✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajiya Fatima Sharif: Kowace mace za ta iya sana’ar noma

Hajiya Fatima Muhammad Sharif ita ce Shugabar kungiyar Mata Manoma ta Jihar Kano (AFAN). Ta bayyana wa Zinariya yadda hakuri da juriya suka sa ta…

Hajiya Fatima Muhammad Sharif ita ce Shugabar kungiyar Mata Manoma ta Jihar Kano (AFAN). Ta bayyana wa Zinariya yadda hakuri da juriya suka sa ta zama babbar manomiya. Ta ce babu sana’ar da ta fi noma samar da aikin yi da kuma riba hade da bunkasa tattalin arziki cikin kankanen lokaci. 

Tarihin rayuwata
An haife ni a kauyen Yako da ke karamar Hukumar kiru ta Jihar Kano. Na yi makarantar firamare ta LEA Central a Yako. Bayan na kammala sai na koma wurin mahaifiyata a lokacin tana aure a Kaduna, a nan na shiga Makarantar GGSS Unguwar Rimi. Daga nan ban ci gaba da karatu ba sai na yi aure a garin kiru. Daga baya kuma sai ni da maigidana muka koma Legas da zama, daga bisani aka kashe shi a wani fadan kabilanci.
Yadda na fara noma
Bayan rasuwar maigidana sai na dawo gida kiru da zama, daga nan na kama sana’a don na taimaki kaina da marayun ‘ya’yana. Da farko na fara sana’ar kiwon kaji daga baya sai na koma kiwon awaki. Ana nan sai na fara kiwon kifi. Daga baya sai na shiga harkar noma. Da yake tun ina makaranta akwai wani karatu da aka koya mana wato ‘domestic science ‘ wanda aka koya mana yadda ake noma da kiwo da sauransu. Wannan ya sa na tashi da sha’awar shuke-shuke, don ina iya tunawa tun ina karama nake shuka masara a gida. Na fara ne da noman shinkafa a garinmu kiru a lokacin nakan noma kimanin buhu takwas. Ana haka sai abin ya bunkasa har muka kafa kungiya ta mata masu noman shinkafa a kauyenmu. Ganin haka ya sa masu shirin FADAMA suka kira mu suka yi mana bita tare da ba mu tallafin iri da taki da sauran kayan aiki, sannan suka bukaci mu koma da yin nomanmu a Fadama, kasancewar ita shinkafa ta fi son wurin da ruwa yake. Muna farawa sai ga shi mun samu buhu 300. Da muka ji dadi sai muka rika karbar hayar tantan a ma’aikatar ayyukan noma ta Jihar Kano, inda muke yin amfani da su wajen nomanmu a wannan shekara sai muka samu buhu 700.
Satifiket da kyaututtuka
Babu shakka dalilin wannan sana’a na samu halartar kwasa-kwasai da bitoci da dama. Akwai lokacin da jami’an Hukumar USAID suka zo suka ga abin da muke yi, sai abin ya ba su sha’awa, suka gayyace ni wani kwas inda suka umarce ni da na zo na koya wa sauran matan da muke wannan harka tare abin da na koyo. Haka kuma wata kungiya ta koyar da mu yadda ake gyaran shinkafa, babu shakka na karu matuka daga wannan bita da aka yi mana sosai. Haka kuma Babban Bankin Najeriya (CBN)sun ba mu lambar yabo.
Nasarori
Na shafe shekara 20 ina noma babu abin da zan ce sai dai na mika godiyata ga Allah, domin tun ina noma buhu bakwai ko takwas a karamar gona, yau ga shi ina da manyan gonaki guda biyu, ina kuma noma sama da buhun shinkafa dubu da 500. A yanzu haka na bude kamfani wanda nake karbar aikin shinkafa ana biya na ladan aikina.
kalubale
Duk abin da mutum yake yi a rayuwa ba ya rasa kalubale, kimanin shekara biyu da suka gabata an yi ambaliyar da ta tafi da duk amfanin gonata, domin na yi asara ta fi ta Naira miliyan biyar wanda hakan ya jawo jarina ya yi kasa, kasancewar ba mu samu kowane irin tallafi daga gwamnati ba, duk da cewa an yi ta zuwa ana kiyasin kwatankwacin asarar da muka yi, sai dai har zuwa yau ba mu ga ko kwabo ba. Haka kuma mukan samu matsaloli da abokan aiki, da yake ba komai mutum yake iya yi da kansa ba, dole sai ya nemo mataimaka. Haka kuma akwai kalubale da muke fuskanta daga ‘yan uwa maza manoma wadanda a kullum nake korafin abin da suke yi mana, maimakon a ce sun karfafe mu, amma kullum kokari suke yi su ga mun koma baya.
Ayyukan da kungiyar Monama take yi
Duk da cewa kungiyarmu ta manoma mata muna da membobi sama da 1,500 a fadin Kano, wadanda suke noma abubuwa daban-daban, a cikinmu akwai manyan manoma da kanana. Sai dai a kullum muna kokarin tallafa wa kananan cikinmu. Wani lokaci za ka sami mace mijinta ya mutu ya bar ta da ‘ya’ya ba ta da hanyar da za su ci abinci, hakan ya sa mukan ba su turaren shinkafa kamar buhu daya ko biyu, idan suka turara sai su dawo da kudin su sake karbar wani, to da haka suke samun nasu rabon.
Mukan hada kai da Hukumar KNARDA inda suke saye har na Naira miliyan daya da rabi. Shinkafar ci bayan an kammala gyara ta mukan samu buhuhuna kanana da manya mu zuba ta a ciki sai mu rika kai wa bankuna muna sayarwa yadda za a biya mu kudinmu a dunkule. A yanzu haka ma wata kungiya da ta zo ta ga yadda shinkafarmu take, sai suka gayyace mu cewa suna so mu kulla kawancen kasuwanci da su yadda za su rika fitar mana da shinkafar kasashen waje.

Iyali
Kamar yadda na fada maigidana ya rasu ya bar ni da ‘ya’ya biyar, maza uku; mata biyu. A yanzu haka babban cikinsu ya kai shekara 25 yana karatu a Health Technology, sannan na biyun kuma soja ne yana Kaduna, sai na ukun ya samu gurbin karatu a Makarantar Hakar Man fetur da ke kudancin kasar nan, yanzu haka ma shirye-shiryen tafiyarsa ake yi. Sai mace wacce take Makarantar Sakandiren Gidauniya da ke Bebeji sai ‘yar autarsu da ke wata karamar sakandire a Kaduna.
Buri
Babban burina yanzu bai shige na ga kafuwar kamfanina Mai suna Kano Women Agro Allied Processing Company ba. Kasancewar a yanzu idan muka yi aikin shinkafarmu daga samfarera sai mu yi mata turare sannan sai mu dauko ta mu kawo ta Kano inda za a gyara a fitar da dutse daga ciki, hakan ya sa nake so na kafa kamfanin inda za mu rika dukkanin wannan ayyukan da kanmu. Haka kuma idan kamfanina ya kafu zan samu damar mu’amala da mutane masu kananan sana’o’i inda za mu rika ba su horo a kan aikin noma.
Abin da na fi so a tuna ta da shi
Ina so ko bayan ba ni a duniya a tuna da ni a matsayin wacce ta taimaki jama’a suka tsaya da kafafunsu. Babu abin da yake min dadi illa na ga mutane suna samun abu a karkashina, wannan ya sa idan na yi shinkafa ba na yarda na kai inji a yi min turare na fi so na dauki mutane su yi da hannunsu yadda za su sami abin kashewa. Baya ga abincin da muke samar wa jama’a, ga kuma ayyuka da ake samarwa. A yanzu haka mutane sama da 200 ne ke cin abinci a karkashina.
Kira ga gwamnati
Muna sane da shirye-shiryen da gwamnati tun daga matakin tarayya zuwa jiha take yi wajen taimakon manoma, sai dai kuma wannan magana tana tsayawa ne kawai a jarida, domin mu manoman na hakika ba ma samun wannan tallafi da sauransu. Muna kira ga gwamnati da ta ba harkar noma muhimmanci, kasancewar a duniya babu sana’ar da ta fi noma muhimmanci, baya ga abinci da ake samawar wa jama’a ga kuma samar da ayyukan yi ga jama’a.
Haka kuma ina kira ga gwamnati idan za ta bayar da taki ta rika bayarwa a farkon damina, amma ba sai damina ta wuce ba. Haka kuma muna kira ga gwamnati da ta rika ba mu rance saboda idan mun je bankuna ba ma samu, sai a ce wai sai mun kawo jingina mai kudi da yawa wacce kuma idan an duba ba mu da ita. Haka kuma mun san cewa akwai kungiyoyi na duniya da ke kawo mana tallafin noma, amma ba mu gani.
Ina fata a duk lokacin da gwamnati ta tashi ba mu wani tallafi to ta neme mu kai tsaye, kada ta rika hada mu da maza, domin wallahi idan ya je hannunsu ba ma ganin komai.
Shawarata ga mata
Idan mutum yana yin sana’a kada ya raina ta, ya yi kokari ya rike ta da kyau, domin bai san nasibin da zai samu a ciki ba. Mata su kama sana’a sosai, kada su zauna haka suna jiran sai mazansu sun yi musu komai na rayuwa. Haka kuma ina kira ga mata wadanda ke sha’awar noma da su fara, sana’a ce ta rufin asiri kuma mai sauki. Kowace mace za ta iya sana’ar noma. Idan kin ga ba za ki iya yi da kanki ba, to akwai yaran da za ki iya sanyawa su yi miki.