Kimanin shekara daya ke nan da tsare wasu ’yan kasuwar canji ta Wapa da ke Kano kan zargin alaka da tura kudade ga masu ayyukan ta’addanci, ba tare da iyalansu sun sake jin duriyarsu ba.
Iyalan ’yan canjin sun ce tun da hukuma ta gayyace su, har yanzu babu wani kwakkwaran bayani a kansu; Ba a bayyana laifinsu ba, ba a gurfanar da su ba a kotu, sai ja wa iyalan rai aike ta yi, sannan duk hukumar da ta dace sun je, amma babu wani bayani mai gamsarwa.
- ‘’Yan canji da manyan mutane ke daukar nauyin ta’addanci’
- Lauyoyin Abduljabbar na neman a dawo da shaidar gwamnati na farko don su yi masa tambayoyi
Mata da ’ya’ya da kuma iyayen ’yan canjin, sun bayyana hakan ne a wani tattaki zuwa Fadar Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, domin neman shi da sauran mahukunta su sanya baki a lamarin.
Iyalan nasu sun bayyana mawuyacin halin da suka shiga tun bayan tsarewar, inda daya daga cikin matan, Halima Jibrin Garo, ta ce, “Tun da aka gayyace su tsawon wata 11 ke nan, har yanzu ba mu samu wani gamsasshen labari ba.
“Muna nan zaune mu da ’ya’yanmu, ga rayuwa ta yi tsada, yara makaranta na neman gagarar su, abinci na neman garar mu, mutanen da suke tallafa mana su ma abin kansu ya ishe su.”
“Saboda haka muke neman tallafi ga gwamnati ta dubi Allah ta taimake mu ta dubi wannan al’amarin da halin da muke ciki.
Halima ta ci gaba da cewa, “Ni kaina an bar ni da ciki wata daya, har na haihu yanzu yarona na da wata hudu amma har yanzu babu labarin mahaifinsa; a ciki akwai wadda ta haifi ’yan biyu, wadanda aka yi wa CS a cikinmu suna da yawa; Don Allah a duba mu, a karbi kokenmu.”
Wani daga cikin kananan yaran da suka halarci tattakin ya ce, “Yanzu ba ma zuwa makaranta kuma a gida da kyar muke samun abin da za mu ci, uwayenmu na shan walaha sosai.”
Sai ja mana rai ake yi —Iyayen ’yan canji
Mahaifiyar daya daga cikin ’yan canjin mai suna Alhaji Abdullahi Usman, ta ce, “Ba mu san laifinsu ba, a kasuwa ne aka gayyace su, tun da ya fita ba mu ji labarinsa ba, sai sa mana rana ake, a ce yau, a ce gobe.
“Don Allah a taimaka mana, kusan shekara guda ke nan ba mu ji labarinshi ba, ba mu gan su ba.”
Ita ma mahaifiyar Abdulrahman Dukawa, ta koka bisa yadda ta ce hukuma ke ta yi musu karairayi.
Ta ce “’Yarsa ta rasu dayar kuma ta fama da matsanancin rashin lafiya, duk bai sani ba.
“Tsakani da Allah abin da ake mana shi ne babbar damuwarmu; Afito da su, in ma hukunci ne su fuskanci shari’a, akalla dai za mu san suna nan da ransu kuma lafiyarsu.”
‘Mijina da ’yan uwansu uku aka tsare’
Zannira Uwaisu, wadda ita ma mijinta da kannansa ke tsare, ta ce, “Surukata na kwance ba ta da lafiya saboda an tsare ’ya’yanta huku a wannan abu.
“Kishiyata mai ’ya’ya tara ita ma tana kwance; Don Allah a taimaka mana, ’ya’yanmu 16 ba sa zuwa makaranta, rayuwa ta yi mana kunci.”
“Ko a waya ma ba mu ji su ba, ballantana mu gan su. Yau a ce mana za a suna a kotu, gobe a ce mana za a sauna a kotu, sai ka ji abu dai shiru.
“Babu labari, Sai a ce alkali ba zai samu zaba ba. Sau biyu ana ce mana alkalai sun yi ritaya,” a kotun mai lamba 4 a Abuja,” inji Halima.
Ta ce abin da suke so shi ne, “A matsayin Mai Martaba na uban talaka da mai kudi, Mai Martaba ya shiga wannan magana, ya taimake mu, a kalli kanann yaran da aka tafi aka bar mu da su, makaranta tana neman gagarar su. Islamiyya ma sun fara gajiya da su.”
‘Har Abuja mun je, amma shiru’
Nasiba, matar Mansur Muhammad Usman, wanda aka tsare tare da kaninsa Zaidu ta ce, “Har Abuja mun je, aka ce za a zo da su kotu za mu gan su.
“Har muka je muka dawo, shari’ar dai ba za a ce ba a zauna ba, amma babu wani kwakkwaran abin da aka yi.
“Haka muka je muka dawo, kuma duk hukumar da ta dace mu bibiya, duk inda muka bi sai a yi shiru.”
Ta ce hukumar DSS ta gayyaci mazajen nasu ne kan zargin ‘alaka’ a harkarsu ta canji, amma ba ta bayyana takamaiman abin da ake zargin su da aikatawa ba.
A cewar Nasiba, da farko hukumar ta gayyaci mijinta ne a ranar Juma’a, sannan ta sake shi cewa ba shi da laifi, amma daga baya ta sake cewa ya koma. “Tun da suka tafi, har yau babu labarinsu.”
‘Gano Masu Daukar Nauyin Ta’addanci 96’
A ranar da matan suka ziyarci sarkin ne, Gwamnatin Tarayya ta sanar cewa ta bankado wasu masu samar da kudi guda 96 don daukar nauyin ta’addanci da kuma masu alaka da kamfanonin hada-hadar kudi 424 da ke ba da gudunmuwar ta’addanci a kasar.
Ministan Yada Labarai da Raya Al’adu, Lai Mohammed ne ya bayyana hakan, yayin wani bayani kan yaki da cin hanci da Gwamnatin Shugaba Buhari ke yi.
A cewarsa, Hukumar Tattara Bayanan Sirri kan Kudade a Najeriya (NFIU) ta gano masana’antu 123 da kamfanoni canji kudade 33 da ke da alaka da ’yan ta’adda a kasar.
Ya ce, “A bangarenta (NFIU), a sharhin da ta yi kan kudade na 2020-2021, ta bayyana masu hada-hadar kudade 96 da ke da alaka da ’yan ta’adda a Najeriya.
“Akwai kuma wasu 424 da ke samar da kudade domin ta’addanci da suka hadar da kamfanoni 123, da kuma na masu musayar kudi 33.
“Bugu da kari an gano wasu 26 da ake zargi da ta’addanci da wasu bakwai kuma da ake hada kai da su kan harkokin ta’addanci, inda wannan bayani ya kai ga kama 45 da ake zargi wadanda kwanan nan za a gabatar da su a gaban kotu,” a cewar Ministan.