Kungiyar Hamas ta kashe adadi mafi yawa na sojojin Isra’ila da suka mamaye Zirin Gaza a rana guda.
A ranar Talata Rundunar Sojin Isra’ila ta koka da cewa ba a taba yi wa sojojinta masu yawa haka kisa a rana guda ba, tun da suka fara kai samame a Gaza a watan Oktoban 2023.
Kakakin rundunar, Daniel Hagari, ya ce, Hamas ta kashe sojojin Isra’ila 24, da wasu sojojin ko-ta-kwana 21 wadanda rokokin Hamas suka tarwatsa motar yakin da suke ciki a kusa da wasu gine-gine.
Daniel Hagari ya ce da kyar aka gano gawarwakin sojojin Isra’ilan da Hamas ta kashe a cikin baraguzan gini a ranar Litinin.
- Uba ya kashe dansa kan tutar jam’iyyar siyasa
- An kama shugaban karamar hukuma kan yunkurin kashe Shugaban Majalisar Benuwe
Wannan ragargazar da sojojin na Isra’ila suka sha na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen duniya ke kokarin ganin an samu maslaha a rikicin.
Hakan kuma na zuwa ne da daidai lokacin da wani babban jami’in gwamnatin Amurka ke shirin zuwa yankin na Gabas ta Tsakiya, domin sanya baki a sako karin mutane da aka yi garkuwa da su.
Kafofin yada labaran Amurka sun ruwaito cewa yarjejeniyar za ta kunshi tayin da Isra’ila ta yi na tsagaita wuta na tsawon watanni biyu.
Ofishin Jinkai na Majalisar Dinkin Duniya (OCHA) ya sanar cewa musayar wuta ta tsananta a Gaza, sakamon samamen Isra’ila a yankin Khan Yunis.
OCHA ya ce sojojin Isra’ila sun kai hari da makaman atilare da jirage marasa matuka kan babban ofishinsaa da ke Khan Yunis inda suka jikkata mutanen da suka samu mafaka a harabar ofisihin.
Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya sun bayyana cewa al’umma na fuskantar barazanar rashin abinci a Gaza, inda akalla mutum miliyan 1.7 suka rasa muhallansu.