✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajiya Amina Yakasai: Sai an girmama malamai za a samu albarkar ilimi

Hajiya Amina Abdullahi Maikano Yakasai tsohuwar malamar makaranta ce wacce a yanzu haka ta yi ritaya. Ta ce ilimi zai amfani mai shi ne kawai…

Hajiya Amina Abdullahi Maikano Yakasai tsohuwar malamar makaranta ce wacce a yanzu haka ta yi ritaya. Ta ce ilimi zai amfani mai shi ne kawai idan ya girmama malaminsa. Duk da cewar ba ta samu damar shiga makarantar boko da kuruciyarta ba, hakan bai sa ta zama koma baya a tsakanin abokan karatunta ko na aikinta ba. Haka kuma ta bayyana cewa harkar ilimi ba za ta taba gyaruwa a kasar nan ba har sai an yi amfani da cancanta wajen daukar malamai:

Daga Lubabatu I. Garba, Kano

Tarihin rayuwata
An haife ni a unguwar Yakasai cikin birnin Kano a shekarar 1955. A lokacin da muka tashi a gidanmu ba a sa mata makarantar boko sai dai ta allo. Daga baya sai na koma unguwar Yola wurin kakata. To a nan ne na koyi karatu da rubutun boko a wurin wata uwar dakina da muke shiga gidanta wasa mai suna Hajiya Tagwaram a yanzu haka tana nan da ranta. Tun ina iya karatun Hausa har ya zamto na kware a Turanci.
Daga nan sai aka yi mini aure. Bayan na yi haihuwa ta uku a 1972 da yake maigidana yana da sha’awar ganin mata sun ci gaba, baya ga haka ya fuskanci na san abubuwa da dama a harkar bokon duk da cewa ba kwakkwarar makaranta na yi ba, sai ya sama mini aiki a makarantar ‘yan mata ta GGC Dala inda nake taimaka wa ma’aikaciyar jinya a dakin shan magani na makarantar.
Aikina shi ne na rubuta sunan marar lafiya a kati sannan na kula da dalibai marasa lafiyar da aka kwantar a wurin. Ina wannan aikin da shugabar makarantar wata Baturiyar ingila ta ga kwazona sai ta kai ni kicin din makarantar, ta ba ni aikin kula da abincin da ake girka wa dalibai. Na yi wannan aiki na tsawon shekaru biyar.
A 1977 sai sabuwar shugabar makarantar GGC Dala ta shawarci maigidana da na koma karatu, muka yi sa’a kuwa a shekarar ma’aikatar ilimi ta bude makarantar horon malamai ta bangaren matan aure sai na shiga. Na kuma yi sa’a aka kai ni aji uku har na kammala. Bayan nan sai aka kai mu don mu koyar a makarantu. Na fara koyarwa a makarantar ‘yan mata ta Shekara inda na koyar tsawon shekara guda. Ina nan sai na koma koyarwa a LEA ta karamar Hukumar Dawakin Kudu. Daga baya kuma na koma Kumbotso inda na koyar a makarantar Sheka.
A 1980 na je Jami’ar Legas na yi wani kwas a kan harkar ilimi. A 1982 sai aka ba ni mukamin shugabar makaranta inda na rike wata makaranta da ke Kurede kusa da Mariri. Dama a wannan lokaci ina da mota idan gari ya waye sai na dauki ‘ya’yana na ajiye su a makarantarsu sannan ni kuma na wuce wurin aiki.  A wannan makaranta na zauna tsawon shekaru biyar. Daga nan sai na koma Makarantar Firamaren Wailari inda na yi shekara uku. Daga nan ne sai aka mayar da ni bangaren kula da malamai (inspector) inda muke yawon duba makarantu da su kansu malamai. Ina wannan aiki a 1992 na je Makaranatr FCE Kano zan saya wa ‘yata fom na JAMB sai na hadu da wata daga cikin dalibanmu na GGC Dala a lokacin ita ce rijistara sai ta tambaye ni matsayin ilimina da aikin da nake yi, sai ta ce lallai ni ma sai na koma karatu don haka a take ta fitar da kudinta ta saya min fom tare da karfafa min gwiwa cewa zan iya karatun a hakan, domin a lokacin ina da ‘ya’ya bakwai. A haka dai muka yi karatu ni da ‘yata Jamila. Bayan mun gama sai na koma wurin aikina ita kuma ‘yata sai ta wuce ta dora digirinta a Jami’ar Bayero. Haka na ci gaba da aikina har lokacin da na yi ritaya a 2007.
Nasarori
Babbar nasarar da na samu a rayuwa ita ce yadda muka fara aiki lafiya muka kuma gama lafiya. Haka kuma mun amfana daga abin da muka samu daga aikin, inda muka rike kanmu da ‘yan uwanmu. Ina kallon ire-iren daliban da muka yaye wadanda a yau suka zama wasu a kasar nan a matsayin nasara, dalibanmu sun hada da tsohuwar Ministar Ilimi Rukayyatu Rufa’i da ‘Yar majalisa Saudatu Sani da su Minista A’isha Isma’il da su Binta Sarki Muktar da sauransu. Kodayake kullum ina fadi cewa biyayya da girmama malamai da dalibanmu na da suka yi shi ne sirrin nasarar da suka samu a rayuwa. Nakan yi mamakin irin abubuwan da nake samun labarin daliban yanzu ke yi wa malamansu.

kalubale
Duk da cewa babu abin da mutum zai yi a rayuwa ba tare da ya hadu da kalubale ba, amma ni zan iya cewa ban hadu da wani kalubale a wurin karatu ko aiki ba, sai dai dan abin da ba za a rasa ba. Ko irin matsalar nan ta hada aiki da ’ya’ya ban samu ba, domin a lokacin muna kusa da gidan mahaifiyata, ita take taimaka mini wajen renon ’ya’yana, da sun fara girma kuma sai na sa su a makaranta. Babu shakka maigidana ya tallafa min a harkar karatuna da a ce haka dukkannin masu gida suke to da ba za a rika samun matsaloli a gidan aure ba, kuma kowacce mace za ta yi alfahari da mijinta. Alhamdulillahi maigidana ya tsaya min sosai a harkar ilimina.
Yawan iyali
‘Ya’yana bakwai; maza shida mace daya, sai dai babban cikinsu ya rasu. Alhamdulillahi dukkaninsu babu wanda bai sami karatu daidai gwargwado ba.
Abincin da na fi so
Ina son tuwon masara da miyar kuka da nama da kuma man shanu. Haka kuma ina son fura da nono.
Buri
Ni a yanzu na gama da rayuwa. Ba ni da wani buri da ya wuce na cika da imani na kuma tashi da shi.
Abin da nake so a tuna ni da shi
Ina so a tuna da ni a matsayin wacce ta kula da tarbiyyar ‘ya’yan al’ummar zamaninta tare da ba su shawarwari nagari.
Shawara game da gyaran harkar ilimi
Abin da ya jawo tabarbarewar harkar ilimi a kasar nan shi ne ana diban wadanda ba su da ra’ayin koyarwa kuma ba su cancanci koyarwar ba. Idan da za a tace malaman da ke koyarwa a yanzu a cikin dubu da kyar za ka sami biyar wadanda suka cancanta. A yanzu idan mutum ya rasa aikin yi sai a samar masa koyarwa a ce ya je ya yi kafin ya sami wani aikin. An mayar da aikin koyarwa aikin ya fi babu.  Idan ana so harkar ilimi ta gyaru a kasar nan dole sai an damka sha’anin koyarwa ga wadanda suka cancanta. A da tun dalibi yana makaranta yake zabar aikin da yake son yi wanda kuma a kan hakan yake dorewa. Koyarwa abu ne mai tsada, tana bukatar kwarewa da hikima da wayo da sanin mai mutum zai yi a cikin aji. Ya kamata a ba harkar koyarwa muhimmanci domin nan ne tushe, duk abin da mutum zai zama a rayuwa sai ya bi ta hanyar makaranta, koda kuwa shugaban kasa ne.
Shawara ga mata
Ina shawartar ‘yan uwana mata da su zama masu hakuri. Aure ibada ne, duk kuwa abu na ibada dole sai mutum ya hadu da abubuwan rashin dadi, sai dai idan ya daure zai dace da rahamar Allah.  Su tsaya su tarbiyyanci ‘ya’yansu da kyau, domin sai ka kula da danka yana karami sannan zai kula da kai a lokacin da ka tsufa. Sannan kuma ina jan hankalin mata da su tsaya su yi sana’a don su taimaka wa kansu da kuma ‘ya’yansu. Ba zai yiwu a ce komai mace take son yi sai ta jira maigida ya yi mata ba, komai kudinsa kuwa. Kamata ya yi kafin a ce ya kawo ke ma a naki bangaren kin yi amfani da wanda ke hannunki. Haka kuma mata a nemi ilimi domin shi ne gishirin zaman duniya. Gemu ba ya hana karatu inji ‘yan magana.
Ina kira ga mazaje da su tallafa wa matansu wajen samun ilimi, domin idan aka ce matar gida tana fita makaranta, to fa dole sai mijinta ya yi hakuri ya kuma taimaka mata kafin a sami abin da ake bukata.