✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hakimai da dagattai 19 sun yi murabsu a Sakkwato

Hakimai da dagattai 19 sun yi murabus a Masarautar Gobir da ke Jihar Sakkwato

Hakimai da dagattai 19 sun ajiye rawaninsu a Karama Hukumar Sabon Birni da ke Jihar Sakkwato domin shiga siyasa.

Yankunan da sarakansu suka yi murabus su ne Sabon Birnin Gabas da Tsilba da Sabon Garin Danbaki da kuma Magajin Dawakin da Dan Faru da Zumbuli da Dawakin da Kanwuri da Hande da Sabon Fegi, Tudun Dankusu da Alhazzai da sauransu, inda suka bayyana goyon bayansu da Sanata Ibrahim Lamido

Sun yi murabus daga sarauta ne mako biyu bayan Hakimin Sabon Birni, Alhaji Abdullahi Muhammad Bawa, ya sauka daga sarautarsa a a ranar 16 ga watan Oktoba, 2024, da cewa, “Na ajiye sarauta ne domin in goyon bayan tafiyar siyasar Sanata Ibrahim Lamido.”

Daya daga cikin wadanda suka ajiye sarautar, Dagacin Taka-Tsaba Alhaji Lauwali Shuaibu, ya shaida wa manema labarai a Sakkwato cewa, “Mun mika takardunmu na sauka daga sarauta, amma babu wanda ya kira mu don jin korafinmu.”

Ya ce sun dauki matakin ne bisa la’aikari da yadda Sanata Lamido ya jajirce wajen kula da jin dadinsu da kuma “zuwa ya kawo mana dauki a duk lokacin da ’yan ta’adda suka kawo mana hari.

“Goyon bayanmu zai karfafi Sanata Lamido ya ci gaba da kyakkyawan aikin da yake wa al’ummarmu”

Alhaji Jamilu Gwanda Gobir, Ubandoman Sarkin Gobir, marigayi Isa Muhammad Bawa, ya ce sun yi haka ne domin ceto yankin Gobir.

“Kimanin sarakai 10 ne suka mara min baya muka ajiye rawunnanmu kuma ni ne na rike sarautar Ubandoma na tsawon shekara tara,” in ji shi.

Tsohon Ubandoman ya ce sarakunan da suka ajiye kujerunsu sun yi alwashin ba za su goyi bayan wani dan siyasa ba, sai wanda ke kula da jin dadin al’ummarsu.