✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajiya Zainab Musa: Mata a rika taimakon juna

Hajiya Zainab Ali Musa baya ga kasancewarta ma’aikaciyar lafiya wacce ta kwashe tsawon shekaru ashirin da biyu tana gudanar da aiki a asibitocin Jihar Kano…

Hajiya Zainab Ali Musa baya ga kasancewarta ma’aikaciyar lafiya wacce ta kwashe tsawon shekaru ashirin da biyu tana gudanar da aiki a asibitocin Jihar Kano daban-daban a yanzu haka ita ce Shugabar Gamayyar kungiyoyin Mata ta kasa (NCWS), reshen Jihar Kano. A tattaunawarsu da Zinariya ta yi kira ga mata da su hada kai wajen taimakon junansu.

Tarihin rayuwata
Sunana Hajiya Zainab Ali Musa, an haife ni a Jihar Kano. Na yi karatun firamare da na sakandire a Kano. Bayan na kammala sai na tafi Kwalejin Koyon Aikin Jinya ta Jihar Kano, inda na samu shaidar satifiket. Daga baya kuma sai na koma na yi difloma a dai wannan kwalejin. Ina kammalawa sai na samu aiki da Hukumar da ke kula da Asibitoci ta Jihar Kano (Kano state Hospitas Management Board), inda na zauna a asibitoci da dama da ke jihar a matsayin mai kula da lafiyar al’umma. Ina nan ina aiki sai a na sake koma wa makaranta, inda na samu shaidar wata diflomar a bangaren tafiyar da harkokin mulki (Public Admin) a Kwalejin Ilimi ta Tarayya (FCE) da ke Kano. A yanzu haka kuma na sake koma wa karatu inda nake Digiri a fannin kula da lafiyar al’umma a Jami’ar Open Unibersity.

Iyali
Ina da aure, ina kuma lura da ’ya’ya bakwai. Duk da cewa ba ni na haifi dukkansu ba, ina da ‘ya’ya uku; sauran hudun na maigidana ne. amma kasancewar ni na rike su tun suna kanana a koyaushe aka zo batun ’ya’ya nakan bayyana cewa ‘ya’yana bakwai.

Yadda na shiga harkokin kungiya
Na shiga harkar kungiya ne a lokacin ina aiki a gundumar Gaya, inda nake aiki a karamar Hukumar Ajingi. Ina aiki a wurin ne sai aka zo da wani shiri na BAMAKO Initiatibe, sai aka ce ana neman mai matsayin karatun difloma, a nan aka nemi da na rike ofishin ci gaban mata (women debelopment office).  Haka na rika hada aikina da na harkokin mata, wanda ya kai ni ga samun kaina tsundum a cikin harkokin kungiya.

Aikace-aikacen kungiyar NCWS
Wannan kungiya ta NCWS ta dade domin an kafa ta a shekarun 1964 ko 1965, sai dai ta shigo Kano ne a shekarun 1980. Kasancewar  kungiyarmu ita ce  babba, kungiyoyin mata da dama masu zaman kansu a Jihar Kano suna yin rajista da mu. Ta fuskar aikace-aikacenmu mun fi kula da harkokin mata da yara da kuma mutane masu bukata ta musamman.
Mukan yi shirye-shirye daban-daban don fadakarwa a kan wasu lamurra da suka shafi rayuwar yau da gobe, misali harkar shaye-shayen muggan kwayoyi da sauransu. Mukan samu kudin gudanar da wasu ayyukanmu ta hanyar karbar kudin haraji da muke karba duk shekara daga wurin kungiyoyin mata. Haka kuma a wasu lokutan  mukan samu taimako daga kungiyoyin kasashen waje.

Nasarori
Tsawon shekara 21 da na yi ina aiki, mun samu babbar nasara ta zama da mutane lafiya. Duk inda na zauna nakan yi kokari na ga cewa mun yi aiki har mu rabu lafiya. Samun cikakken goyon baya daga maigidana, ya sa na samu nasara ta fuskar gudanar da aikina, domin ko a lokacin da nake haihuwa ga kuma tafiya wurin aiki a daya bangaren, maigidana ya taimaka min kwarai da gaske. Ko a yanzu da muke harkar kungiya a duk lokacin da wani abu ya taso ko na tafiya ne, da zarar na sanar da shi zai amince ba tare da nuna min damuwa ba.
 kalubale
Duk da dai zai yi wuya a ce rayuwa ta tafi ba tare da samun kalubale ba, amma ni dai kam Alhamdulillahi ban samu wani cikas a harkar gudanar da aikina ba. Idan ma wani abu na ji an fadi a kaina nakan dauki maganar a kan yanayin halin rayuwa kawai, dole mutum ya samu masoyi da kuma makiya. A lokuta da dama idan za ka biye ta zancen mutane to fa ba yadda za a yi ka zauna lafiya da wasu mutanen saboda tsegunguma da za a rika kawo maka. Ni abin da nake yi shi ne, idan ka gaya mini magana cewa wane ya ce kaza, to yadda ka fade ta haka nakan bar ta a wurin, ba zan je in kure shi ko kuma na dauki mataki a kan sa ba.
Buri
Babban burina bai wuce a ce mun gama da aiki da kuma harkar kungiya lafiya ba. Tare da fatan shugabar da za ta zo nan gaba za ta dora a kan inda na tsaya, za kuma ta tafi tare da matan kungiyar a duk lamurran da za ta gudanar. Ina da burin ganin mata sun hada kai wajen taimakon junansu.
Abinci
Na fi son abincinmu na gargajiya, musamman tuwo da kowace irin miya.
Kwalliya
Ni mutum ce mai son kwalliya, ba na son na ga mace na yawo babu kwalliya. A kullum nakan gaya wa mata cewa su kasance cikin tsafta da kwalliya, ko zane daya gare ta, ya kamata ta rika tsaftace shi tana fitowa fes da ita.
Mutane abin koyi
Mutanen da suke burge ni har nake sha’awar yin koyi da su suna da yawa, amma idan aka ce in zabi daya, to, zan ce tsohuwar Shugabar wannan kungiya tamu wato Hajiya Zainab Ahmed. Na koyi abubuwa da dama daga wurinta sosai. Ina yaba mata sakamakon abubuwan da ta yi.
Shawara ga mata
Ina shawartar mata ‘yan uwana da mu daina kyashin juna. Idan wata ta samu wani matsayi, sai wata ta koma gefe ta rika zundenta don me za ta samu wannan mukami da sauransu. Kamata ya yi mata mu hada kai wajen taimakon junanmu. Idan wata sana’a kika iya kada ki ji kyashin koya wa  wata ‘yar uwarki. Wannan shi zai haifar da hadin kai a tsakaninmu.
Ta bangaren zamantakewa ina shawartar mata da su kasance masu hakuri, duk abin da hakuri bai bayar ba, to rashinsa ba zai bayar ba. Haka kuma mata su rika sanya batun kula da iyalinsu a gaba, a kowane hali muka kasance mu san cewa nauyin kula da iyalinmu yana kanmu. Kada mu bari wasu ayyuka su sha mana gaba mu ajiye batun iyalinmu a gefe.