Kimanin kwanaki biyu ke nan ana jita-jitar cewa sojoji a sun yi nasarar hamɓarar da gwamnatin Shugaba Kasar Kwadebuwa, Alassane Ouattara.
Jita-jitar ta fara yaɗuwa ne tun bayan jin ƙarar harbe-harbe a yankunan ƙasar da dama musamman a babban birnin ƙasar na Abijan.
- Ba mu tilasta wa kowa ya koma APC ba — Tinubu
- Jami’an tsaron Zulum sun buɗe wa Boko Haram wuta a Maiduguri
Wasu rahotanni na nuna cewa an samu ɓarkewar rikici ne a cikin birnin na Abijan, lamarin da ake hasashen ya yi sanadiyar masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Ouattara kimanin mutum 33 cikin kwana biyu.
Sai dai har ya zuwa yanzu babu wani tabbataccen rahoton daga majiya mai ƙarfi da ke bayyana hakikanin abin da ke faruwa sakamakon ɗaukewar intanet da kuma tsayawar ayyukan gwamnati.
Har ya zuwa yanzu ba a tabbacin halin da shugaban ƙasar ke ciki, inda wasu ke zargin ya yi ɓatan dabo, wasu na ganin an kama shi inda wasu kuma na hasashen cewa ya mutu, amma dai har yanzu babu tabbas duka akai.
Har wa yau bincike ya nuna cewa wasu bidiyo da ake yadawa ake kuma danganta su da lamarin, ba na gaskiya ba ne wasu kuma ba ma daga ƙasar suka fito ba.
Ba wannan ne karo na farko da aka taɓa samun jita-jitar juyin mulki a ƙasar ba, a shekaru da dama a baya an sha samun irin wannan jita-jitar, tun bayan da wasu daga cikin ’yan ƙasar ke ganin cewa shugaban ƙasar ya zamo ɗan amshin shatan Faransa.