Yayin da mahajjata ke shirin tsayuwar Arafa a kasar Saudiyya ranar Juma’a, kimanin maniyyata 754 daga Jihar Kano ne ba su sami tafiya ba.
Daga cikinsu kuwa har da Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazan jihar, Muhammad Abba Danbatta tare da wasu daraktoci da jami’an hukumar.
- Akwai hannun ‘na gida’ a harin kurkukun Kuje – Ahmed Lawan
- An cafke ’yan sandan da aka kama suna waya da maharan kurkukun Kuje
Maniyyatan da ba su su sami tafiya Kasa Mai Tsarki ba sun koka kan abin da suka kira rashin adalci da aka yi musu na rashin sanin halin da suke ciki tun da farko.
Aminiya ta ziyarci sansanin alhazan jihar, inda maniyyatan suka bayyana mata cewa hukumar alhazan ta yi watsi da su a cikin ruwan sama da cizon sauro.
Malama Hauwa Babba daga Karamar Hukumar Ungoggo ta zargi jami’an hukumar da zaluntar su.
‘An zalunce mu, an yi watsi da mu’
“Ba abin da zan ce sai dai in ce an cuce mu, mun biya kudinmu shekaru uku da suka wuce, amma ga mu an bar mu muna ragaita babu tafiya Makka babu kuma kudinmu.
“Sun zalunce mu sun tafi sun bar mu a gida; Allah Ya saka mana cutar da suka yi mana,” inji ta.
Ita ma wata manniyaciya, Malama Aisha Musa daga Karamar Hukumar Tudun Wadan Dankadai ta yi Allah wadai da halin ko-in-kula da shugaban hukumar alhazan yankinsu ya nuna musu.
“Shi shugabanmu ba ya zuwa wurinmu ballantana mu gan shi mu ji dadi; Idan mun kira shi wayarshi a kashe.
“To wannan cuta ce aka yi mana kuma ba za mu yafe ba, domin an bar mu a cikin halin rashin kulawa da rashin tabbas.
“Ga shi tun da muka zo wurin nan mu ke ciyar da kanmu safe da rana da dare, sau daya rak aka ba mu abinci, leda daya mu uku.”
‘Ina cikin damuwa’
Shi ma wani maniyyaci da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa ya shiga cikin damuwa sanadiyyar tafiyar da bai samu yi ba.
Ya ce, “Innalllahi wainna ilaihi rajiun! Ai fadin halin da muke ciki ba zai yiwu ba, gaskiya ban taba shiga irin wannan yanayi ba.
“Ba abin da zan ce sai dai Allah Ya yi mana sakayya bisa wannan hali da shugabanminmu suka yi mana.
“Wallahi su ne suka janyo mana wannan lamarin sakamakon rashin shiri na gaskiya da ba su yi game da harkar aikin Hajji.”
‘Mun bar su da Allah’
Shi ma Bala Uzairu Magaji daga Ungogo, ya bayyana cewa duk da cewa hukumar ba ta kyauta musu ba, amma ba za su dauki matakin zanga-zanga ba, sai dai za su dauki matakin hakuri.
Ya shaida wa Aminiya cewa, “Babu matakin da za mu dauka na zanga-zanga ga gwamnati.
“Mun sami tarbiyyar hakuri daga malaman bitarmu, muna fatan ba za a sake maimaita irin hakan a badi ba.”
Wani mamiyyaci, Tasiu Ado Musa ya zargi hukumomi da hana su yin Aikin Hajjin bana.
“Bayan duk mun cika ka’idoji da hukumomi suka sharadanta mana tun daga kan cika kudinmu har zuwa allurori da gwaje-gwajen lafiya, amma sai ga shi mun kasa tafiya.
“Mun yi wahala ba kadan ba sai dai kawai Allah Ya bi mana hakkinmu. Allah ba ya zalunci.
“Sun kwashe mutanen da suke so su tafi, amma mu sun bar mu,” kamar yadda ya bayyana mana.
Shi ma wani maniyyaci ya bayyana cewa abin da yake damun sa shi ne yadda zai fuskanci iyalinsa da batun rashin tafiya Kasa Mai Tsarki da bai yi ba.
“Mun yi sallama da iyalinmu da ’yan uwanmu cewa za mu wuce Kasa Mai Tsarki, amma sai ga shi lamarin ya canza.
“Yanzu ni yadda zan fuskanci iyalina nake tunani; Na san yanzu suna nan suna cikin bakin ciki saboda halin da muka sami kanmu a ciki. Allah dai Ya ba mu ladan niyya,” in ji shi.