Tukari sun yi sojan gona a matsayin alhazai tare da mamaye masaukan alhazai a sansanin Mina da ke kasar Saudiyya, lamarin da ya janyo alhazan suka rasa tudun dafawa.
Tun da farko, tukarin sun yi amfani da damar rashin sanin juna tsakanin alhazan, yawansu da kuma zamansu a masaukai daban-daban a Makkah da Madina inda alhaji ba zai iya sanin ko makwabcinsa alhaji ne ko a’a.
Aminiya ta gano cewa sai da jami’an hukumomin alhazai na jihohi suka rika bi shemomi suna fitar da tukari daga ciki tare da maye gurbinsu da alhazan.
A wata shema ta alhazai mata daga Jihar Kano, an fitar da akalla tukari 10 wadanda suke sanye da fararen kaya kamar alhazan, tare da yin magana cikin harshen Hausa.
An gano su ne ta hanyar neman kowacce hajiya ta fito da katin shaidarta, wanda tukarin ba su da ita.
Wakiliyarmu wacce ta zama ganau, ta shaida mana cewa wasu tukarin har sun yi shimfida suna hutawa bayan sun gama karin kumallo da abincin da aka tanada domin alhazan, kafin dubunsu ta cika.
An kama tukari da shaidar wata
Wani abin almara da ya faru a wurin, shi ne yadda wata tukari da ta nuna katin shaidar wata hajiya, wanda ake zaton sato shi ta yi, domin kuwa bayan da aka tsananta bincike an gano hakikanin mai katin shaidar.
A yayin da zafin rana ya kai maki 46 na ma’aunin Celsius a ranar Litinin da aka fara aikin Hajjin na bana, shigar burtun da tukarun suka yi ta sa wasu alhazai sun kare da zama a rana, wasu kuma suka fake a inuwar tantuna da sauran gine-ginen da ke sansanin nasu.
Wasunsu sun yi ta shiga duk tantin da suka samu, lamarin da ya haifar da rudani, kafin daga bisani a yi waje da tukarun.
Malamai masu wayar da kan mahajjata na daga cikin wadanda haka ta shafa da farko, inda kafin su zo wasu sun mamaye tantin da aka kebe musu.
Wani daga cikin alhazan Najeriya maza da Aminiya ta samu sun a rakube a rumfar wani tanti, ya yi zargin akwai “Wasu tukari da suka yi sojan gona a cikin mahajjata.
“Ni ban sani ba, mun hau mota, sai aka ce kowannenmu zai biya Riyal 100, ashe tukaru ne duk a cikin motar, ni ban sani ba.
“Dazu kuma askarawa suka kama wani Tukaru a cikin wani tantin suka tafi da shi.”
Shi ma wani alhajin da ya ki bayyana sunansa ya ce, “Akwai dan uwana da ke zaune a nan Saudiyya, da ya ce zai zo wurina ya zauna a Mina, amma na ce masa ya hakura.”
Aminiya ta yi kicibus da wasu alhazai maza a wani lungu a wajen tantunan ’yan Najeriya, amma ba ta yarda da take-takensu ba.
Ko da muka tambaye su cewa ’yan Najeriya ne, sai suka amsa, amma da muka nemi sanin jihar da suka fito sai suka fara kame-kame.
Wasu alhazai da Aminiya ta tattauna da su sun dora laifin faruwar hakan a kan jami’an hukumomin aikin Hajji musamman na jihohi da yin shakulatin bangaro da batun masaukin.
Wata hajiya da ta nemi a boye sunanta ta bayyana cewa “Wannan laifin jamian alhazai ne. Da ace da shugabanci tun farko ma tukarin ba za su sami damar yin kutse a masaukin alhazan ba, domin tun a kofar shigowa ya kamata a ajiye mai bincike wanda zai tabbatar kowane alhaji ya nuna katin shaidarsa kafin ya shiga.
“Amma ba hakan aka yi ba, dukkaninmu haka muka shigo masaukin nan sasakai ba tare da muna sanye da katin shaidar ba.
“Sai da aka ga uwar bari sannan ne fa aka ce kowa sai ya rataya katin shaidarsaa a wuyansa.”
A cewarta “tukarin nan ma ba a san su ba, za su iya yi wa alhazai sata. Wannan sakaci ne babba.”
Wani jami’in Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) da muka zanta da shi a Mina, ya tabbatar mana cewa an samu tukaru sun shiga cikin mahajjata, suka kame wasu wurare, shi ya sa da farko “aka tsaurara cewa babu alhajin da zai shiga tanti sai wanda ke sanye da sarkar alhazai ta musamman.
Wani jami’in hukumar ya bayyana cewa “Ba alhazan Najeriya kadai ba ne ke da wannan matsalar.”
Ya ce baya ga haka, akwai matsalar karancin masauki ga daukacin mahajjatan dukkan kasashe.
Mutum sama da miliyan 2.5 daga kasashe 160 ne suke halartar aikin Hajjin bana, amma jimillar masaukan da ke Muna na mutum 96,000 ne.
Game da matakan da hukumar take dauka domin magance matsalar, jami’an sun bayyana cewa ana yi wa alhazan da suka samu tanti “magana, ana bude tanti a yi rumfa a tsakanin tantuna ta waje domin wasu su samu sauki,” daga wannan tsananin zafin ranar.
“Ana kuma tunanin fara kwasar mahajjata da ba su samu wuri ba zuwa Arafat, amma ba a yanke shawara ba tukuna.
“Shari’a ma ta san da lalurar, amma dai ba a yanke hukunci ba tukuna, sai idan babu makawa,” in ji jami’in.
Wannan dai shi ne Hajjin farko da alhazai sama da miliyan biyu suka halarta tun bayan bullar annobar COVID-19.
A wannan karo kuma Najeriya ta yi nasarar kwashe daukacin maniyyatanta 95,000 zuwa Kasa Mai Tsarki domin sauke farali.