✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajji: Sarkin Zazzau ya gargadi maniyyata kan zuwa da goro Saudiyya

Sarkin Zazzau ya gargadi maniyyata kan daukar kayan laifi ko na bakin ido domin kada su fada a tarkon dillalan miyagun kwayoyi.

Sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli, ya gargadi maniyyata aikin Hajjin bana da su guji zuwa da goro kasar Saudiyya.

Sarkin Zazzau ya yi gargadin ne a yayin da yake bankwana ga sahun farko na maniyyata daga Jihar Kaduna, kafin tashinsu zwua Kasa Mai Tsarki.

“Ku guji daukar goro zuwa Saudiyya domin dokar kasar ta haramta, don haka za a iya tsare duk wanda aka samu da goro. Duk maniyyacin da aka kama da goro kuma, da wuya gwamna ko sarki su iya kwato shi,” in ji shi.

Ya kuma shawarci maniyyata da su nesanci daukar duk wani kayan laifi, ko taimaka wa bakin ido da daukar kaya a filin jirgi, domin kada su fada a tarkon dillalan miyagun kwayoyi.

Ita kuma a nata jawabin, Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Hadiza Balarabe Sabuwa, ta bukaci maniyyatan da su kasance wakilai na gari ga jihar da ma Najeriya a Kasa Mai Tsarki.