✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajiya A’isha Aliyu Shamaki: Dalilin da nake koya wa matan Arewa sana’o’i

Hajiya A’isha Aliyu Shamaki ita ce Sarauniyar Matan Arewa a Legas. ’Yar kasuwa ce, kuma ta shahara wajen taimakon mabukata a sassa da dama na…

Hajiya A’isha Aliyu Shamaki ita ce Sarauniyar Matan Arewa a Legas. ’Yar kasuwa ce, kuma ta shahara wajen taimakon mabukata a sassa da dama na Jihar Legas. Ta bayyana ayyukan da ta sa a gaba shi ne koyar da matan Arewa sana’o’i don su dogara da kansu.

Tarihin rayuwata
Sunana Hajiya Aisha Aliyu Shamaki. Ni ce Sarauniyar matan Arewa a Jihar Legas. An haife ni a shekarar 1972 a karamar Hukumar Hong da ke Jihar Adamawa. Na yi karatun zamani. Na yi firamare, bayan na kammala sai na tafi makarantar sakandire a Jihar Adamawa. Daga nan na tafi birnin Landan da ke kasar Ingila na karanta fannin dinki da kwalliya. Bayan na dawo gida sai na yi aure. Kodayake maigidana bai bar ni na ci gaba da karatu ba, amma ya bar ni in yi sana’a. Tun wannan lokaci nake sana’o’i kamar dinki da kuma zuwa kasashen waje ina kawo kayayyakin sayarwa.
Hada sarauta da kasuwanci da kuma kula da gida
Alhamadulillahi. Idan Ubangiji ya kaddara za ka zama shugaba ko jagoran jama’a zai ba ka baiwar yadda za ka tafiyar da ayyukan da ke gabanka. Ba na wasa da kula da iyalina. Duk abin da zan yi gidana ne farko kuma iyalina ne farko. Idan ina gida ina tabbatar da cewa na kammala duka abubuwan da suka kamata na ayyukan gida, sannan nakan tsara duk abin da zan yi gobe. Kamar kasuwanci, ina yin kasuwanci kamar nau’i shida, saboda haka kowane na san lokacin da nake yin sa, saboda haka sarauta ba za ta hana ni yin kasuwancina da ayyukana na gida ba, kasancewar yanzu an ci gaba.
Manufa
Manufata ita ce, in taimaka wa jama’a musamman ma mata. Ina so in ci gaba da koya wa mata sana’o’in hannu yadda za su dogara da kansu. Ka san ko da ka yi karatu ba ka da aiki, idan ya kasance ka iya sana’a, to babu shakka ba za ka tozarta ba.

Dalilin samun sarautar Saruniyar matan Arewa
An nada ni sarauniyar matan Arewa a Legas kuma sarkin Hausawan Legas, Alhaji Sani Kabiru ne ya nada ni. Kuma ina ganin dalilin da ya sa aka nada ni shi ne, saboda ayyukan da suka ga ina yi a Jihar Legas. Na dade ina zuwa gidan marayu da makafi don in taimaka musu. Shekaru goma da suka wuce ina zuwa unguwar Obalende inda mata ke taruwa ina kai musu kayayyaki daban-daban. Shi ne da suka ji labarina sai suka nada sarautar matan Arewa.
Nasarori
Nasorin da na samu sun hada da taimakon mata da koya musu sana’o’i, kamar yin sabulu da dinki da fannin girke-girke kamar waina da zobo da kunun zaki da kwalliya da sauransu. Ina so in rika shirya musu bita da taron kara wa juna ilimi.
 Tallafi
Gaskiya yanzu ina tallafawa da dan abin da Allah Ya hore mini. Don duk abin da kake son tallafi dole sai ka fara da abin da yake aljihunka, saboda haka zan ci gaba da yi da kudina in ya so daga bisani sai mu nemi tallafin gwamnati da sauran jama’ar gari. Ka ga kamar zuwa asibiti abu ne da yake bukatar kudi, haka ma koyar da sana’a.
kalubale
kalubalen da nake fuskanta shi ne, na karancin kudi. Ka ga kamar fitar da nake so na yi da mata abu ne da yake bukatar kudi haka ma tarukan da zan shirya musu da kuma sana’o’in da zan koya musu, su ma suna bukatar kudi. Kuma ina sa ran ziyartar kananan hikumomin Jihar Legas don ganawa da matan Arewa. Duk wadannan abubuwa suna bukatar kudi sosai.
kungiyar ba da tallafi
Gaskiya ne ina da kungiyar da muka kafa don taimakon jama’a, musamman masu bukatar taimako. Sunan kungiyarmu: kungiyar taimakon mata wacce Hajiya Fatima Shehu ke jagoranta. Muna ayyuka daban-daban na taimaka wa al’umma daban-daban.
Dalilin kin shiga siyasa
Gaskiya dalilin da ya sa ba na siyasa shi ne, a matsayina ta Sarauniya, ni uwa ce, babu yadda zan shiga wata siyasa. Ina goyon bayan dukkan jam’iyyun siyasa. Ba ni da wata jam’iyyar siyasa da na kebe. Ina yi musu fatan alheri. Kuma ko da mukamin siyasa aka ba ni ba zan karba ba.
Shawara ga mata
Ya kamata mata su tashi su nemi abin yi, zama kawai ba zai haifar musu da da mai ido ba. Su fahimci yin sana’a komai kankantar na da amfani. Idan suna sana’a za su tare wani abu a gida, sannan mijinsu zai rika ba su daraja, sannan ba za su rika tambayar mijinsu ya ba su kudin da za su wata gudunmuwa lokacin bikin aure da suna da sauransu.  Ina kuma ba mata shawara su yi karatu, kasancewar komai na duniya sai da ilimi.
Tufafi
Na fi son dinkunan gargajiya. Musamman na Arewa, sannan na fi son farar kala.
Abinci
Na fi son tuwon shinkafa.
kasashen waje
Na ziyarci kasar Ingila da kasar Siwizalan da Indiya da kuma Jamus. A kasashen Afirka na je Sanegal da Togo da Ghana da sauransu.