✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hakikanin ibada a Musulunci

Daga Malam Muhammad Sani HarunBabban Masallacin Izala na Sabo Ibadan Godiya ta tabbata ga Allah Mahaliccin dukkan komai, kuma Shi a kan komai Mai iko…

Imam Muhammad Sani Haruna, Limamin Babban Masallacin Izala na Sabo IbadanDaga Malam Muhammad Sani Harun
Babban Masallacin Izala na Sabo Ibadan

Godiya ta tabbata ga Allah Mahaliccin dukkan komai, kuma Shi a kan komai Mai iko ne. Na shaida babu wanda Ya cancanci a bauta masa da gaskiya sai Allah, Shi kadai ba Ya da abokin tarayya a gare Shi. “Ya ba kowane abu siffarsa kuma Ya shiryar (da shi hanyar rayuwarsa).” Kuma na shaida lallai Annabi Muhammad BawanSa ne kuma ManzonSa ne, ya haska duhu da sunnarsa, kuma ya haskaka mana hanyar shiriya. Allah Ya Allah Ka kara tsira da aminci a gare shi da alayensa da sahabbansa da kuma taslimi.
Bayan haka, lallai Allah Ma’abucin tsarki da daukaka Ya bayyana mana hakikanin dalilin halittarmu. Sai Ya ce: “Kuma ban halitta aljanu da mutane ba sai domin su bauta Mini.” (k:51:56). Kuma Annabi Nuhu da sauran Annabawa da Manzanni (AS) sun fada wa mutanensu cewa: “Ku bauta wa Allah, kuma ba ku da wani abin bauta a waninSa.” Kuma Allah Mai girman daraja Ya bayyana cewa Ya aiko manzanni ga al’ummomi ne domin a bauta maSa. “Kuma lallai ne, hakika, Mun aika a cikin kowace al’umma da wani Manzo (ya ce), “Ku bauta wa Allah kuma ku nisanci dagutu.” To, daga gare su akwai wanda Allah Ya shiryar, kuma daga cikinsu akwai wanda bata ta wajaba a kansa.” (k:16:36).
Kuma Allah Mai girma da daukaka Ya umarci ManzonSa (SAW) da ya bauta maSa har sai mutuwa ta dauke shi. Sai Ya ce: “Ka bauta wa Ubangijinka har sai mutuwa ta zo maka.”
Mece ce wanna bauta da Allah Ya halitta mu dominta, kuma Ya umarce da aikata ta a cikin nassoshi da yawa?
Wasu mutane suna zaton ibada ko bauta ba ta wuce ’yan raka’o’in da mutum yake sallata ba, ko ranakun da yake azumta ko faralin Hajji da yake saukewa, ko zakkar dukiya da yake fitarwa! Wanna fahimta ina rantsuwa da Allah mummunar fahimta ce.
Lallai ibada ko bauta, ya ’yan uwana masoya Allah! Suna ne da ya kunshi duk abin da Allah Yake so kuma Ya yarda da shi, na daga magana da ayyuka, na fili da na boye. Don haka Sallah da Zakka da Azumi da Hajji da sadaka da tsare amana da kyautata wa iyaye da sadar da zumunta da tarbiyyar ’ya’ya da cika alkawari zuwa karshen duk kyawawan dabi’u, dukkansu suna daga cikin ibada ba wai wani bangarensu kadai ba.
Lallai duk wani aikin da ake karuwa da shi ake yi don amfanin jama’a, Musulunci yana lissafa shi a cikin ibada, matukar mai aikatawar ya yi nufin alheri ba nufin samun yabo a wurin mutane ba. Duk wani aiki da mutum zai yi ya share kwaranye bakin ciki ga wani ko ya saukaka damuwar mai damuwa ko ya taimaki mai neman taimako ko ya biya bashin wanda bashi ya addabe shi, ko ya ilimantar da jahili ko ya sauki bako ko ya kawar da sharri daga wani abin halitta, kai hatta kawar da kaya ko kwalba ko wani abu da zai cutar daga kan hanya, wadannan abubuwa da suka gabata ibada ne da ake kusantar Allah da su, idan niyya ta inganta kuma aka dace da koyarwar Littafin Allah (Alkur’ani Mai girma) da Sunnar zababbenSa (Annabi Muhammad SAW).
Ina jawo hankalinku zuwa ga wani abin da Annabi (SAW) ya ruwaito mana kan daya daga abubuwan da za su faru Ranar kiyama, cikin wani faifan muhawarar da za ta gudana a tsakanin Allah da bayinSa!
“Lallai Allah Mai girman daraja zai ce Ranar kiyama: “Ya dan Adam! Na yi rashin lafiya amma ba ka gaishe Ni ba.” Sai ya ce, “Ya Ubangiji! Yaya zan gaishe Ka, bayan Kai ne Ubangijin talikai?” Sai Ya ce: “Ashe ba ka san bawaNa wane ya yi rashin lafiya ba, amma ba ka je gaishe shi ba? Ba ka san cewa da ka je gaishe shi za ka same Ni a wurinsa ba? Ya dan Adam! Na nemi ka ciyar da Ni, amma ba ka ciyar da Ni ba. Sai ya ce: “Ya Ubangiji! Yaya zan ciyar da Kai, bayan Kai ne Ubangijin talikai?” Sai Ya ce, “Amma ba ka san bawaNa wane ya nemi ka ciyar da shi, amma ba ka ciyar da shi ba? Ba ka san cewa da ka ciyar da shi da ka samu haka a wuriNa ba? Ya dan Adam na roki ka shayar da Ni ruwa ka ki. Sai ya ce: “Ya Ubangiji! Yaya zan shayar da kai ruwa alhali Kai ne Ubangijin talikai? Sai Ya ce: “BawaNa wane ya nemi ka shayar da shi ruwan sha, ka hana shi. Ba ka san cewa da ka ba shi ruwan shan da ka iske haka a wuriNa ba?” Muslim ya ruwaito.
Lallai Musulunci bai sunnata wadannan abubuwa kawai ba, har ma yana kiranka zuwa ga aikata su, yana umartarka ka yi su.
An karbo daga Abu Zarril Gifari (RA) ya ce: “Na tambayi  Manzon Allah (SAW) kan me zai nesanta bawa daga wuta?” Sai ya ce: “Imani da Allah.” Sai na ce: “Ya Annabin Allah! Tare da imani akwai aiki! Sai ya ce: “Ka ciyar daga abin da Allah Ya mallaka maka.” Na ce: “Ya Annabin Allah! Idan ya kasance fakiri ne wanda bai da abin da zai bayar fa?” Sai ya ce: “Ya yi umarni da alheri ya hana abin ki.” Sai na ce: “Idan ba zai iya umarni da alheri ya hana abin ki ba fa? Sai ya ce: “Ya taimaki cima-zaune wajen koya masa sana’a.” Na ce: “Ya Manzon Allah! Kana ganin, idan ba zai iya koya masa ba fa?” Ya ce: “Ya taimaki wanda aka zalunta.” Na ce: “Ya Annabin Allah! In ya kasance mai rauni ne da ba zai iya taimakon wanda aka zalunta ba fa?” Sai ya ce: “Ba ka nufin ka bar wa abokinka wani alheri ne, to, ya kame cutarwarsa daga mutane.” Sai na ce: “Ya Manzon Allah! Kana ganin in ya aikata wannan zai shiga Aljanna?” Sai (SAW) ya ce: “Babu wani mumini da zai nemi daya daga cikin wadannan dabi’u (ya rika aikata ta) face ta kama hannunsa har zuwa gidan Aljanna.” Baihaki ya ruwaito.
Daga wannan Hadisi za mu san cewa lallai Musulunci bai kebe wata kungiya ayyananniya daga cikin mutane da yin ibada ba. A’a ga daukacin jama’a ne. Kuma bai sanya ibadar dukiya kadai ba, balle mawadata su kadaita da ita ba, kuma bai kebe ta ga jiki kadai ba, balle masu karfi su kebanta da ita, bai sanya ta ga kwararrun masana ba, balle malamai su kebanta da ita, a’a kowane mutum yana da ibadar aiwatarwa gwargwadon ikonsa.
Lallai Allah da mala’ikunSa suna salati ga Annabi. Ya ku wadanda suka yi imani! Ku yi salati a gare shi da taslimi. Ya Allah Ka kara tsira da aminci a bisa Shugabanmu Annabi Muhammad da alayen Annabi Muhammad a cikin talikai, Lallai Kai Abin godiya ne Mai girma. Allah Ya yi mana gafara ni da ku.