✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajiya Fa’iza Ahmad: Mata a rika kula da gida

Hajiya Fa’iza Ahmad ita ce  rijistara Kwalejin horar da malamai ta tarayya(FCE) da ke Yola a karkashin Jami’ar Adamawa. A hirarta da Zinariya ta ba…

Hajiya Fa’iza Ahmad ita ce  rijistara Kwalejin horar da malamai ta tarayya(FCE) da ke Yola a karkashin Jami’ar Adamawa. A hirarta da Zinariya ta ba matasa shawara kan yadda za su inganta rayuwarsu, ta yi bayani

Tarihina
Sunana Fa’iza Ahmad, ni ’yar Yola ce amma an haife ni a Kaduna. Na yi firamare a Yola, sannan na yi sakandare a Maiduguri, sai Jami’ar Bayero inda na yi digiri a harshen Turanci a bangaren koyarwa. Bayan na kammala ne na fara aiki a 1985 a makarantar sakandare ta Adamawa, bayan shekara 3 sai na koma Jami’ar Maiduguri na yi digiri-na-biyu shi ma a fannin koyarwa amma a bangaren ba dalibai shawara. Daga nan na ci gaba da karantarwa a Adamawa har na kai matsayin shugabar makaranta (principal).
A shekarar 2001 ne na fara aiki da makarantar FCE da ke Yola a sashin gudanarwa, wato a bangaren rijistiri inda na zama principal assistant registrar. Har yanzu dai ina aiki a FCE din a matsayin rijistararsu.
Abin da ba zan manta da shi ba tun ina karama
A lokacin da nake karama akwai lokacin da muka yi bako, sai aka samu akasi mahaifinmu ba ya nan, a lokacin mu takwas ne a gida, sai mu yaran muka fita muka gaishe shi, sannan muka gaya masa cewa babanmu ba ya nan. Sai bakon ya fara raba taro da sisi, sai sauran ’yan uwana suka ce mini in je in karba sai na ki. Kuma na ci gaba da wasan da nake yi. Da babanmu ya dawo aka ba shi labari sai ya yi fushi game da yadda sauran ’yan uwana suka karbi kudi wajen bako. Ya yi musu horo ni kuma sai ya yaba mini a kan cewa hakan da na yi ya nuna rashin kwadayi ne kuma yana da kyau a rayuwa. A lokacin ban fahimci irin fusatar da babanmu ya yi da abin ya faru ba. Amma yanzu da yake na zama uwa, sai na ga ba zan so hakan ya faru ga ’ya’yana ba.
Shakuwa tsakanin iyayena
Akwai mata da yawa a gidanmu saboda haka bangaren mahaifinmu daban yake da namu, sai na fi shakuwa da mahaifiyata, amma bayan na girma a gaskiya na fi shakuwa da mahaifina. Yadda maigidana yake cudanya da ’ya’yanmu akwai bambanci da yadda muka girma a wurin iyayenmu. Mahaifina ya kasance mai sauraren mu duk da yake tsarin zaman ya bambanta. Ta haka idan ma kana son yin wani tadin za ka yi masa ba tare da shakka ba. A kodayaushe idan har ina da lalura, mahaifina yakan tsaya mini a duk inda nake.

Abin da na koya daga mahaifina
Mahaifina mutum ne mai son ganin gaskiya ta tsaya da kafafunta. Ya yi karatun addini har ya zama alkali, kuma ya yi iya gwargwadon iyawarsa wajen tarbiyyantar da mu a bisa tsarin da addinin Musulunci ya tanada. Yanzu muna kokarin koyi da halayensa. Sai dai akwai abin da na kasa koya, wato mahaifina mutum ne mai bin lokaci, in dai ya ba ka lokaci, misali karfe hudu; hudun nan tana cika za ka gan shi. Wani lokaci nakan saba lokaci saboda yawan ayyuka.  Kuma wannan abin yana damuna sosai. Amma Allah Ne mafi sani.

Abin da na koya daga mahaifiyata
Mahaifiyata ba ta son a rika yi mata karya. Idan ta gane an yi mata karya, to akwai babbar magana. Amma ko da ta fusata, idan aka gaya mata gaskiyar magana, sai ta yi hakuri. Tana da tsafta, domin ba zan manta ba daga mun tashi da safe, kafin sallar Asuba,  za mu gyara gadonmu. Kuma idan mun sauka ba ta son a sake komawa domin tana son ganin ko’ina da tsafta. Tsafta na cikin abubuwan da na koya a wurinta. Ya kamata mata su rika tsabta.
Yadda na hadu da maigidana
Na hadu da maigidana a nan Yola, bayan na gama karatun sakandare, sai na shiga makarantar koyar da shari’a, sai wata rana wani ya ce ana mini magana, sai na tarar da shi, tun ranar ma ya gaya mini cewa aure na yake so ya yi. Allah Ya sa akwai rabo sai Allah Ya tabbatar.
Kyautar ba-zata daga maigidana
Akwai lokacin da nake makaranta za mu fara jarrabawa, sai na tsorata domin ina ganin ban yi shiri sosai ba, kasancewar na yi rashin lafiya sai ban samu damar yin karatu sosai ba, abin mamakin shi ne, ya turo wani mutum daga Kano zuwa Yola don ya kawo mini katin karfafa gwiwa, inda a ciki yake cewa yana da yakinin zan ci jarraba domin ya san ni mai kwazo ce. Gaskiya hakan ya burge ni.
kalubalen da na taba fuskanta a wurin aiki
Ba za a taba rasa kalubale a rayuwa ba. Tun ranar da na fara aiki, nake son yadda tsarin aikin yake, amma sai na ga wani lokaci akwai bambanci. Idan mutum mai kwazon aiki ne ba a yi masa uzuri, sai ya kasance ranar da aka samu kuskure, a rika kananan maganganu ke nan, kin ga ya kamata mai yi kullum ranar da bai yi ba sai a yi masa uzuri, amma abin ba haka yake ba. Wannan yana cikin abin da yake ba ni mamaki kuma har yanzu ban gane me ya sa ba.
Shawara ga matasa
Shawarata ga matasa ita ce, su nemi ilimi. An koyar da mu a jami’a a kan cewa duk abin da zai iya kawo canji mai kyau sai an samu ilimi a ciki. Shi ilimin zai nuna yadda za a yi tsarin rayuwa da kuma sanin yadda za a yi cudanya da mutane. Samun ilimi zai cire jahilci domin duk inda akwai jahilci, to akwai wahala. Zamantakewar gida na dan Adam in akwai jahilci yana da wahala.
Mata su nemi ilimi domin su masu ba da tarbiyya ne. Mace jahila ba za ta iya ba da kyakkyawar tarbiyya ba. Duk matar da ba ta da sani, to ba ta san abin da ya kamata ta aikata ba.
Na uku, a hakkin mata da ke gida akwai tsarin da aka sa na auratayya: mata ita ce maigida. Akan ce namiji ne maigida amma ni nakan canza ba wai don na nuna fifikon mace a kan maigidanta ba. Ina nufin don ita ce za ta iya gyara gida ya yi dadi. Idan tana da tsari da tarbiyya da kuma ilimi, kuma tana mayar da hankalinta a kan gidanta komai zai tafi daidai. Dalilin da ya sa nake kiranta maigida ke nan. A lura dukiyar miji ma ya zama a kan hakkin ita mata a gida ne. Miji ne mai ciyarwa da shayarwa da ba da wajen zama, amma zamar da wadannan ababen ya danganta da irin matar gidan da ake da ita. Wannan abin da nake son matasa su mayar da hankali a kai. Domin yanzu ina ganin kamar an yi watsi da shi. Ya kamata mata su san cewa lura da gidan nan babban hakki ne gare su.
Matasa su rage gaggawa, daga sun kammala makaranta a lokaci daya suke so su yi aure; su mallaki mota da gida. Wannan gaggawar na saurin haifar da rashin jin dadin rayuwa, domin a kullum suna son abin da Allah bai nufe su da samu ba, ko kuma matsayinsu bai kai sa samu ba.
Abin da nake son a tuna ni da shi
Ina son duk wadanda na yi cudanya da su su tuna a kan cewa na yi musu adalci. Su rika tuna cewa na yi musu abin da ya kamata. Ina son na samu yarda a wurin wadanda nake mu’amala da su, saboda ko ba na nan su rika ba da kyakkyawar shaida a kaina.