✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajiya Umma Aminu Sanusi: Burina in ga rayuwar mata ta inganta

Hajiya Umma Aminu Sanusi ita ce Iyar garin Kano, wato sabuwar sarautar da Sarkin Kano Muhamamdu Sanusi ya kirkiro ya kuma nada yayarsa  a dai-dai…

Hajiya Umma Aminu Sanusi ita ce Iyar garin Kano, wato sabuwar sarautar da Sarkin Kano Muhamamdu Sanusi ya kirkiro ya kuma nada yayarsa  a dai-dai lokacin da aka yi bikin rantsar da shi a  matsayin Sarkin  Kano.Ta shafe shekaru 35 tana aiki a matakin gwamnatin jihar Kano da kuma ta tarayya.

Tarihin rayuwata
Sunana Hajiya Umma Aminu Sunusi. Mahaifina shi ne marigayi Ciroman Kano Ambasada Alhaji Aminu Sanusi. An haife ni a shekarar 1957. Kamar yadda al’adar mutanen da take musamman kuma gidan sarauta dan fari ba ya girma a gaban iyayensa sai dai kakanni, don haka ni ma na taso a hannun kakana Sarkin Kano Sanusi. A wurinsa na zauna har zuwa lokacin da ya yi murabus ya koma Azare. Kasancewar muna makaranta a wancan lokacin sai aka bar mu a nan Kano. Na yi karatun firamarena a makarantar Cikin Gida ta kofar Kudu. Daga nan sai na koma makarantar ’yan mata ta Shekara bayan na kammala sai na shiga sakandiren‘ GGC ’Dala. Daga nan sai na tafi Kwalejin Share Fagen shiga Jami’a ta Zariya. Daga nan
sai na sami shiga Jami’ar Bayero inda na karanci fannin Harkokin Mulki. Bayan na kammala sai na yi bautar kasa a Ma’aikatar Walwalar Jama’a. Daga nan kuma sai na fara aiki a ma’aikatar daukar Ma’aikata ta Kano. Muna nan sai aka ba wa maigidana Kwamishina a jihar Neja da yake dan can ne. Da muka koma Neja sai na ci gaba da aikina a can. To Bayan an yi juyin mulki lokacin Janar Buhari sai muka dawo Kano sai maigidana ya ci gaba da aikinsa na koyarwa a Jami’ar Bayero da ke Kano, ni kuma na koma da aiki a jihar Kano. Ina nan ina aiki har na kai matsayin babbar Sakatare a Ma’aikatar Mata. Ina nan sai aka kira ni na je kwas a makarantar Koyon Harkokin Mulki (NIPPS) da ke Kuru a Jos.Bayan na dawo na ci gaba da aikina inda na zauna a ma’aikatu daban-daban. Ina nan ina aiki sai na nemi canjin aiki zuwa matakin gwamnatin tarayya. A can ma Abuja na zauna a ma’aikatu daban-daban har dai zuwa lokacin da na yi ritaya a watan Disambar bara.
Iyalina
Maigidana shi ne marigayi Farfesa Musa Abdullahi wanda ya rike mukamin
Mataimakin Shugaban Jami’a. ‘Ya’yanmu bakwai tare.
Nasarori da kalubale
A rayuwa dole ne wata rana mutum ya sha zuma wata rana kuma ya sha madaci. Amma idan mutum ya yi imani da Allah ya san komai mai zuwa ne ya wuce. Batun nasara kuwa Alhamdulillahi domin ina yi wa Allah godiya bisa abubuwan da ya yi min. Ba na mancewa a lokacin da muka dawo Kano daga Neja a lokacin mulkin Gwaman Kano Hamza Abdullahi ba a daukar mace a matsayin Jami’a mai kula da Harkokin Mulki amma bayan ya duba takarduna da aiyukan da na yi sai Gwamnan ya amince aka dauke ni. Na gode wa Allah da ya sa na yi aiki ba tare da ba wa Gwamna kunya ba. Ga shi yanzu ta sanadina an ci gaba da daukar mata a wannan aiki. Haka kuma ina daga cikin mata na farko da suka samu mukamin Babban Sakatare. Har ila yau ni ce mace ta farko daga jihar Kano da ta fara zuwa karatu makarantar ‘NIPPS’ da ke Kuru. Sannan uwa uba kuma ga sarautar da aka yi min ta Iyar Gari. Alhamdulillahi babu abin da zan ce sai godiya.
Sarautar Iyar Gari
Wannan sarauta sabuwar sarauta ce mai martaba Sarkin Kano Muhamamdu Sanusi II wanda kanina ne ya ba ni ita. Duk da cewa a tsarin sarautar sullubawa da wuya ka samu an nada mace sarauta, sai dai cewa a ko da yaushe zamani yana zuwa da canji. Wannan ba shi ne karo na farko da aka ba mace sarauta a wannan masarauta ba, domin ko marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya yi wa babbar ‘yarsa sarautar Magajiyar ‘Yar Sarki. Haka kuma wannan Sarkin a lokacin yana dan Maje ya yi wa uwargidansa sarautar Giwar dan Maje.
Ana nan ana shirye-shiryen bude mana ofis inda za mu rika gudanar da harkokin wannan sarauta. Kasancewar sarki mai son ci gaban talaka ne, musamman ta fuskar ilimi da tattalin arziki, don haka za mu taimaka masa wajen cikar wannan buri nasa. A aikace-aikacen da za mu yi za mu rika taimaka wa mata wajen ilimantar da su tare da sama musu sana’o’i. Haka kum a duk lokacin da wani abu ya bullo za mu yi kokarin wayar wa matanmu kai, misali game da wata annoba da sauransu. Duk da cewar gwamnati tana iya nata kokarin a kai, mu ma a bangaren
masarauta muna ganin ya dace mu ba da tamu gudummowar wajen ci gaban al’umma. Za mu yi wannnan aiyuka ne tare da hadin kan kungiyoyi. Ba wai kawai mata za mu koya wa sana’o’i ba har da matasa wadanda suke da sha’awar yin sana’o’i amma ba su da hali, za mu koya musu sana’ar da suke so tare da ba su wani tallafi don dogaro da kai. Za mu nemi tallafi daga jama’ a wadanda ko yaushe a shirye suke su sa dukiyarsu a abubuwan alheri irin wannan. Za mu neme su su zo su taimaka mana wajen gudanar da wannan aiki.
Haka kuma za mu rika kula da gyaran aure, idan an sami matsala a tsakanin ma’aurata za mu yi iya namu kokarin wajen ganin an sulhunta tsakaninsu. Muna so mu ceto rayuwar irin ‘ya’yan da iyayensu suka rabu da juna wadanda kan fada wani hali sakamakon hakan.
Za mu bude bangaren lafiya , ta yadda za mu taimaka wa jama’a da magunguna ko daukar nauyin yi musu aiki don rabuwa da wani ciwo. Haka kuma a bangaren ilimi idan har mun samu yadda muke so ba wai kawai daukar nauyin dalibai a gida Najeriya ba har da kasashen waje. A wasu lokutan za ki ga an yi baki mata a masarauta wadanda a al’adance kamata ya yi ‘yan uwansu mata su karbe su tun daga lokacin saukarsu har zuwa gabatar da su ga Sarki, to ofishinmu ma zai kula da wannan bangare.

Burina
Barina a rayuwa shi ne na ga jama’ar kasar nan musaman ma na Kano sun fita daga cikin halin kuncin rayuwa. Na sani mutum ba zai iya yi wa jama’a maganin dukkanin matsalolinsu ba, amma akwai bukatar a taimaka ta yadda abubuwa za su inganta. Ina so ta hanyar wannan sarauta da aka yi min na ga na bayar da tawa gudumowar a wannan banagre wajen tallafa wa talaka da gajiyayyu da wadanda rayuwarsu take cikin wani hali insha Allah. An gano cewa yawancin mutanen da ke aiwatar da muggan halaye a cikin al’umma rashin aikin yi ne ko zaman banza shi ke kai su ga hakan. Shi ya sa muka ce za mu yi aiki wajen ganin al’ummarmu sun sami sana’a yadda za su mayar da taro sisi. Ina rokon Allah idan har mun fara wannan aiki ya ci gaba har bayan ranmu. Jama’a su amfana kamar yadda hakan shi ne burin mai martaba Sarki wanda ni kuma zan yi aiki a matsayin mai taimaka masa a wannan bangare.
Shawara ga mata
Ina kiran mata da su yi hakuri da zaman aure a yi wa mazaje biyayya.Sannan a kula da tarbiyyar yara, mu sani amana ce Allah ya damka mana. A sa ido a karatun yara. Abu na gaba mace ta nemi sana’a yadda za ta dogara da kanta, domin a duk lokacin da mace ta nemi nata aka hada da na maigida rayuwar ta fi samun inganci da tsari sannan an fi samun zaman lafiya a tsakanin ma’auratan. Don sana’ar da mace ke yi za ta taimaka wa maigida wajen karatun yara da suturarsu kai wani
lokacin ma har da abincin da iyalinta za su ci. Zan yi amfani da wannan dama na yi kira ga mazajen da ke hana matansu yin sana’a da su daure su bar su, domin zamani ne ya zo da hakan. Mace tana bukatar abubuwa na kanta da ‘yan uwanta, ba zai yiwu kullum ta dora wa mijinta lalurorinta ba bayan shi ma yana da nasa hidimomin.