Musulunci da ya wajabta a kan kowane baligi mace ko namiji, kuma mai cikakkiyar lafiya.
An gano yin azumi na tattare da wani alfanu ga jikin dan Adam, lamarin da ke inganta lafiya da kuma kora kamuwa da wasu cututtuka da ka iya zama barazana.
- Yadda rashin lantarki da tsadar fetur ke kassara masana’antu
- Abubuwan da aka yi rangwame a kansu da azumi
Aminiya ta tattauna da Dokta Bashir Jamilu na asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, don jin yadda azumi ke inganta lafiyar jikin mutum, inda ya bayyana mana wadannan hanyoyin:
1. Rage yawan sukarin jikin mutum
A ka’ida dai jikin mutum ba ya shiga yanayin azumi sosai sai an shafe sa’a takwas bayan abinci na karshe da mutum ya ci. Wannan shi ne lokacin da cikin mutum ya gama narkar da abubuwan gina jiki da ya samu daga abincin.
Jim kadan bayan wannan lokacin, jikin mutum zai koma wa sikarin da ke adane a hanta da tsokar jiki domin samun karfi. Bayan dan lokaci kadan, idan sukarin ya kare, to kitse ne zai koma wuri na gaba da jiki zai iya samun karfi daga gare shi.
2. Kone kitsen jiki
Idan jikin mutum ya fara kone kitse, wannan na taimakawa wajen rage kiba da rage maiko da kuma rage yiwuwar mutum ya kamu da ciwon siga.
3. Rage kiba
Sakamakon kone sukari da kitse a jikin dan Adam, hakan na sa nauyi da kibar dan adam ya ragu wadda hakan ce manufar motsa jiki.
4. Inganta lafiyar zuciya
Binciken likitoci ya gano kaso 31.5 na mutanen da ke mutuwa; na mutuwa ne sakamakon cututtuka da suka shafi ciwon zuciya.
A cewar Dokta Bashir azumi na inganta lafiyar zuciya kasancewar yana kone kitse sannan ya kawar da teba, al’amarin da ke daidaita sauka da hauhauwar jini.
5. Inganta garkuwar jiki
Da zarar an kone sukari da kitse kuma an rage teba sannan an samu lafiyar zuciya to dan adam ya kan samu garkuwa da kuzari fiye da lokacin da ba ya azumi.
Ita kuma garkuwa na taimaka wa jiki ne wajen hana kamuwa da wata cuta ko kuma cutar ba za ta yi tasiri a jikin dan adam ba.
A cewar Dokta Bashir, azumi na da matuka fa’ida ga jikin dan Adam, wanda yana taimakawa sosai wajen dakile da kuma inganta garkuwa jiki.