✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajiya Umma: Macen da ta kashe Naira miliyan 12 wajen kafa kungiyar kwallon kafa

Umma Hassan Muhammad, wadda aka fi sani da Hajiya Umma, fitacciyar ’yar kasuwa ce a Jihar Filato, inda a bara ta kafa kungiyar kwallon kafa…

Umma Hassan Muhammad, wadda aka fi sani da Hajiya Umma, fitacciyar ’yar kasuwa ce a Jihar Filato, inda a bara ta kafa kungiyar kwallon kafa mai suna Umma Hassan Football Academy, Aminiya ta tattauna da ita kan abin da ya ja hankalinta ta kafa kungiyar kwallon kafa, matsalolin da take fuskanta da kuma nasarorin da ta cimma. Hajiya Umma ta kuma yi karin bayani kan yadda ta kashe Naira miliyan 12 wajen kafawa da kuma gudanar da kungiyar kwallon kafarta. Ga yadda hirar ta kasance:

 

Aminiya: Mene ne takaitaccen tarihinki?

Hajiya Umma: Assalamu alaikum, sunana Umma Hassan Muhammad, amma an fi sanina da Hajiya Umma, an haife ni a Jos a Layin ’Yan Tifa, ina da ’ya’ya hudu; maza biyu, mata biyu, dana na farko ya kammala karatu a kasar Uganda, yanzu haka ya kammala digiri na biyu a Kimiyyar Kwamfuta, sai daya dana yana aji uku a karamar sakandare a Jos, sai wacce take aji daya na karamar sakandare, sai ’yar autata tana ajin share-fage na uku. A bangaren karatun boko kuwa, iyakacina sakandare, kuma ban ci gaba ba saboda mahaifina bai yarda ba, wato ya yi mana aure, amma na so in zama likita ce.

 

Aminiya: Me ya ja hankalinki ki fara harkar wasanni?

Hajiya Umma: Da ma can ina da sha’awar harkar wasanni, domin tun ina sakandare ma ina wasanni, inda nake wasan Badminton, inda a 1994 na zamo gwarzuwar ’yar wasa a yayin gasar makarantun sakandare na ’yan mata a Najeriya, inda har aka ba ni satifiket na zuwa waje don mu wakilci Najeriya, amma ba a bar ni a gida ba, iyayena ba su bar ni ba, a lokacin na wakilici Sakandaren ’Yan Mata da ke Jogana a Jihar Kano ke nan.

 

Aminiya: Me ya sa kika zabi harkar kwallon kafa?

Hajiya Umma: Na zabi kwallon kafa saboda matasa a Najeriya sun fi son kwallon kafa ne, kuma yawancinsu kwallon kafa tana debe musu kewa, domin tana hana su shaye-shaye. Yanzu haka ina da kungiyar kwallon kafa da ake kira Umma Hassan Football Academy, an kafa ta kimanin shekara daya da wata hudu ke nan a Jihar Filato.

Kuma ’yan wasa da suke kungiyar sun kama daga shekara 17 zuwa sama ne. A kwanakin baya ma kungiyata ta buga wasan karshe da kulob din Plateau United duk da cewa sun lallasa mu da ci uku da nema.

 

Aminiya: Zuwa yanzu kina da kimanin ’yan wasa nawa a kungiyar taki?

Hajiya Umma: A yanzu jimillar ’yan wasana da suka hada da ’yan kasa da shekara 17 da 19 da kuma 20 sun kai 95. Ina daukar nauyinsu, akwai wadanda na mayar da su makaranta, saboda kwallo ba za ta yiwu babu karatu ba, ko da yaro ya iya idan ba ya da ilimi to akwai wurin da ba zai je ba, ko a filin jirgin sama akwai takardun da ake ba su, idan babu ilimi sai ka ga sun samu matsala, su kansu kulob-kulob din da suke daukar ’yan wasan sun fi son wadanda suka yi karatu. Akwai ’yan wasan da idan sun zo sai an ba su kudin motar komawa gida.

 

Aminiya: Ko kina biyansu albashi?

Hajiya Umma: Ba na biyansu amma dai ina taimaka musu sosai.

 

Aminiya:  Zuwa yanzu wace nasara kika cimma dalilin kafa kungiyar kwallon kafar?

Hajiya Umma: Nasara daya ita ce, a duk fadin Jihar Filato babu Academy kamar tawa, inda a yanzu haka na sayi fili.

 

Aminiya: A kwanakin baya an yada cewa wadansu daga cikin yaranki za su fita kasashen waje, ina zancen ya kwana?

Hajiya Umma: kwarai akwai yarana biyu da suka je kasar kuburus (Cyprus), amma sai aka samu akasi a lokacin an rufe daukar ’yan wasa, sun yi latti, sai suka dawo, kulob daya a can sun ce suna son yarona daya a cikinsu, yanzu haka ana batun sake komawarsa, kuma yanzu zancen da nake yi  akwai yara kusan 18 wadanda suke Legas, akwai wadanda suke Abuja daga yanzu zuwa kowane lokaci za su iya tafiya, akwai wadanda za su tafi kuburus da Tanzaniya da Afirka ta Kudu da kuma Ukraine.

 Kuma na mayar da hankalina ga yaran Jihar Filato ne. Amma kwallon kafa tana da wani abu,  za ka ga wani yaro daga wani gari idan ya ji labari  sai ka ga ya kawo kansa, duk yaron da ya kawo kansa muna karbarsa, amma a gaskiya mun yi saboda yaran Jihar Filato ne.

 

Aminiya: Daga cikin yaranki ko akwai wadanda suke buga wa kulob-kulob na Najeriya?

Hajiya Umma: Yanzu haka akwai yara uku, akwai daya a Ifeanyi Ubah da ke Nnewi a Anambra, akwai daya a Wikki Tourist da ke Bauchi, akwai daya a Niger Tornadoes da ke Minna.

 

Aminiya: Yanzu wani shiri kike yi don fadada kungiyar taki?

Hajiya Umma: Ka san na sayi fili, to a wannan filin za a samar da filin kwallo da dakin kwanan ’yan wasa da wurin ninkaya da na motsa jiki (gym). Nan da wata biyu za mu fara amfani da filin, inda daga nan sauran gine-gine za su biyo baya.

 

Aminiya: Harkar kwallon kafa na bukatar kudi, ta ina kike samun kudin gudanar da kungiyar taki?

Hajiya Umma: Na fara safarar kaya daga Dubai zuwa Najeriya tun a shekarar 2007, ina sayo shaddoji da atamfofi da leshi da takalma da jakankuna da kuma hijabai da  abaya da sauran kayan mata, inda a yanzu nake harkar sufuri, sannan har yanzu ina ci gaba da sayar da kayan mata, ina samun kudina ta wadannan harkoki, sannan ni ejan ce da ke samar wa ’yan Najeriya ayyuka a kasar Saudiyya.

 

Aminiya: Mun ji kin ambaci kina harkar sufuri, wace irin sufuri?

Hajiya Umma: Ina harkar sufuri, inda a yanzu haka ina da Keke NAPEP sama da 200 a hannun matasa, za ka ga mutum yana da digiri amma ya rasa aikin yi, to ina hada wa matasa wadannan kekuna na NAPEP, sannan a sa masa kudin da zai biya, daga karshe ya zama nasa.

 

Aminiya: Yaushe kika fara harkar sufuri?

Hajiya Umma: Na fara harkar sufuri fiye da shekara tara, inda na fara da babura, wato da Jincheng, aka dawo Boder, bayan gwamnati ta hana amfani da babur sai na koma Keke NAPEP, kuma tun a wancan lokacin duk Jihar Filato babu mai yawan baburana, ko a lokacin ina da babura fiye da 125.

 

Aminiya: Bayan an hana aiki da babura yaya kika yi?

Hajiya Umma: Na yi amfani da ’yan sanda wajen karbar baburan, a karshe na kai su jihohin da aka yarda a rika amfani da su. A yanzu ina da Keke NAPEP 200 a kasa.

 

Aminiya:  Zuwa yanzu wane kalubale kike fuskanta a harkar kwallon kafa?

Hajiya Umma: Babbar matsalar da nake fuskanta a harkar kwallon kafa ita ce ta wurin ejan-ejan da suke fitar da yarana zuwa kasashen waje, domin a yanzu haka akwai kudadena da suke hannun ejan, sun karba za su fita da yaran amma wadansu wayata ma ba sa dauka, a yanzu muna kokarin ganin an shawo kan batun.

 

Aminiya: Ko wannan ya sa gwiwarki ta yi sanyi?

Hajiya Umma: Ina kuwa, ka san komai mutum ya fara sai ya samu kalubale, amma a yanzu ina kara wayo a kan harkar, kuma nan gaba komai zai tafi daidai.

 

Aminiya: Daga fara harkar kwallon kafa kina ga kin kashe kamar nawa?

Hajiya Umma: Na kashe ya fi Naira miliyan 12, kama daga sayen fili da sayen kayan ’yan wasa da batun fitar da yarana zuwa kasashen waje da kuma ihsanin da nake yi wa ’yan wasa da koci-kocina.

 

Aminiya; Ana jita-jitar wai kudin jini kike amfani da su, me za ki ce a kan hakan?

Hajiya Umma: Ana maganganu iri-iri a kan kudin da nake kashewa, amma dan uwana ma lokacin da ake yakin Jos ba a gan shi ba, da shi da babur dinsa, na san fiye da mutum 100 da hakan ya faru da su, amma da yake ni akwai zargin cewa kudina na tsafi ne, kasancewar tsakanin mutuwarsa da na mahaifina kwana 26 ne, sai ake ta yamididin wai ni na ba da su a sha jininsu. Sun manta mahaifina ya yi shekara 10 yana jinya. Babu kuma inda ba mu kai shi don ya samu lafiya ba, amma Allah bai yarda ba.  Hakan ya daga mini hankali, har ya kai ga na janye jikina da shiga cikin mutane. Amma daga baya sai na ce tun da abin nan don Allah nake yi sai maganar mutane ta daina damuna.

 

Aminiya: Ga shi kina da aure, shin ba ki fuskanci turjiya daga wurin mijinki kan batun kafa kungiyar kwallon kafa ba?

Hajiya Umma: Ko kadan, domin shi ma ya yi harkar kwallon kafa sosai, ya ba ni dukan gudunmawar da nake bukata.