Hajiya Maryam Buba da aka fi sani da (mama), ’yar siyasa ce kuma tsohuwar kwamishina a ma’aikatar tsara birane a Jihar Nasarawa, a yanzu ta fito takarar majalisar dokoki a jam’iyyar APC daga mazabar Nasarawa ta Arewa. Ta tattauna wadansu batutuwa da suka shafi rayuwarta, inda ta shawarci mata su rika fitowa takarar siyasa don su kwato ’yancinsu. Ga yadda hirar ta kasance:
Tarihin Rayuwata
Sunana Maryam Buba. An haife ni a kauyen Kafin-Wambai da ke yankin Rayawa a Lafiya ta Tsakiya, a nan Jihar Nasarawa a ranar 2 ga Nuwamba, shekarar 1954. Na yi makarantar firamare dina a kauyen Wunge. Na yi sakandare kuma a garin Bauci. Daga nan na yi makarantar koyon aikin jinya (nurse) a garin Jos da ke Jihar Filato. Bayan nan na je Jami’ar Ibadan inda na yi Difloma ta farko a fannin kiwon lafiya. Daga nan na fara aiki a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH) a matsayin mai koyar da aikin ungwanzoma. Da aka kirkiro Jihar Nasarawa a shekarar 1996 sai na je kasar Gambiya, inda na koyar a wata makarantar kiwon lafiya a kasar.
Na dawo gida Jihar Nasarawa a shekarar 2002, sai na fara aiki a ma’aikatar lafiya a matsayin Darakatar Likitoci, inda a shekarar 2005 na je kasar Thailand na ci gaba da karatu. Daga nan na shiga harkar siyasa bayan na dawo Najeriya, inda tsohon gwamnan jihar nan wanda yanzu sanata ne wato Sanata Abdullahi Adamu ya nada ni kwamishina a ma’aikatar tsara birane. Daga baya na sake koma wa ma’aikatar kiwon lafiya na ci gaba da aikina. Ina kuma aiki da kungiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu. Kuma a yanzu haka ina shirye-shiryen fitowa takarar kujerar majalisar dokokin jihar a mazabar yankin Nasarawa ta Arewa.
Halayen da na koya a wurin iyayena
Ni dai ban tashi cikin kulawar mahaifiyata ba saboda ta bar gidan mahaifina kafin in girma. Kuma na fito ne daga babban gida, wato mahaifina yana da mata da ’ya’ya masu yawa, saboda haka ne na fi shakuwa da shi fiye da mahaifiyata. Mahaifina wanda aka fi kiransa da Malam Kusin, kafin rasuwarsa ya kasance mai horar da ’ya’yansa da ma wadanda ba nasa ba kan yadda za su fuskanci rayuwa yadda ta kamata. Shi ya sa a duk lokacin da wani yaro ya aikata laifi a unguwarmu za ka ji ana cewa a kai shi wurin Malam Kusin ya hukunta shi. Mahaifinmu ya yi mana nasiha a kan mu rika jin tsoron Allah, sannan ya bukaci mu zauna lafiya da sauran jama’a ba tare da fitina ko musguna wa wani ba da sauransu.
Na tuna lokacin da yake tara mu sannan ya ce mu rika girmama na gaba da mu, sannan yakan fada mana a kowane lokaci cewa bin na gaba tamkar bin Allah ne. Ya fi so na sosai a cikin duka ’ya’yansa, saboda ni ce babbar ’yarsa mace. Kuma har gobe ba zan manta da wasu shawarwari da ya ba ni ba, inda ya ce kada in gayawa wani da yau nake amfana da su. Saboda haka iyayena sun koya mini kyawawan halaye da dama, musamma shi mahaifina kamar yadda na bayyana maka na girma a wurinsa.
kalubale ina karama
Babban kalubalen da na fuskanta a rayuwata a lokacin da nake tasowa shi ne, kamar yadda na bayyana maka a baya ban tashi cikin kulawar mahaifiyata ba, don ta bar gidanmu kafin na girma, to a gaskiya hakan ya kasance mini babban kalubale, don ban samu cikakkiyar kulawa da farin cikin zama da mahaifiya ba. Shi ya sa na samu kaina a cikin wani hali da zan iya bayyanawa a matsayin marar dadi da nake tasowa. Batun talla da wahalar da yara mata da ake fadi yanzu duk sun shafi wasunmu da muke tasowa. Shi ya sa wasunmu ma mun yi saurin girma fiye da shekarunmu a lokacin. Ka ji babban kalubalen da na fuskanta ke nan a rayuwana da nake tasowa kodayake hakan ya koya mini abubuwa da dama da yau zan iya ba da labari.
Tallafi daga maigidana
Shi dai maigidana tamkar mahaifina ne kuma dan uwana nake ganinsa a koyaushe, domin duk abin da ya shafi gidanmu, wato yadda za a samu ci gaba da sauransu, ba ya bata lokaci wajen ba da tallafi. Yana kuma ba ni shawarwari masu amfani, musamman a kan harkar siyasa da nake yi. Shi ya tallafa wa ’ya’yanmu da ikon Allah dukansu har suka kammala karatunsu na jami’a, wasu a cikinsu ma sun yi digiri na biyu. Yana biya wa kowa bukatunsa ba ma ni da ’ya’yana ba kawai har da wasu daga waje. Saboda haka nema addu’ar da nake masa a kullum ita ce Allah Ya ci gaba da saka masa da alheri, Ya kuma bar shi cikin koshin lafiya.
kungiyoyi
Ni ce shugabar kungiyarmu ta kiwon lafiya a nan Jihar Nasarawa, wadda ta kunshi cibiyoyin kiwon lafiya daban-daban da dama a jihar nan. Ina kuma daya daga cikin mambobin kungiyar Matan Najeriya. Ina cikin kungiyar Matan Karkarar Najeriya. Ni ce kuma Shugabar kungiyar Gida-Gida don tabbatar da nasarar Gwamna Almakura a shekarar 2015 a jihar nan a siyasance ke nan. Ina cikin kungiyoyi da dama a ciki da wajen jihar nan.
Takara a siyasa
Abin da ya ba ni karfin gwiwar fitowa takarar kujerar majalisar dokokin jihar nan shi ne, yadda mata yau ba sa son fitowa takara ko yin gwagwarmayar siyasa a kasar nan. Na biyu ka ga mu mata ke jefa kuri’u mu zabi maza, amma da zarar sun yi nasara ba sa tunawa da mu wajen ba mu mukamai da tallafa mana da sauransu. Shi ya sa nake so in fito takara don in kirkiro da dokokin da za su kwato mana ’yancinmu daga wurin mazaje. Kuma ina so in yi amfani da wannan damar in yi kira ga ’yan uwana mata cewa su tashi su nemi ilimin zamani da na addini su kuma fito kwansu da kwarkwata don su kada kuri’unsu ga jam’iyyar APC mai adalci, don ita ce kawai za ta iya kwato musu ’yancinsu, ta kuma gudanar da shugabanci nagari a kasar nan.