Ayarin farko na maniyyatan Najeriya mai dauke da mutum 546, ya isa kasar Saudiyya bayan da suka tashi daga Babban Filin Jirgin Sama na Maiduguri, Jihar Borno.
Da yake kaddamar da fara jigilar maniyyatan na bana, Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, ya yi kira gare au da su kasance masu da’a, bin doka da oda da kuma zame wa Najeriya jakadu nagari yayin zamansu a Kasa Mai Tsarki.
- Alarammomin Kano sun gudanar da addu’o’i na musamman don samun tsaro da shugaba na gari
- NAJERIYA A YAU: Yadda Tsadar Taki Za Ta Hana Noma Bana
Shugaban ya ce, “Hajji a matsayin ibada, aiki ne mai wahala mai bukatar hakuri, sadaukarwa da kamun kai wajen gabatar da shi.
“Don haka na hore ku da ku kiyaye dukkanin dokokin yaki da COVID-19 da aka gindaya a iya zaman da za ku yi a Kasa Mai Tsarki.”
Da yake jawabin ta bakin mukaddashinsa, Gwamnan Babagana Zulum na Jihar Borno, Buhari ya roki maniyyatan da su roka wa Najeriya dawwamammen zaman lafiya.
“A yau, muna godiya ga Allah Madaukaki da Ya ba mu ikon fara jigilar alhazan Najeriya daga Babban Filin Jirgin Sama na Maiduguri.
“Wannan alama ce da ke nuni da irin kokarin da Gwamnatin Tarayya ta yi wajen tabbatar da maido da zaman lafiya a Jihar Borno.”
Tun farko a jawabinsa, Shugaban Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCON), Alhaji Zikirullahi Kunle Hassan, ya jingina nasarar da aka samu ta fara jigilar alhazai ga Gwamnan Borno.
Ya ce jimillar maniyyata 43,000 ne ake sa ran za su sauke farali daga Najeriya a Hajjin bana.
A hannu guda, Gwamnatin Jihar Gombe ta tsayar da ranakun 20 da 21 ga Yuni a matsayin lokacin da za ta yi jigilar maniyyatan jihar zuwa Kasar Saudiyya.
Sakataren Hukumar Alhazai na jihar, Malam Sa’adu Hassan ne ya bayyana hakan yayin wata tattauna da aka yi da shi game da Hajjin bana a ranar Alhamis.
A cewar Hassan, maniyyatan jihar su 1,105 ne za a gabatar da Hajji bana tare da su, kuma kamfanin Max Air ne zai yi aikin jigilar maniyyatan zuwa Saudiyya.
Ya kara da cewa, Naira miliyan 2 da dubu 450 ne kowane maniyyacin jihar ya biya a matsayin kudin kujera kamar yadda hukumar NAHCON ta bukata.
Sai dai, ya ce za a maida wa kowa Kudin Guzirinsa (BTA), Dala 800.
Hassan ya danganta tsadar kujerar Hajji da aka fuskanta da karin kudin tikitin da kamfanonin jiragen sama suka yi da kuma karin harajin da Gwamnatin Saudiyya ta yi daga kashi 5 zuwa kashi 15 cikin 100.
Daga nan, ya ja hankalin maniyyatan a kan kowa ya tabbatar da ya yi rigakafin COVID-19, wanda a cewarsa rashin hakan zai haifar wa maniyyaci cikas wajen shiga Kasar Saudiyya.
Kafin wannan lokaci, sai da aka shafe shekaru biyu cur ba a samu zarafin gabatar da Hajji ba sakamakon bullar annobar COVID-19.
Daga Haruna Gimba Yaya (Gombe) Da Hassan Ibrahim (Maiduguri) Da Bashir Isah