Rikicin hana shaye-shaye a unguwar Mararraba dake Birnin Kano ya haddasa rasuwar wani matashi, Huzaifa Wada Ibrahim.
Matashin dai ya yi baƙin jini ne wurin ƴan shaye-shayen saboda dokar hana shaye-shaye da ya rubuta a jikin bangon gidansu.
Mahaifiyarsa, Hajiya Rabi Wada ta ce rikici ne ya ɓarke tsakanin maƙwabcinsu dake cajin waya da kuma wani matashi da yake shan wiwi a gefen shagonsa.
Kotu ta daure lauyan bogi wata 15 a Kano
Gwamnan Kano ya raba wa Kwamishinoninsa 19 ma’aikatu
A cewarta mai shan wiwin yaƙi daina wa har ma ya kwashe mai cajin waya da mari.
Ta ce “shi yaro da ma ya na da wani ciwo sai ya faɗi. Ya na faɗuwa sai aka kai shi asibiti.”
Shi wannan mai cajin wayar abokin ɗanta Huzaifa ne.
Bayan an dawo da shi daga asibitin ne kuma sai Huzaifa dake cikin gida ya ji hayaniya a waje ya tashi ya fita domin ganin me ke faruwa.
Ƙanwar Huzaifa, Safiyya Wada ita ce ta bi shi waje.
Ta ce ya na fita sai suka afka masa su uku.
“Su ka dinga caka masa wuƙa a ƙirjinsa, ya taso zai shiga gida sai ya faɗi a ƙofar gida.”
A na sa ɓangaren, mahaifin Huzaifa, Alhaji Wada Ibrahim Namangu ya roƙi mahukunta su bi musu haƙƙin ransa.
Kakakin ƴan sandan jihar Kano, SP Haruna Kiyawa ya shaidawa Aminiya cewa ba shi da cikakken rahoton abin da ya faru amma zai sanar da mu da zarar ya gama tattara bayanai.