✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajiyar Kaduna ta samu tukwicin Naira dubu 100 saboda mayar da kuxin tsintuwa a Saudiyya

Wata Hajiyar Kaduna mai suna Amina Abdullahi Gele ta samu tukwicin Naira dubu 100 saboda mayar da kuxin guzurin wata Hajiya Dala 750 a Madina…

Wata Hajiyar Kaduna mai suna Amina Abdullahi Gele ta samu tukwicin Naira dubu 100 saboda mayar da kuxin guzurin wata Hajiya Dala 750 a Madina da ta tsinta a lokacin aikin Hajjin bara.

Alhaji Ibrahim Sambo Magnet da ke Katsina ne ya aiko wa Hajiyar tukwicin ta hannun Hukumar Alhazai ta Jihar Kaduna domin nuna jin daxin kan halin dattaku da tsoron Allah da ta nuna a can qasar Saudiyya.
Da yake miqa cakin kuxin a Sakatariyar Hukumar da ke Kaduna, Babban Jami’in Kula da Hukumar, Imam Hussaini Sulaiman Tsoho ya ce waxanda Allah Ya nufa da imani su ke yin tsintuwa su nemi mai shi domin ba su abinsu musamman a qasa irin ta Saudiyya. Ya ce dama Allah Ya hana yin tsintuwa a cikin Masallacin Madina da Makkah a yayin aikin Hajji kuma duk wanda ya yi bai nemi mai su ya ba shi abinsa ba to zai lalata aikin hajjinsa. “Wannan abu da kika yi kin xaukaka martabar Hukumar Alhazai da Jihar Kaduna. Allah ne kawai zai biya ki domin irinku kaxan ne a cikin al’umma. Sai mai matuqar tsoron Allah ne zai tsinci irin wannan kuxi ya nemi mai su ya ba shi abinsa,” inji shi.
Imam Tsoho ya nemi maniyyatan bana su yi koyi da halin Hajiyar wajen taimakon ’yan uwansu a qasar Saudiya.
A jawabin Hajiya Amina Gele ta nuna farin ciki kan wannan tukwici duk da cewa ba ta sa rai ba. “Gaskiya ban sa ran samun wani tukwici ba, amma ina godiya ga wannan bawan Allah da ya aiko da kuxin da kuma Hukumar Alhazai ta Jihar, Allah Ya saka da alheri,” inji ta.