✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajiya Sa’adatu Mustapha Sa’ad: Yadda nake siyasa da kuma sarauta

Hajiya Sa’adatu Mustapha Sa’ad ita ce Alkyabbar Kaltungo da ke Jihar Gombe, ta rike mukamin shugabar matan jam’iyyar PDP a Jihar Gombe kafin ta zama…

Hajiya Sa’adatu Mustapha Sa’ad ita ce Alkyabbar Kaltungo da ke Jihar Gombe, ta rike mukamin shugabar matan jam’iyyar PDP a Jihar Gombe kafin ta zama Kwamishinar Mata a jihar, ta yi bayanin yadda take siyasa da kuma sarauta.

Assalamu alaikum, sunana Hajiya Sa’adatu Mustapha Sa’ad, an haife ni a Zariya, amma na girma a Gombe, na yi makarantar firamare a Central Primary School da ke Gombe, daga nan na yi Kwalejin ’Yan mata ta Gwamnatin Tarayya da ke Lantang a Jihar Filato. Bayan na kammala sai na karanta kwas din zama lauya a Jami’ar Maiduguri a Jihar Barno.
Na yi makarantar lauyoyi da ke Legas, sannan na yi hidimar kasa a Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Barno. Bayan na kammala hidimar kasa sai na fara aiki a cibiyar lauyoyi a Maiduguri, daga baya na koma Legas inda na yi rike wata cibiyar lauyoyi mai zaman kanta. Daga baya na shiga siyasa, inda na rike mukamin Shugabar Matan Jam’iyyar PDP ta Jihar Gombe tsawon shekara biyu, daga nan aka nada ni Kwamishinar Mata da Jin dadin Matasa ta Jihar Gombe. A lokacin da nake Legas an nada ni sarautar Yeye Otun Areogunfilorun ta Idimu, sannan an nada ni Alkyabbar Kaltungo da kuma Zinariyar Dogon Ruwa duka a Jihar Gombe.
Abubuwan da ba zan manta da su ina karama ba
Nakan tuna lokacin da nake karama, musamman lokacin da nake makarantar firamare, idan an kada kararrawar fita tara, mukan fita daga aji da gudu mu je mu shiga layin danwake da alalen da da ake yi a cikin gwangwani madara. Wani lokaci za mu hada danwake da alale, wani lokaci ma har da shinkafa, nakan tuna yadda muke hada su mu ci ba tare da wani abu ya faru da mu, yanzu nakan tuna idan na hada wadannan nau’ikan abincin yaya cikina zai kasance.
Nakan tuna yadda nake taya mahaifiyata aikin kicin, hakan ya taimaka mini wajen iya dafa abinci mai dadi da gamsarwa tun ina karama.
Halayen da na koya a wurin mahaifina
Na fi koyi da halayen mahaifina, mutum ne mai tausayi, sannan zai iya ba mutum abin da yake da shi, shi kuma ya hakura, wani lokaci nakan yi mamakin da zai ba mutane kudi, shi kuma ya zauna ba shi da shi. Bai yarda ya rika ajiye abu don gobe ba, komai ya samu yana raba wa jama’a, domin ya san wani ma zai zo. To haka nima nake.
Yadda nake tunawa da mahaifina
Na shaku da mahaifina sosai, haka zan zo in rika yi masa surutu amma bai taba gajiya ba, mutum ne da komai za ka fada masa zai saurare ka, ban taba ganin yana fushi ba, na fi so in zauna kusa da shi a kan mahaifiyata. Nakan yi masa addu’a idan na tuna da shi, hakan ya sanya duk ilimin da na samu daga wurinsa nake kokarin bayar da shi ga ’ya’yana guda biyu. A lokacin da zan yi jarrabawar fita daga firamare ni kadai ce na samu damar shiga Kwalajen ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya daga firamaren da na yi, ko da aka zo intabiyu ma na yi kokari sosai, a nan aka kai ni makaranta a Lantang, a lokacin da mahaifana suka kai ni makarantar, mahaifiyata sai ta fara kuka, musamman ma da ta lura da rashin kyawun hanya, a nan ta fada masa ya a canza mini wata makaranta, hakan bai yiwuwa ba, yakan kawo mini ziyara sau uku a kowane zangon karatu. Akwai lokacin da zan koma makaranta sai na manta ban sa yi tumatir ba, kodayake a lokacin ana karancinsa a Gombe da Bauchi, hakan ya sanya sai da muka kwana a Jos don mu sayi tumatir, duk lokacin da nake cikin kadaici sai in fara tuna irin wadannan abubuwan da mahaifina ya yi mini. Allah Ya ji kansa.
Farin cikin zama uwa
Alhamdullillah, kowace mace burinta bai wuce ta haihu ba, nakan tuna irin laulayin da na shiga a lokacin da nake da ciki, watarana sai na ji jikina wani iri, ban taba tunanin haihuwa ce ta zo mini ba, rashin lafiyar ta sanya na kira abokiyata ta raka ni asibiti saboda ina jin jikina wani iri. Na ga likita, na fada masa abin da yake damuna, sai ya ce ai ina gab da haihuwa, ban yarda ba, muka rika gardama, kafin ka ce me sai na ji cikina ya fara motsawa, Allah Ya taimake ni na haihu lafiya. ’Yata ta farko mace ce. Bayan na haihu sai na rika kallonta, na kasa shayar da ita nono har sai da Nas din da ke lura da mu ta zo, ita taimaka mini da dabarun yadda zan shayar da ita.
Haka lokacin da aka zo batun wanka da ruwan zafi, haka na rika kiciniya da tsohuwar da take koya mini wankan, na kwalla ihu lokacin da ta yaba mini ganye mai ruwan zafi, daga nan na karbi ganyen da take mini wanka da shi, na sanya shi a cikin ruwan zafi, ni ma na yaba mata, hakan ya sanya washegari ta ki yi mini wankan. Haka muka rika dirama, amma yanzu komai ya zama tarihi. Ba Tarbiyyantar da ’ya’ya har su girma ba abu ne mai sauki ba, ba kai ba barci, kullum hankalinka na wajensu. Ina gode wa Allah SWT yanzu duk sun girma.
Yadda na taimaka wa mata
Gwamna dankwambo ya taimaka wa mata, ya samar dakunan shan magani ga mata, sannan matar gwamna ta kirkiro shirin taimaka wa mata, shiri ne na yadda za a koya wa mata sana’o’i, sannan bayan an yaye su a ba su kayan aiki da kuma Naira dubu 50 don su dogara da kansu, ni ce na jagoranci wannan shirin, kuma mata da yawa sun amfana.
Gwagwarmayar siyasa
Gwagwarmayar siyasa babu sauki, na fahimci siyasa makaranta ce, na hadu da mutane daban-daban, nagari da kuma baragurbi, haka na yi aiki da su, inda hakan ya ba ni damar kara sanin halayen jama’a, lokacin da na zama shugabar matar jam’iyyar PDP na fuskanci kalubale, musamman irin kallon da ake yi wa duk macen da ta shiga siyasa, na yi hakan ne don nuna wa masu irin wannan tunani cewa ba haka ba ne.
Yadda nake hada siyasa da lura da iyali
Ba abu ne mai sauki hada siyasa da kuma lura da iyali ba, hakan ya sanya lokaci yake da matukar muhimmanci a wurina, duk da haka ban taba yarda lokacin wani ya danne ya na wani ba. ’Ya’yana suna makaranta amma duk da haka ina lura da duk motsinsu, duk da rashin lokaci amma wani lokaci cikin dare ma nakan kai musu ziyara.

kalubale bayan an nada ni Alkyabbar Kaltungo
Akwai kalubale sosai bayan an nada ka sarauta, domin wani nauyi aka dora maka, sannan idanun jama’arka na kanka domin su ga abin da za ka yi, don haka ina bakin kokarina wajen ganin na yi wa jama’ata abubuwan da za su ji dadi. A yanzu ina da shirin taimaka wa mata da kananan yara, musamman ma yara da suke da nakasa, don su ji cewa har yanzu suna da daraja a cikin sauran al’umma.
Yadda na hadu da mijina
Na hadu da mijina a lokacin ina jami’a, a lokacin da ya yi mini magana ban shirya ba, saboda babu burin da nake da shi kamar in kammala digirina, na ce masa ba zan yi aure ba yanzu ba, ya yi hakuri, amma ya ci gaba da matsa mini, cikin ikon Allah ya zama mijina.
Babbar kyauta daga gare shi
Babbar kyautar da ya ba ni bayan nuna soyayyar gare ni ita ce, kyautar zoben gwal, har yanzu ina farin ciki da wannan kyautar.
Mutanen da nake koyi da su
Ina koyi da Laila Dogonyaro, ina girmama ta da kuma sha’awar yadda ta gudanar da harkokinta na yau da kullum, tana damuwa da duk wani abu da ya shafi mata, ina so in zama kamarta, ina so in kare hakkin mata.
Yadda nake hutawa
Lokaci zuwa lokaci nakan fita da iyalina, na fi yin hakan lokacin da ’ya’yana suka zo hutu Najeriya, mukan fita shakatawa, mu ci abinci tare, mu yi hira tare.
Ado da Kwalliya
Ina son sanya tufafin da zai kare mini mutunci, ina son yin adon bai daya, wato komai ya kasance da launi daya, wato tun daga kan jaka da agogo da takalmi har zuwa dankwali. Ina son ado da atamfa, idan na sanya ta nakan ji hankalina ya kwanta, sannan ba ta takura mini, musamman idan aka duba yanayinmu. Ina kuma amfani da mayukan gargajiya kamar Man Kade da Man Kwakwa, sannan ina amfanin da Halawa wadda mutanen Jihar Barno suke amfani da ita wajen gyaran jiki.
Wuraren da nake zuwa hutu
Ina son zuwa wuraren da ke da zama lafiya, kamar yankin Niagara da ke kasar Kanada da kuma wuraren da yanayinsu yake da kyawu da kuma dadi, misali kamar Dajin Yankari da ke Jihar Bauchi da Burtalin Obudu da ke Kalaba a Jihar Kuros Riba. Idan na je Legas kuma nakan ziyarci koramar Badagry, duka wadannan wurare suna kwantar da hankali da sa nishadi.
Abin da nake so a tuna ni da shi
Ina so a tuna ni a matsayin wacce take sanya jama’a farin ciki.