Hajiya Laraba Dattijo sananniya ce da ta yi fice a ayyukan sa-kai, musamman bangaren taimakon al’umma a Jihar Sakkwato. Ta yi fice ne bayan ta gina wani gidan marayu da dukiyarta kafin daga baya gwamnatin Jihar Sakkwato ta karbe gidan daga hannunta inda ya koma na gwamnati. Ta yi yawo kasashe daban daban don taimakon al’umma, musamman marayu da marasa galihu. Aminiya ta ji ta bakinta don sanin sirrin ficen da ta yi wurin taimakon al’umma da sauran batutuwa kamar haka:
Tarihinta da Ayyukanta:
An haife ni a Jihar Kano. Na yi karatun firamare a Kano amma sai na koma Sakkwato don kammala a darul kur’an inda na hada da yin karatun Sakandare duk a wannan makaranta, ban tsaya a nan ba sai na wuce Jami’ar Usman danfodiyo da ke Sakkwato. Da na kammala ne sai na mayar da hankalina a wurin ayyukkan sa-kai da suka sanya ni tafiye-tafiye zuwa kasashen waje inda na yi kwasa-kwasai da yawa a garuruwa goma sha daya na Amurka irin su New York da Danba da Chicago da Colorado da San Francisco da Atlanta Geogia da sauransu. Kuma har yanzu ina bisa ga ayyukkan sa kai na kungiyoyi masu zaman kansu. Yanzu haka ni ce shugabar kungiyar mata da ake kira (Women and Youth for Rural Debelopment). Harkar kungiyoyi ta sanya ni zama Sakatariya a Jam’iyyar Matan Arewa (JMA) ta Sakkwato. Ni na kafa gidan marayu na Jihar Sakkwato a lokacin da nake kula da marasa galihu. Na zama shugabar riko ta majalisar mata ta jiha. An zabe ni daga cikin mata masu kula da kidayar jama’a. Na zama shugabar mata mafi nasara a jiha. Na zama memba a amitattun mata ta arewa ta yamma da kungiyar tuntuba ta Arewa da kuma memba a mata masu son cigaba a jiha, da shugabar mata a Jami’ar danfodiyo kuma na shiga cikin majalisar zartarwa da kwamitin amintattu. Kwamitin amintattun ilmin mata da tallace-tallacensu ni ce shugaba, Sakatariyar majalisar mata ta kasa kan siyasa da wayar da kansu da cigaba. Memba a hukumar yawon bude ido ta jiha. Ni na kirkiro asusun miliyan 50 don tallafawa masu cutar yoyon fitsari a asibitin Maryam Abacha. Kafin wannan asusun sai da na samar masu da gadaje 12 da katifu da kujeru da koyawa majinyata hanyoyin dogaro da kai. Na shirya ziyarori a gidan yari daban-daban. Na wakilci matan kasar nan a Cairo da Libiy. Haka kuma ni memba ce a hukumar masana’antu da ciniki ta jiha da kuma Hadaddiyar kungiyar sa kai ta jiha da kuma kasancewat Babbar Mai binciken kudi a Hukumar bunkasa masana’antu da kasuwanci ta Jihar Sakkwato.
kalubalen da na fuskanta:
kalubalen da ake samu bai fi mutum bai fahimci lamurra ba sai ka yi ta samun matsala. Aikin da muke yi na sa-kai yawanci ana fadakar da mutane kan abin da ba su sani ba, don haka dole ne a fuskanci kalubale tun da akwai bambancin ra’ayi. Wasu na kallon muna fitar da ’ya\yansu mata ne daga gidajensu don su lalace, don suna yi mana kallon matan siyasa mabarnata ne. Hakan dai bai sanya mu daina wayar da kai da ilmantarwa ba har aka samu cigaban da muka samu a yanzu.
kasashen da na ziyarta:
Amurka da Libiya da Nijar da Burkina Faso da dukkan jihohin Nijeriya.
Burina a rayuwa:
Ban da wani buri kamar in gama lafiya da duniyar nan. A tuna da ni ga dukkan abin da na aiwatar da ya samu nasara. Kamar gidan marayun nan na jihar Sakkwato da na kafa shekaru da suka gabata duk wanda ya sanni to a kan taimakon marayu ya sanni. Ka ga duk wanda ya san ni na kafa gidan in ya wuce ta gaban gidan zai tuna da ni ya yi mini addu’a a matsayin uwar marayun Jihar Sakkwato.
Wata kawata da ake kira Hajara Yaldu, ma’aikaciya ce a ma’aikatar jin dadi da walwala ta jihar Sakkwato ta taba kawo min labarin wani jariri da aka jefar a bola, nan da nan muka garzaya muka dauko shi kuma muka ci gaba da ba shi kulawar da ta kamata. Ba shi kadai ba, akwai sauran yara masu yawa da muka tarbiyantar da su tun suna kanana. Wasu ma sai bayan da suka girma suka mallaki hankalinsu ne sannan suka gano iyayensu na asali. Ka ga wannan ai babbar nasara ce.
A halin da ake ciki na mika gidan marayun da na gina ga gwamnati don ba zan iya tafiyar gidan ni kadai ganin yadda gidan ya bunkasa. Sannan an samu matsala bayan wadanda na dauka a wancan lokaci don su kula da gidan tuni suka daina wai fada musu cewa yin ido biyu da marayu da safe haramun ne. Na yi kokarein fahimtyar da su cewa wadannan yara ba shegu ba ne, marayu ne amma abin ya ci tura. Sannan tallafin Naira dubu dari biyu da gwamnati ke ba ni a matsayin tallafi ba ya isa don haka na yanke shawarar mika gidan kacokan ga gwamnatin jiha don ta cigaba da ba shi kulawar da ta dace.
Shawarata ga mata:
Yanzu ba wata mace da ba ta san ciwon kanta ba. Yakamata su fito da hanyoyin taimakawa mazajensu da kuma dangoginsu. Sannan ina kira ga gwamnati ta tallafawa mata musamman wadanda ke gida ba sa fita da hanyoyin dogaro da kai. Yanzu idan ka lura an samu cigaba sosai a karatun mata, don an daina ma tinkaho da digiri na daya.
Abin da ba zan taba mantawa da shi a rayuwa ba:
Akwai wata unguwa da ake kira kofar Marke mun je duba marar lafiya sai muka biya ta wani gida, babban gida ne muka samu matar gidan tana yin daka, kusan karfe goma na dare. Da na tambaya me ya sa take daka yanzu ba ta bari sai da safe take gaya mana cewa mai gidanta ne ba ya shan furar da aka dama ta da inji. Har sai da maigidanta ya doke ta a kan me ya sa ta yi amfani da inji wajen dama masa fura, shi da hannu yake so a dama masa kuma ya umarce ta komai dare ta yi masa wata furar kuma da hannu za ta dama masa. Wannan bayani da matar nan ta yi mana ya tayar min da hankali kuma ba zan taba mantawa da shi a rayuwa ba.
Sai dai muna fata maza su fahimci halin da matansu ke ciki kuma su rika tausaya musu don cigaba da jin dadin zaman aure. Aure dai ibada ne, ba bauta ba ne don haka ya dace ma’aurata su fahimci haka. Allah Ya sa mu dace, amin.