✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajiya Maimuna Muhammad Bala: Komai na rayuwa sai da ilimi

Hajiya Maimuna Muhammad ita ce mai ba Gwamnan Jihar Kebbi Sa’idu dakingari shawara ta musamman kan harkokin Ilimi. Ta yi shugabancin makarantun sakandare a Jihar…

Hajiya Maimuna Bala Muhammad  dauke da lambobin yabon da ta samu wajen taimakon al’umma Hajiya Maimuna Muhammad ita ce mai ba Gwamnan Jihar Kebbi Sa’idu dakingari shawara ta musamman kan harkokin Ilimi. Ta yi shugabancin makarantun sakandare a Jihar Sakkwato da Kebbi. Ta yi aiki da Ma’aikatar Ayyuka da ta Ruwa da Lafiya da ta Matasa da Wasanni a Jihar Kebbi. Ta bukaci iyaye su ba ’ya’yansu ilimi domin komai na ruwa yanzu sai da ilimi.

Tarihina
Assalamu alaikum, sunana  Hajiya Mai-muna Muhammad Bala,  an haife ni a garin Zuru da ke Jihar Kebbi a ranar 5 ga Mayu, 1954. Na shiga makarantar firamare a Zuru a shekarar 1958, daga nan na yi makarantar kwaleji da ke Katsina daga shekarar 1966 zuwa 1968.  Bayan shekara biyu sai na dawo W.T.C da ke Birnin Kebbi,  inda na samu shaidar karatu ta Grade Two.
Kafin jarrabawa ta fito sai na fara koyarwa a wata firamare a Zuru daga 1970  zuwa 1971. Bayan jarrabawata ta fito sai na yi makarantar horon malamai da ke Kano daga 1972 zuwa 1975, kafin na kammala ne na yi aure,  ina nan a gidan mijina har a 1978 sai na samu shiga Jami’ar danfodiyo da ke Sakkwato, inda na yi digiri na farko a kan Turanci. Bayan na kammala ne na yi hidimar kasa a W.T.C Bodinga, ina wannan makaranta kafin in kammala sai Hukumar Ilimi ta Jihar Sakkwato ta nada ni shugabar rikon makarantar. Ina kan wannan mukami sai Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Sakkwato ta gamsu da bajintar da na yi, don haka tun kafin na kammala hidimar kasa, sai aka tura ni GGSS Rabah a matsayin shugabar makarantar, daga nan kuma aka mayar da ni W.A.T.C  Gusau 1983.
A 1989 sai aka dawo da ni Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Sakkwato, ina nan a ma’aikatar ilimi sai aka samu wata matsala a GGSS Rabah, sai aka sake mayar da ni matsayin shugabar makarantar. Bayan wata uku na gyara komai.
Daga nan aka dawo da ni inda nake aiki wato Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Sakkwato. Daga baya na zama shugabar makarantar GGC Sakkwato.
Bayan an kirkiro Jihar Kebbi a 1991 sai na dawo jiharmu, inda aka kai ni Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha a matsayin Mataimakiyar Darakta mai kula da sashen jarrabawa, ina nan a wannan ma’aikata sai matar Gwamna Abubakar Musa Garkuwa ta nuna tana son jami’i mai kula da tsare tsare a ma’aikatar kula da mata, sai aka tura ni a ma’aikatar, bayan nan a 1994 sai aka tura ni ofishin cabinet office, a matsayin Darakta mai kula da al’amuran siyasa,  a cikin shekarar 1996 aka ba ni Kwamishinar Ruwa da Albarkatun kasa, ni ce kwamishiniya ta farko a wannan ma’aikata, daga nan na yi Kwamishinar Al’amuran Mata daga 1998 zuwa 1999. Na yi digiri na biyu a shekarar 2002 a Sakkwato.
Bayan na kammala wa’adin kwami-shinar mata, sai na rubuta wa gwamnati na dawo aiki, daga nan aka tura ni Ma’aikatar Ayyuka a matsayin Darakta Mai Kula da Sha’anin Mulki, daga nan na zama Babbar Sakatariya. Na yi aiki da Ma’aikatar  daukar Ma’aikata da ta Ruwa da ta Lafiya da ta Matasa da Wasanni. Na yi ritaya a shekarar 2010.
Bayan na yi ritaya 2010 sai Gwamnan Jihar Kebbi Sa’idu Usman Nasamu ya nada ni mai ba shi shawara ta musamman kan harkokin ilimi.
kalubale
Akwai lokacin da aka tura ni GGSS Rabah inda na je na tarar da matsaloli masu yawa, akwai rashin da’a da abubuwa wadanda  ba su dace ba a makarantar, na samu kalubale sosai daga malamai maza, amma bai kamata in fade su ba, Allah Ya taimake ni makarantar ta koma daidai; amma kafin in gyara makarantar na sha wahala sosai.
Haka kuma a Gusau, ko da na je maka-rantar na tarar dalibai na fada, su ma malamai na fada, ranar da na isa makarantar na tarar tana cin wuta, hankalina ya tashi sosai. Amma cikin kankanen lokaci Allah Ya taimake ni komai ya daidaita.
Abin da ba zan taba mantawa da shi ba
Abin da ba zan taba mantawa da shi ba bai shafi aikina ba, wato ranar da mahaifiyata ta rasu. Ita ce ta ba ni goyon baya na yi karatu, ta nuna mini amfanin karatu.
Shawara ga iyaye
Shawarar da zan ba mata ita ce, su ba ’ya’yansu ilimi, har ya kasance ko iyaye na da rai ko ba su da rai za su zama ’ya’ya nagari, sannan su aza su kan sana’o’i. Amma a ce mace sai ta je tana bara ko tana bin gidajen jama’a tana roko, amma idan tana da iliminta ba za ta wulakanta ba ko ba ta aiki akwai sana’o’i,  wadanda in ba ka da ilimi ba za ka yi su ba, ina kira ga mata su koyi sana’a, don su taimaka wa ’ya’yansu  da mazajensu, amma idan iyaye ba su nuna wa ’ya’yansu ilimi na da amfani ba, su ma ba za su damu da shi ba.
Mace mai ilimi za ta iya kula da gida da mijinta da ’ya’yanta da makarantarsu da lafiyarsu da tsaftar gida, idan ba ta da ilimi ba za a samu haka ba. Komai sai a rika dora wa maigida, abin da bai kai ya kawo ba sai ka ji uwar gida na cewa a jira maigida  ya dawo.  Zai matukar wahala a ga mace mai ilimi amma ’ya’yanta kuma su kasance cikin rashin tsari da koshin lafiya.
Abubuwan da na fi sha’awa
Ni mace ce mai sha’awar rubuce–rubuce da karance-karance, a kan haka ne ma tun ina sakandare na fara rubuta littafi. Littafi na farko da na fara rubuta shi ne ‘Sadik and Ten Regulations’ na kaddamar da shi a 1991. Na kuma samu alheri sosai domin a lokacin Naira 200 kudi ne mai yawa, daga baya na rubuta littattafai har guda tara na Turanci da Hausa, daga cikin su akwai ‘Dikko dan Maice’ da, ‘Kada Mai Rikida’, sai ‘Kowa Na son Nagari’ da kuma ‘Wasiyyar Sarkin Gambo da kuma ’ya’yansa’. Daga cikin na Turanci akwai:  ‘A Joy in The Cradle’ da ‘He Who Laugh Last’ sai kuma ‘Career berses for Unibersal Basic Education’ dukkan wadannan littattafai na Turanci da na Hausa, suna koyar da halaye nagari, ’ya’ya su kasance nagari, su bar mugayen halaye kamar  shan giya da zina da caca da luwadi da rashin da’a ga iyaye ko shugabanni da shan taba da sauran kayan da ke sa maye. Su kuma kasance masu koya wa yara su gyara Turancinsu. Yanzu haka ina nan ina rubuta wasu amma ban sanya musu sunaye ba, domin sun shafi tarihin annabawa ne.
kasashen da na ziyarta
Na je wani kwas a Cibiyar Horaswa ta International Training Centre, Worthing, a kasar Ingila, na kuma je Brazil da India da Sudan da Nijar da Saudiyya da Suwazilan da sauransu.
Zama da maigida
Lokacin da ina tare da maigidana ba a iya sanin ko akwai wata matsala tsakaninmu, ba na jiransa kafin na yi cefanen gida, haka kuma kamar abincin gida da kuma kula da yara kamar suturarsu ko tawa gaskiya idan ina sukuni ba na jira ya yi mana, amma idan ya yi mana, sai mun kari yi masa godiya.
Haka kamar gyaran gida  ko wani wuri ya balle a cikin gida ko gyaran kujeru ba na tsayawa in ce lallai sai ya yi, amma kuma duk abin da na yi a gida babu wanda zai taba sanin na yi, har ’ya’yanmu ba za su sani  ba, nakan nuna musu ni da shi muke yi, muna hada gwiwa domin domin rufin asirinmu da na ’ya’yanmu.

za ka yi su ba, ina kira ga mata su koyi sana’a, don su taimaka wa ’ya’yansu  da mazajensu, amma idan iyaye ba su nuna wa ’ya’yansu ilimi na da amfani ba, su ma ba za su damu da shi ba.
Mace mai ilimi za ta iya kula da gida da mijinta da ’ya’yanta da makarantarsu da lafiyarsu da tsaftar gida, idan ba ta da ilimi ba za a samu haka ba. Komai sai a rika dora wa maigida, abin da bai kai ya kawo ba sai ka ji uwar gida na cewa a jira maigida  ya dawo.  Zai yi matukar wahala a ga mace mai ilimi amma ’ya’yanta kuma su kasance cikin rashin tsari da koshin lafiya.
Abubuwan da na fi sha’awa
Ni mace ce mai sha’awar rubuce–rubuce da karance-karance, a kan haka ne ma tun ina sakandare na fara rubuta littafi. Littafi na farko shi ne ‘Sadik and Ten Regulations’ na kaddamar da shi a 1991. Na samu alheri sosai domin a lokacin Naira 200 kudi ne mai yawa, daga baya na rubuta littattafai har guda tara na Turanci da Hausa, daga cikin su akwai ‘Dikko dan Maice’ da, ‘Kada Mai Rikida’, sai ‘Kowa Na son Nagari’ da kuma ‘Wasiyyar Sarkin Gambo da kuma ’ya’yansa’. Daga cikin na Turanci akwai:  ‘A Joy in The Cradle’ da ‘He Who Laugh Last’ sai kuma ‘Career berses for Unibersal Basic Education’ dukkan wadannan littattafai na Turanci da na Hausa, suna koyar da kyawawan halaye, ’ya’ya su kasance nagari, su bar mugayen halaye kamar  shan giya da zina da caca da luwadi da rashin da’a ga iyaye ko shugabanni da shan taba da sauran kayan da ke sa maye. Su kuma kasance masu koya wa yara su gyara Turancinsu. Yanzu haka ina rubuta wasu amma ban sanya musu sunaye ba, domin sun shafi tarihin Annabawa ne.
kasashen da na ziyarta
Na je wani kwas a Cibiyar Horaswa ta International Training Centre, Worthing, a kasar Ingila, na kuma je Brazil da India da Sudan da Nijar da Saudiyya da Suwazilan da sauransu.
Zama da maigida
Lokacin da ina tare da maigidana ba a iya sanin ko akwai wata matsala tsakaninmu, ba na jiransa kafin na yi cefanen gida, haka kuma kamar abincin gida da kuma kula da yara kamar suturarsu ko tawa gaskiya idan ina da sukuni ba na jira ya yi mana, amma idan ya yi mana, sai mu yi masa godiya.
Haka kamar gyaran gida  ko wani wuri ya balle a cikin gida ko gyaran kujeru ba na tsayawa in ce lallai sai ya yi, amma duk abin da na yi a gida babu wanda zai taba sanin na yi, har ’ya’yanmu ba za su sani  ba, nakan nuna musu ni da shi muke yi, muna hada gwiwa domin domin rufin asirinmu da na ’ya’yanmu.