✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajiya Asma’u Ibrahim Boyi: Mata a rungumi harkar koyarwa

Hajiya Asm’au Ibrahim Boyi, jami’a ce da ta samar da makarantar da ke koyar da yara masu larura da suka hada da masu makanta da…

Hajiya Asm’au Ibrahim Boyi, jami’a ce da ta samar da makarantar da ke koyar da yara masu larura da suka hada da masu makanta da kurumta  da ‘yan wada da masu gabunci, sannan ta mallaki makarantun da ke koyar da yara masu lafiya a Kaduna da Legas. Ta yi bayanin yadda ya kamata mata su rungumi harkar koyarwa, sannan ta bukaci al’umma su daina kyamar yara masu larura.

Tarihin rayuwata
Assalamu alaikum, sunana Asma’u Ibrahim Boyi, an haife ni a Zariya cikin shekarun 1970, na yi rayuwa a sassan Najeriya daban-daban ciki har da Kudu maso Gabas, hakan ya faru ne saboda yanayin aikin mahaifina. Na fara makarantar firamare a Jihar Enugu, daga baya na fara makarantar sakandare a Mani Jihar Katsina, kodayake na kammala sakandaren ’yan mata ta Dutsin Ma duk a Jihar Katsina.
Bayan na kammala sakandare sai na samu damar shiga makarantar Kaduna Polytechnic, inda na karata aikin jarida, amma kasancewar ina da burin koyarwa ya sanya bayan na yi haihuwar farko, sai na tafi Ingila, inda na je makarantar koyon aikin koyarwa. Bayan na dawo Najeriya sai na fara koyarwa a makarantar Montessori. Bayan wadansu shekaru sai na kafa makarantar Montessori a Legas. A matsayina ta uwa mai jan ’ya’ya a jiki duk larurar da suke dauke da ita, sai na samar da wani bangare a makarantar da zai koyar da masu larura kamar ta gabunci da ’yan wada da sauransu.
Sunan mijina Malam Ibrahim Boyi, darakta ne Hukumar PAN, muna da ’ya’ya hudu.
Yadda na taso
Na yi rayuwa mai dadi a lokacin da nake karama, masu iya magana na cewa da na kowa ne, don haka a lokacin mukan je duk gidan da muka dama, sannan mu ci, mu sha, babu wata fargaba, wani lokacin ma idan mun ci abinci a waje haka za mu kwanta ba tare da mun ci abincin dare a gida ba.
Na shaku da kanina kasancewar mahaifanmu ba su samu haihuwa sai da aka dauki wadansu shekaru, daga baya mahaifiyarmu ta haifi tagwaye, sannan ta ci gaba da haihuwa. Mahaifiyarmu ta rasu ina da shekara 17.
Halayen mahaifiyarmu da na dauka
Na dauki halin yadda mahaifiyarmu take jan kowa a jiki, tana da matukar nuna kulawa ga duk wanda take tare da shi, ba ta nuna wariya, kowane yaro nata ne, bayan ta haihu ’ya’ya da yawa sai muka taso tare cikin so da kauna da kuma samun kulawa daga gare ta, a kwanan nan ina filin jirgin sama sai wani ya same ni, ya gaishe ni da Hausa, sannan ya ce mini yana daya daga cikin yaran da suka taso a gidanmu, saboda yanayin aikin mahaifinmu duk garin da ya je za ka samu ’yan kauyenmu da ke zama ko makaranta a garin, sai ka ga ya zama mahaifinsu, za su zo gidanmu, inda ake mayar da su ’yan gidan.
Burina ina karama
A lokacin da nake karama ba ni da burin da ya wuce in zama malama, shi ya sa yawancin abokaina da wadanda muka taso tare suke kira na ‘Malama’, a lokacin nakan tara duk yaran makwabta a wuri daya, sannan in rika koya musu karatu. Ina gode wa Allah domin burina ya cika.
Dalilin da ya sa na kirkiro makarantar masu larura
 Na samar da makarantar ne ni da kawata ba tare da tunanin samar da ta masu larura ba, wata rana ina ofis sai wata mata ta same ni, ta ce tana da danta mai larura irin ta gabunta, ta kai shi makarantu da yawa amma an ki daukarsa, sai na fada mata ta ba ni lokacin domin ba ni da kwarewa koyar da masu larura kamar ta gabunci da makanta da kurumta da sauransu ba, sannan ba ni da wani malami da ya kware a wannan bangaren, don haka a lokacin da nake zangon karshe na karatuna a Ingila sai na tattauna da wani abokin karatuna a kan al’amarin, inda ya karfafa mini gwiwa a kan batun, daga nan na rika ziyarta makarantun masu larura, na ga yadda ake koya musu da kuma yadda suke rayuwa, hakan ya sa da na zo aikin sanin makamar koyarwa, sai na bukaci a kai ni irin wadannan makarantu, a karshe na samu horo kan yadda ake koya musu.
Yadda na hadu da mijina
Abin mamakin shi ne, na hadu da mijina tun ina shekara 5 zuwa 8, mahaifansa da nawa abokai ne, wata rana sai aka dauke mu don mu halarci bikin ’yar uwarsa a kauyensu, ban san me ya debi ni na shiga yawo ba sai na yi batan kai, na rika kukan neman taimako, ina ta yawo a kan titi, yana yawo a kan kekensa sai ya gan ni, inda ya dawo da ni gida. Bayan ya dawo da ni gida mahaifiyarmu ta yi farin ciki, inda a nan ya rika fada wa ’yan uwansa cewa zai aure ni, mahaifiyarmu kamar da wasa ta ce tun da ya samo ni, to kuwa za ta aura masa ni.
Mun manta da abin da ya faru, kowa ya ci gaba da rayuwarsa. Bayan wadansu shekaru sai ya nemi ya gan ni, a nan ya tambayi ’yan uwansa mata ina zai same mu, ai kuwa muna zaune sai muka ji an yi sallama, mahaifiyata ta tambaye ni wane ne yake sallama, na ce mata ban san ko wane ne ba, amma na ga kamar yana kama da gidansu wane, sai ta ce in shigo da su, daga wannan rana muka fara soyayya, a yau ga shi mun yi aure har mun samu ’ya’ya hudu.
Babbar kyauta daga mijina
Ban cika son kayan kyale-kyale ba, a wani bangare zan ce mijina ya ba ni kyautar soyayya; ya ba ni kyautar karfafa gwiwa da kuma shawarwari.
Farin cikin zama uwa
Na yi farin ciki sosai, mun samu haihuwa ta farko ne a shekarar 1993 a Kaduna, na yi kuka sosai, saboda na so a ce mahaifiyata ta ga jikokinta kamar yadda takan nanata burinta ta ga jikokinta. Takan ce ina hasashen irin ’ya’yan da za ki haifa da Ibrahim, ina tsammani za su zama kamar Turawa ne, don haka lokacin da na haifi ’yata ta farko, sai na kalle ta na ce ina ma mama tana raye ta gan ki.

Lura da su a lokacin da suke girma na karu da darussa masu yawa, ’yata ta farko yanzu tana aji biyu a jami’a, tana karanta aikin lauya ne, ta biyu kuma tana ajin farko a jami’a, tana karanta aikin jarida, na uku kuma ya kammala sakandare yanzu, sai kuma na karshe mai shekara shida. Idan na gan su sai in ce ‘Alhamdullillah’.
Burina
Burina a yanzu shi ne in zama uwa tagari, sannan in zama kwararriyar malamar masu larura, kasancewar burina rayuwarsu ta inganta.
Yadda nake lura da iyali da kuma aikina
Na sha fada wa mutane cewa koyarwa akwai dadi, domin za ta ba ka damar ka tafi ’ya’yanka makaranta, sannan idan an tashi ku dawo tare, za ku je hutu tare, sannan ku dawo makaranta tare, don haka kullum kana tare da su, don haka ina ba mata shawara ku rika koyarwa duk da cewa ba kowa ne yake son koyarwa ba.
Mutanen da nake koyi da su
A matsayina ta Musulma, babban wanda nake koyi da shi, shi ne, Annabi Muhammadu (SAW) da kuma matansa, a kullum ina fadi tashi wajen ganin na yi koyi da koyarwarsa.
Darussan da na koya a rayuwa
A koyaushe nakan koyi darasi daga kuskuren da na yi, ba na tsoron in yi kuskure domin ina ganinsa a matsayin wani mataki na koyon darussan rayuwa.
Abubuwan da nake so a rika tuna ni da shi
Burina nan gaba al’umma ta rungumi yaran da suke da larura ko’ina suka samu kansu. A kwanan baya mun gabatar da wani taro a Kaduna a kan wayar da kan jama’a muhimmanci ilimi a rayuwar dan Adam, mun kira iyayen yara da malamai da masu makarantu masu zaman kansu, sannan muka yi musu bayani muhimmancin ba wa masu larura ilimi, sannan muka karfafa musu gwiwar yadda za su rika karbar irin wadannan yaran a makarantarsu.  Ina so a tuna ni a matsayin matar da ta yi gwagwarmaya wajen inganta rayuwar yara masu larura.