✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajjin Bana: Alhazan Najeriya sun isa Muna

Alhazan Najeriya kimanin 90,000 sun sauka a Muna ranar Litinin domin  fara  aikin Hajjin bana. Jigilar alhazan ta fara ne tun a ranar Lahadi 7…

Alhazan Najeriya kimanin 90,000 sun sauka a Muna ranar Litinin domin  fara  aikin Hajjin bana.
Jigilar alhazan ta fara ne tun a ranar Lahadi 7 ga watan Zulhijja kamar yadda jami’in gudanar da jigilar na Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) Dr Aliyu Tanko ya shaida wa Aminiya.
Dr Tanko ya ce Hukumar NAHCON ta fara jigilar ahazan  ranar 7 ga watan Zulhajji a maimakon ranar 8 ga watan don a rage cunkoson da ake samu akan titin Makka a yayin jigilar alhazan.

Hajji: Yadda Saudiyya ta tsara jigilar alhazai a minti 15

Ranar Asabar za a kammala jigilar maniyyata Aikin Hajjin bana – NAHCON
“Hukumomin Kasar Saudiyya sun umarci kasashen da ke da yawan alhazan cewa dole ne su fara jigilar alhazansu zuwa filin Muna tun daga ranar 7 ga watan Zulhajji don alhazan su isa filin Muna da wuri haka kuma don su sami isasshen hutu kafin ranar Arafat wacce ake gudanarwa a ranar 9 ga watan Zulhijja.

“Hakan ya sa muka fara jigilar alhazanmu a jiya inda kuma muka karasa a yau”
A bisa abin da aka saba alhazai na fita Muna ne a ranar 8 ga watan Zulhajji wanda kuma shi ne mataki na farko a tsarin gudanar da aikin Hajjin.
Alhazan za su zauna a wannan wuri su gudanar da sallolin Azahar da Laasar da Magariba da Isha har zuwa wayewar gari sannan su wuce filin Arfa.